Matar aure kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa
Published: 6th, February 2025 GMT
An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano.
’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya, kasancewar mahaifiyarsa da mahaifin sun rabu.
Bayanai sun nuna cewa duk da cewa kakar ta ki amincewa, amma sai da matar ta nace ta dauki yaron da cewa za ta kula da shi, bayan nan ne kuma sanya masa tafasasshen ruwa a gaban nasa, maimakon ruwan dumi.
Duk da raunin da tafasasshen ruwan ya yi masa kuma, sai aka kai shi wurin mai maganin gargajiya maimakon asibiti, inda bayan kwana uku rai ya yi halinsa.
HOTUNA: Yadda gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Kano Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinjiKakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa matar tana tsare ana mata tambayoyi kafin a gurfanar da ita a gaban kuliya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
Daga Abdullahi Shettima
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna.
Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”
A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su cim ma nasara a rayuwarsu.
Haka kuma, ya halarci baje kolin birnin Dubai mai taken “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira da Tasirin Zamantakewa,” inda ya jaddada muhimmancin jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha wajen buɗe damarmaki ga al’umma.
A yayin taron, Gwamnan ya gudanar da ganawa ta musamman da Marwan Bin Galita, Darakta-Janar na birnin Dubai, inda suka tattauna batutuwan kirkirar makamashin sharar gida, kula da sharar zamani, da tsare-tsaren gine-ginen birane na zamani.
Duk ɓangarorin biyu sun amince da zurfafa haɗin kai a fannin fasaha da musayar ƙwarewa domin tallafawa sauyin tattalin arzikin Kaduna zuwa mai ɗorewa.
Gwamna Sani ya bayyana cewa halartar Kaduna a taron (APCS 2025) na nuna shirin jihar na shiga sahun gaba wajen yin haɗin kai, ƙirƙira da zama abin koyi a fannin ci gaba mai ɗorewa — a Najeriya da duniya baki ɗaya.
Karshe.