MDD za ta yi zaman gaggawa kan yaƙin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo
Published: 7th, February 2025 GMT
A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA.
MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana.
Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka.
Sai dai har yanzu Rwanda ba ta bayyana a hukumance cewa dakarunta na a cikin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congon ba.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yaki
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
Gwamnatin kasar Saudiya ta yi allawadai da HKI a kissan da take wa falasdinawa a Gaza, a jiya talata a gaban kutun ICJ. Saudiya ta bayyana cewa gwamnatin HKI ta sabawa dokokin kasa da kasa da dama a kissan kiyashin da take yi a Gaza.
Wakilin kasar a gaban kotun Muhammad Saud Al-Nasser, ya kara da cewa, HKI ta ci gaba ta sabawa wadannan dokoki, amma kuma bata da dalilan saba masu.
Banda kissan kiyashin da take yi a Gaza, Al-Nasser ya ce HKI ta maida Gaza kofai, ta rusa mafi yawan gine-ginen yankin, sannan ta hana shigowar abinci da ruwa da magunguna zuwa yankin, wadanda ko wane daya daga cikinsu take hakkin bil’adama ne wanda yake kaiwa ga laifin yaki.
Gwamnatin Saudiya ta gabatar da wannan jawabin ne a rana ta biyu da bude zaman da kotun ta ICJ tayi don tattaunwa da kuma jin ra’ayin kasashe dangane da take hakkin bi’adaman da HKI take yi a Gaza. A halin yanzu fiye da kwamaki 50 kenan da gwamnatin HKI ta ke hana shigowar abinci da magunguna da kuma bukatun falasdinawa zuwa yankin.
Har’ila yau kotun ta girka wannan zaman ne don tattauna yadda HKI take mu’amala da umurnin ta danganda take hakkin bil’adama a Gaza.