Kissoshin Rayuwa Imam Hassan (s) 12
Published: 9th, February 2025 GMT
12-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa Shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na shahid Aya. Murtadha muttahhari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen ,Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan (s) limami na 2 daga cikin limamai masu tsare daga iyalan gidan manzon All..(s) kuma dan Fitima(s) diyar manzon All..(s) na farko.
Kuma a cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar yadda manzon All..(s) bayan kwanaki kadan da komawa Madina sai All..ya umurceshi da ya ji makabartan Bakiyya, ya nema masu gafara, don haka a cikin dare ya kira daya daga cikin yentattun bayinsa wanda ake kira Abu Maubihah inda ya fada masa cewa an umurce ni in nemawwa mutanen makabartan bakiyya gafara daga wajen All ..T kuma ina son ka rakani.
A lokacinda suka isar makabartan sai ya fadawa Abu Maubihah kan cewa an bani zami na mubudan taskokin duniya har abada, sannan aljanna, ko kuma haduwa da All..,amma na zami haduwa da All..,
Daga karshe ya zami haduwa da All..T. Sannan bayan kwanaki kadan, sai fara rashin lafiyarsa ta karshe, a nane sai yayi tunanin yadda iko zai koma ga Aliyu dan Abitalib (a) bayansa da sauki. Sai ya tada rundunar Usama dan Zaidu, ta tara dukkan manya-manyan sahabbansa daga cikin muhajirun da ansar, ya dora Usama dan shekara 17 a kansu.
A ciki ya umurci shi da yaje kasar Ruma ta gabas inda aka kashe babansa, ya yi kafirai.
Ya nuna masa dukkan dabarbarun yaki. Sannan ya bashi tutar, sai Usama yake wani wuri a bayan madina wanda ake kira Jurf. Sai yace masa. Amma suka ki fitowa su same shi, wasu ma suka fara sukan shugabancin Usama dan Zaidu, a lokacinda labari ya zo masa wasu sunki fita, sannan suna sukan shugabancin Usama a nan ma sai ya sake fita ya kuma yi masu Magana ya sake jaddada cewa, usman a ya canacanci shugabanci, haka ma babansa kafin shi. Duk da cewa a lokacin ma sun ki amincewa da jagorancin bababansa.
Mun kawo fara kawo maku abinda zamu iya dauka a cikin wannan hadisin, na cewa dabarar da manzon All..(s) yayi na nisantar da masu kodayin Mulki a bayansa ba zai kai ga nasarab, sannan su ma sun fahinci haka, shi ya sa suka sabawa manzon All..(s). Bayan haka.
Mun ji cewa a cikin manya-manyan sahabban da ya Sanya a cikin rundunar Usama akwai, Abubakar, da Umar da Abu ubaida dan jarrah da Usman da sauransu.
Sanna yaki sanya su kan rundunar ne don kada, wani daga cikinsu ya yi amfani da wannan damar don biyar bukatuna sa na kaiwa da shugabanci a bayansa.
Don haka ya tushe masu hanya, sannan ya la’ani duk wanda ya ki tafiya da rundunar Usama.
Banda haka wata dubarar da manzon All..(s) ya yi na shugabantar da Usama dan Zaidu kan wadannan manya-manyan sahabban, shi ne ya nuna masu cewa, shugabanci cancanta ne ba yawan shekaru ba. Kuma All..ya na bawa shugabanci ga wanda ya ga dama, kuma zai bashi ilmi da kuma karfin da yake bukata don cancantar shugabancin.
Don haka manzon All..(s) ya bar wannan duniyar, manya-manyan sahabban manzon All..(s) su na karkashin shugabancin Usama dan Zaidu wanda bai fi shekaru 17 a diniya ba.
Don haka me zai hana Aliyu dan Abitalib wanda ya Usama shekaru, wato dan shekara 30 a duniya a lokacin, zama khalifan manzon All..(s) a bayansa(s)?.
A wani hadisi manzon All..(s) ya na cewa: wanda ya gabatar da kansa a cikin musulmi al-hali ya san da cewa akwai wanda ya fi cancanta da aikin to hakika ya kha’inci All..da manzonsa dakuma muminai (s).
A wani hadisin, yana cewa: All..yana kudaitarwa, sosai kan, wajen zaben mafi korewar mutane, wanda ya kasance mafi cancanta ga wani matsayi. Lalle su sanya maslahar al-umma ne abin lura wajen zaben wanda ya cancanta. Su kasance amintattu a cikin abinda suke karba daga hannun mutane. A cikin cikin kuma kudaden da suke kasewa don abubuwan ji dadin rayuwar mutane. Sannan su tafiyar da al-amuran mutanen a cikin adalci kadai.
Wannan kada ya kasance da yawan shekaru, sai dai ya kasance tare da kwarewa da kuma sanin makamar aiki, da sanin abubuwan da mutane suke bukata.
Don haka manzon All..(s) a cikin shugabantar da Usama Dan Zaidu ya kakkabo wasu daga cikin wadanda suke takara da Amirulmuminina (a) kan shugabancin al-ummar musulmi.
Ya karya zukatansu, daga neman wannan mukamin, ya kuma kashe guiwarsu daga ynkuri don neman wannan matsayin. Ya nisantar da su nesa ba kusa ba daga wannan burin nasu. Sannan suma sun fahinci haka a wajen manzon All…(s) kan hakan.
Baku ga cewa, Umar yana cewa Usama! Manzon All.. zai yi wafati kana shugabana? Basu gushe ba suna suna jan kafa, sun ci gaba da sabawa manzon All..(s) har sai da ya yi wafata. (s).
Wannan kadan Kenan na abinda za’a iya fahinta na shugabatar da Usama dan shekara kimani 17 kan shaihunan kurasihawa da kuma wasu shuwagabannin ansar wadanda suka kodayin shugabancin al-ummar musulmi bayan wafatin sa (s).
Har’ila yau wannan ya tabbatar mana akwai makirci babban da aka kulla don hana Imam Ali (s) zama a kan kujerar da shi kadai ya dace da ita bayan manzon All..(s).
Zazzabi ta yi tsanani ga manzon All..(s), a lokacin matansa suka kusa da shi, a duk sanda suka sa hannunsu a kansa suna jin zafin jikinsa.
Sun sanya ruwan sanyi kusa da shi, a duk sanna ya sa hannunsa cikinsa sai ya taba ruwan ya shafi kansa da hannunsa.
Sai mutane suna ta kai kawo suna bankwana da shi, sai da suka taru a gidan sai yana fada masu: Ya ku mutane, an kusa a dauki raina, daukewa mai sauki, a tafi da ni. Hakikin na gabatar da maganganu, don sauke uzuri da ke kaina a kanku. Sai dai lalle ni ina barin Littafin All..mai girma da daukaka da kuma zurriyata Ahlubaiti na. Sai ya kana hannun Aliyu(a) ya daga ta. : Sai yace: Ga Aliyu nan tare da Alkur’ani , kuma kur’ani yana tare da Ali ba zasu rabu ba, har sai sun riskeni a tabki.
Abinda yakamata al-umma ta yi shi ne ta bi umurnin manzon All..ta bi abinda ya fada mata ta bi Amirulmuminina (s), ta mika mata shugabanci, don shi ne kawai zai tafiyar da al-amarinsu kan koyarwar Alkur’ani mai girma. Ya kuma yi hukunci da hukuncin All..
Ta ta yi haka kuwa da ta tsira daga dukkan tawaya, kuma fitinu ba zasu same ta ba haka ma dukkan hatsurra ba zasu sameta ba. Da kuwa musulunci zai taka matakansa kai tsaye tare da daukaka ya kuma sami iko da duniya gaba daya. Ya cika shi da adalci.
Har’ila yau kafin rasuwarsa manzon All..(s) ya daura rawaninsa, sai ya je masallaci ya hau mimbarinsa, sai yace masu, Lalle Ubangijina ya hukunta ya kuma rantse kan cewa ba zai yafe zulunci azzalumi ba, don haka ina hadaku da All…duk wani mutum wanda yake da wani abu da na yi masa sai ya tashi ya fada don yayi kisasi, a yi kisasa a gidan duniya yafi mani da kisasa a Lahira. A gaban mala’iku da annabawa…}.
Sai kowa ya kasa Magana, manzon All..(s) yana nuna masu kan cewa zalunci ko wace irice mutum ya warware shi a lduniya ya fi masa a yi masa adalci a lahira.
An dade ba wanda yayi Magana sai wani mutum daga karshen masallacin mai suna Sawadat dan Qais, sai yace ai manzon All..(s) ya taba dokansa cikinsa wani lokaci don haka yana son kisasi.
Sai manzon All..(s) yace masa ya zo . sannan ya aiki Bilala ya kawo bulala a gida, da ya kawo sai mutana suna gani me mutumin nan za iyi da manzon All..(s) a cikin wannan halin da yake na rashin rafiya.
Sai Sawada ya zo kusa yana karkarwa., saboda haibar manzon All.. sai y ace: Ya manzon All..ka kyaye mani cikink, sai ya ce ya manzon All..(s) kayi mani izini in Sanya bakina a kan cikinka, sai yace masa ee. Sai ya Sanya bakinsa a kan cikin manzon All… idanunsa yana zubar da hawaye. Sai yana cewa ina neman tsari daga wuta albarkan wurin kisashi daga manzon All..(s), a ranar lahira.
Sai manzon All..(s) ya ce masa, zaka yi kissasi ne ko kai yi afwa, ya swadatah sai y ace Afwa ya manzon All..(s).
Sai manzon All..(s) yad aga hannayensa masu albarka yana uddu’a yana cewa: Ya Ubangiji ! ka gafartawa Sawadatah saboda afwan da yayi wa annabinka Muhammadu.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu . wassalamu Alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: manya manyan masu sauraro
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira.
Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa.
Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono.
Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aureHar ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su.
Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da suke da sauran numfashi inda a yanzu haka ake da ’yan gudun hijira sama da 3,500 da ke neman mafaka a cikin garin Bakori.
Kazalika, rahotanni sun kuma ce akwai wasu sama da 2,500 da ke garin Guga don neman mafaka.
’Yan gudun hijirar wadanda akasarinsu mata ne da ƙananan yara sun watsu a wurare daban daban.
Aminiya ta zagaya unguwan Kafaɗi da unguwar Ma’aru da ke Sabuwar Abuja a cikin garin na Bakori, inda wakilinmu ya tarar da cincirindon mata da ƙananan yara a rakuɓe, a gidajen ’yan uwa, wasu kuma a makarantun firamaren gwamnati da ke karamar hukumar ta Bakori.
A tattaunawar Wakilinmu da wasu daga cikin ’yan gudun hijira wadanda suka fito daga kauyaku daban-daban na jihar, sun nuna alhininsu game da yadda ’yan bindigar ke cin karensu ba babbaka a yankin.
Imrana Shafi’u wanda ’yan bindigar suka harbe shi a ƙafa har wuri biyu, wanda shi ya yi hijira ne daga kauyan Ɗan Marka, ya ce lamarin na da ban tsoro matuƙa.
A cewarsa, “Ni ma Allah ne ya sa zan rayu domin ’yan bindigan sun zaci na mutu ne.
“Domin da suka zo kanmu harbin kan mai uwa da wabi, suka yi ta yi, inda suka kashe mutane da dama.
“Ni ma dai Allah ne ya tsirar dani, domin duk wadanda nake tare da su duk an kashe su, ni kadai na tsira cikin ikon Allah,” in ji shi.
Ita kuwa Malama Marawiya wacce ta yi gudun hijira daga kauyan ’Yar Dabaru ta ce da rana tsaka ’yan bindiga suka keto cikin kauyan nasu, suka tarwatsasu sa’ilin da suka tasa ƙeyar mata sama da 10 kuma duk yawancinsu suna ɗauke da goyo suka yi cikin daji da su.
Marawiya ta kara da cewa kusan kwanakin matan 10 ke nan a hannun su kuma sun ce sai an biya kudin fansa har Naira miliyan daya da rabi kan kowanne mutum daya kafin a sake su.
Ta Kara da cewa “A da in suka dauki mutum bai wuce su ce a ba su Naira dubu ɗari biyar ba amma a wannan karon sai suka ce sai an biya har sama da naira miliyan daya da rabi ga kowanne mutum,” in ji ta.
Yusuf Usman, wanda suka yi sansani a wata makarantar Firamare ta Nadabo da ke cikin garin Bakori, ya ce kusan su ɗari uku ne suka yi gudun hijira daga kauyan Doma, cikinsu har da tsofaffi.
Ya kuma ce, “A haka muka tako da ƙafa muka yini muna tafiya tare da mata da yaran kanana har Allah ya kawo mu garin Bakori,” in ji shi.
Ya kara da cewa kusan shekara biyar kenan suna fama da wannan matsalar ta tsaro, kuma ba dare ba rana bare damina ko rani, haka ake shigowa kauyakun su ana kashe su sannan kuma a tasa ƙeyar su a tafi da su daji domin karɓan kuɗin fansa.
Shugaban kwamitin da ƙaramar hukumar Bakori ta kafa domin kula da ’yan gudun hijirar, Mallam Mamman Yaro Bakori, ya ce adadin ’yan gudun hijirar sun kai 3,500 a garin Bakori.
Ya Kara da cewa a garin Guga Kuma akwai akalla kimanin mutane 2,500 da suke gudun hijira a can.
Shugaban ya ce kuma kusan a kullum yawan su ƙaruwa yake yi, sannan suna warwatse ne a wurare daban daban a inda wasu suke zaune a gidajen ‘yan uwansu wasu kuma suna zaune ne a makarantar firamare ta Nadabo a cikin garin Bakori.
Sai dai ya ce tuni Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Barde ya bayar da umurnin kai masu tallafin kayan abinci sau uku a rana tare da kudin cefane don saukaka masu rayuwar da suke ciki.
Wasu na bayyana cewa a ‘yan kwanakinnan ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka kafa sansaninsu a dajin Guga da Kandarawa da Kakumi.