Shugaba Tinubu Ya Sauke Shugabar Jami’ar Abuja Farfesa Aisha Maikudi
Published: 7th, February 2025 GMT
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami’o’in gwamnatin tarayya da dama da suka hada da Jami’ar Abuja wadda a yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon.
A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya ce a jami’ar Yakubu Gowon, shugaba Tinubu ya rusa majalisar zartarwa gaba daya tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga mukaminta na shugabar Jami’ar.
Sanata Lanre Tejuoso, wanda a halin yanzu shi ne uban Jami’ar Aikin Gona ta Makurdi ne aka nada shi a matsayin Uban Jami’ar Yakubu Gowon. Sanata Joy Emordi, wacce a yanzu ita ce shugabar jami’ar ilimi ta Alvan Ikoku za ta gaje shi a Makurdi.
Shugaba Tinubu ya nada Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin mukaddashiyar shugaban jami’ar Yakubu Gowon na tsawon watanni shida. Ba za ta cancanci neman matsayin Shugabancin Jami’ar ba idan aka tashi neman shugaba.
Bugu da kari, shugaba Tinubu ya cire Farfesa Polycarp Emeka Chigbu daga mukaminsa na Shugaban jami’ar Nsukka (UNN), kafin wa’adinsa ya kare a ranar 14 ga watan Fabrairu.
An nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin magajinsa na tsawon watanni shida kuma ba zai cancanci neman mukamin na dindindin ba.
Gen. Ike Nwachukwu ya koma Uban Jami’ar Uyo. Shugaba Tinubu ya nada Injiniya Olubunmi Kayode Ojo a matsayin sabon shugabar UNN. A baya, Ojo ya rike wannan matsayi a Jami’ar Tarayya ta Lokoja da Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti.
Farfesa Zubairu Tajo Abdullahi, wanda a halin yanzu shi ne Uban Jami’ar Uyo, an nada shi ya gaji Ojo a Jami’ar Tarayya ta Lokoja.
Sanata Sani Stores shi ne sabon Shugaban Jami’ar Ilimi ta Alvan Ikoku, wanda ya gaji Sanata Joy Emordi. Sanata Stores dan majalisa ne a Jami’ar Najeriya, Nsukka.
Bugu da kari kuma, Barista Olugbenga Kukoyi, wanda dan majalisa ne a jami’ar Najeriya, Nsukka, an nada shi a matsayin sabon shugaban jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra.
Sanarwar ta bayyana cewa duk nade-naden mukamai sun fara aiki ne nan take.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, wadannan sauye-sauyen na nuni da kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar ilimi mai zurfi a Najeriya ta hanyar jagoranci da rikon amana.
Sanarwar ta kara da cewa sake fasalin na da nufin karfafa harkokin mulki da nagartar ilimi a bangaren ilimin manyan makarantun Najeriya.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jami ar Yakubu Gowon jami ar Yakubu Gowon Shugaba Tinubu ya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu zai ziyarci Katsina
Karon farko tun bayan zamowarsa shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai ziyarci Jihar Katsina.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bala Zango, ne ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce shugaban zai kai ziyarar ce, domin ƙaddamarwa da kuma rangadin wasu ayyukan da Gwamna Umar Dikko Radda ya aiwatar a jihar.
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a AbujaKarin bayani na tafe.