NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa
Published: 7th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa?
Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba.
A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi sun koma sayen na gwangwani ko na leda.
Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: farashi
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza
Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza.
A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba amma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri.
Ta bayyana cewa kin bari a shigar da kayayyakin jin kai na yankunan Falasdinawa tun daga ranar 2 ga watan Maris ya kara ta’azzara wahalhalun jin kai a Gaza, tana mai bayanin cewa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na kokarin samar da muhimman abubuwan da ake bukata domin ci gaba da rayuwar al’ummar Falasdinu.