Sin Na Maraba Da Baki Daga Daukacin Duniya Su Zo Su More Da Kyawawan Al’adun Sinawa
Published: 6th, February 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya tattalin arziki, da kuma kyakkyawar makomar bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin.
Kididdiga ta nuna cewa, ya zuwa ran 5 ga watan Fabrairu, adadin kudin da aka samu na tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun Bikin Bazarar, ya zarce Yuan biliyan 10, kuma masu kallon fina-finai sun kai yawan miliyan 187, wanda ya zama adadi mafi kololuwa da aka samu. Kazalika, an fitar da fina-finai da dama zuwa kasashen waje a lokaci guda, inda kuma wasu suka kasance kan gaba a gidajen sinima da ake kallon fina-finan da ba na Ingilishi ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
এছাড়াও পড়ুন:
Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya.
Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jinjirin watan ba a ranar Lahadi.
Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da UkraineHakan na nufin yau Litinin, 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.
A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Asabar da ta gabata ce Fadar Sarkin Musulmin ta ba da umarnin duban watan na Zhul Qi’ida.