Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Biya NAHCON Naira Biliyan 4.5 Na Maniyyatan Bana
Published: 6th, February 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar.
Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.
Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809.
A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Don haka Labbo ya bukaci Maniyyatan jihar da su gaggauta kammala biyan kudinsu kafin wa’adin da NAHCON ta bayyana, saboda rashin yin haka na iya sa su rasa kujerunsu.
Ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara gudanar da taron bita ga maniyyata a cibiyoyin da wasu Malamai suka kebe domin alhazan jihar.
Yayin da yake tsokaci kan masaukin Alhazai, Labbo ya ce hukumar ta samar da masauki na alfarma kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah, domin alhazan jihar su sami damar gudanar da ayyukansu cikin sauki.
Don haka ya bukaci maniyyatan da su ci gaba da bai wa hukumar hadin kai domin cimma burin da ake so.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tun ffarko da hukumar ta sanar da sama da miliyan 8.4 a matsayin kudin aikin Hajjin shekarar 2025 ga maniyyatan jihar.
Shugaban hukumar ya bayyana cewar sun yi taro da jami’an hukumar na shiyoyi, wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar da ke Dutse.
Ya yaba da irin goyon baya da kuma kyakkyawar alakar aiki da ake samu a tsakanin mahukuntan hukumar da ko’odinetocin, inda ya yi addu’ar samun dauwamammen hadin gwiwa domin amfanin kowa da kowa da kuma ci gaban jihar.
Ya kuma bayyana cewar sun yi taro da jami’an hukumar na shiyoyi, wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar da ke Dutse.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hukumar Alhazai Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.
Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.
A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.
Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.
Abdullahi Jalaluddeen