Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki a Katsina
Published: 7th, February 2025 GMT
Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya wa al’ummarta kudin wutar lantarki a kowane wata.
Shugaban Hukumar, Alhaji Bishir Sabi’u na cewa nan gaba za a kammala aikin layin da aka ware musu na musamman na Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa (TCN).
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa karamar hukumar ta riga ta hada garin Jibia da layi na musamman na TCN domin garin ya rika samun wutar yadda ya kamata.
Ya ce, “duk da cewa an yi gwajin wutar, amma ba a riga an kammala aikin layin na TCN ba, kuma da ya fara aiki, al’ummar garin za su fara samun wutar lantarki tsawon awa 24.”
’Yan sanda sun sa dokar hana yawon dare a Gombe NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibaiHonorabul Sabi’u wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Mohammed Lawal-Jibia, ya ce karamar hukumar ta kulla yarjejeniyar da Kamfanin Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), domin biyan kudin wutar lantarki Naira miliyan biyu ga al’umma a duk wata.
Ya ce sun dauki matakin ne domin rage wa jama’a wahalar da suke fama da ita ta tsadar rayuwa, musamman lura da yadda matsalar tsaro ta addabi yankin.
Ya bayyana cewa mma duk da haka, masu sana’o’in da ke jan wutar lantarki sosai ba sa cikin masu cin gajiyar tagomashin.
Alhaji Mohammed Lawal-Jibia ya sanar da hakan ranar Alhamis a yayin karbar bakuncin shugabannin Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) a kai kai masa ziyarar aiki.
Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa an samu wannan nasara da makamancin sa aka samu a bangaren noma da ilimi da sauransu ne da sahalewar Gwamna Dikko Radda.
A cewarsa, matsalar tsaro a karamar hukumar ta ragu sosai, yana ai cewa gwamnan bai taba yin watsi da bukatar al’ummar Jibia kan sha’anin tsaro ba.
Hasalima, gwamnan ya ba da fili da za a gina gidaje 152 domin sake tsugunar da ’yan gudun hijira a karamar hukumar.
Jibia na daga cikin kananan hukumomin Jihar Katsina mafiya fama da hare-haren ’yan ta’adda, inda da wuya a yini ba tare da hari ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Lantarki karamar hukumar wutar lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati.
Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar.
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a BornoBakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace.
“Jihar Katsina na da makaruntun gaba da sakanadare na gwamnati huɗu da ke bayar da takardar shaidar difloma da koyarwa, sai kuma ƙarin 39 masu zaman kansu.
“Sai dai bincikenmu ya bankaɗo biyu ne kacal a cikin 39 suke da cikakkiyar rajista da hukumomi.”
Kwamishinan, ya kuma ce shida daga cikinsu na buƙatar gyare-gyare domin kammala rajistar, yayin da 22 ke aiki ba tare da rajistar ba.
“Ƙarƙashin sabon tsarin da muka ɗauka yanzu, ya zamo dole makarantun da ke bayar da takardar shaidar digiri su yi rajista da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).
“Masu difloma kuma da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE), sai masu koyarwa da Hukumar Kula da Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (NCCE).
Bakori, ya jaddada cewa, duk makarantar da ta saɓa wa wannan tsarin, a shirye gwamnatin take ta rufe ta.
Sai dai ya yi wa ɗaliban da ke makarantun albishir ɗin cewa gwamnatin za ta tabbatar ta sauya musu makaranta zuwa masu rajista daga waɗanda ba su da su, idan buƙatar rufe su ta taso.