Kudin Ajiyar Najeriya Na Kasashen Waje Sun Ragu Da Dalar Amurka Biliya 1.79
Published: 7th, February 2025 GMT
Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata.
Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun zama dala biliyan $39.
An bayyana koma bayan ne a kudaden waje na ajiya da babban bankin kasar yake da su, da ya kamata ace a ranar 4 ga watan Febrairu ne za a fitar da kididdiga akan halin da kudaden wajen suke ciki,amma ba a yi ba.
Bugu da kari wannanbayanin ya fito ne daga kamfanin dake kula da kai da komawar kudaden Waje Bismack Rewane da yake hasashen samun raguwar kudaden ajiyar na Najeriya a tsakanin shekarar 2025-2026 sai sami koma baya da kaso 11.47,wato zuwa dala biliyan 36.21, yayin a a cikin shekarar 2026 zai zama dala biliyan 37.65,alhali a 2024 ya kasance dala biliyan 40.9.
Farashin Naira idan aka kwatanta ta da Dala, a 3 ga watan nan na Febrairu shi ne ; Naira 1,500.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: dala biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya sheƙar da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban suke yi.
A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ta jawo ɗiga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaɓen 2027.
Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan ƙasar suke kokawa bisa yadda ake gudanar da mulki da kuma yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC.
NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaWannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai da nufin gano alƙiblar da siyasar Najeriya take shirin fuskanta.
Domin sauke shirin. Latsa nan