HausaTv:
2025-11-03@08:36:37 GMT

ICC Na Neman Shaidu Kan Ta’asar Da Aka Aikata A Gabashin DR Congo

Published: 6th, February 2025 GMT

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na neman shaidu kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Matakin zai shafi irin ta’asar da aka aikata daga ranar 1 ga watan Janairun 2022 zuwa yau, bisa la’akari da tashe-tashen hankula da aka yi a makonnin baya-bayan nan musamman a birnin Goma – babban birnin lardin Kivu ta Arewa.

Kotun ta ICC ta ce an jikkata dubban mutane tare da kashe daruruwan mutane a birnin Goma da kewaye.

Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da fararen hula da dakarun wanzar da zaman lafiya, bayan shafe tsawon watanni ana gwabza fada tsakanin sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da kungiyar M23 da kawayenta.

Ofishin mai gabatar da kara ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da shaidu, da kungiyoyin kasa da kasa, kungiyoyin farar hula, da su bayar da duk wata shaida da ke hannunsu, dangane da zargin laifukan da dukkan bangarorin suka aikata.

A nata bangaren, DRC tana shirin gabatar da kudiri ga kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya a wannan Juma’a a birnin Geneva na kasar Switzerland, na neman a gudanar da bincike kan abin da ta kira “gaggarumin take hakkin dan Adam” a birnin Goma.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.

“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.

Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.

“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.

Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.

“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
  • Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai