Afirka Ta Kudu Ta Dage A Kan Matsayinta Duk Tare Da Barazabar Amurka Na Kin Halattan Taron G20
Published: 7th, February 2025 GMT
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta ki bada kai ga bukatun Amurka duk tare da barazanar sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio na fasa zuwa taron G20 a kasar
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ronald Lamola ministan harkokin wajen kasar Afirka ta kudu na cewa
“kasarmu yentacciyar kasa ce, kan tsarin democradiya, sannan tana mutunta bil’adama, tana daidaito tsakanin kasa, babu bambamcin launin fata”
Lamola ya kara da cewa kasarsa na da tsarin zamanta kewa mai cikekken yanci daga duk wata kasa a duniya.
Ministan ya kara da cewa, ba sauyin yanayi ne kawai muke tattaunawa a taron G20 ba,
Kafin haka sakataren harkokin wajen Amurka yace, shi ba zai halacci taro inda babu ambaton bukatun Amurka ba.
A ranakun 20-21 na watan Fabrayrun da muke ciki ne za’a gudanar da taron G20 a birnin Jorhamsboug na kasar Afirka ta kudu.
Amma Amurka tana korafin yadda Afrika ta kudu tasa HKI a gaba, kan kisan kiyashin Gaza da kuma wata dakar wacce shugaban kasar Cyril Ramaposa ya sanyawa hannu dangane da rabon filaye cikin adalci a kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp