PCN Ta Kai Ziyara Ga Hukumar Samarda Magunguna Ta Jihar Kano
Published: 6th, February 2025 GMT
Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA).
Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo.
Jami’ar Jihar Kano mai kula da ofishin PCN Kano Pharmacist Hasiya Abubakar Ladan ce ta jagoranci tawagar da suka kai ziyarar.
Wannan ziyarar wani mafari ne na tantancewa da wata tawagar kwararru daga hedikwatar PCN ta kasa da ke Abuja.
Ta bayyana cewa ziyarar na da nufin tantance yadda DMCSA ke bin ka’idoji, don ba da Takaddar Rijistar wuraren sayarda magunguna.
Pharmacist Ladan ta yabawa shugabannin DMCSA bisa yadda suke tafiyar da ayyukan kungiyar yadda ya kamata tare da nuna gamsuwa da matakin da hukumar ta dauka.
Darakta Janar na DMCSA Pharmacist Gali Sule, ya tarbi tawagar inda ya zagaya da su a rumbunan adana kayayyaki.
Ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da samar da magunguna domin inganta sashin sarrafa magunguna kamar yadda PCN da NAFDAC suka bada shawara.
Pharmacist Sule ta godewa tawagar bisa ziyarar da suka kai tare da ba su tabbacin hadin kan DMCSA a duk lokacin da ake gudanar da aikin tantancewa.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Tantancewa
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila
Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron
A wata gagarumar nuna rashin amincewa da tushen zaluncin da ya addabi duniya, tawagogin kasashen Iran, Yemen, da Falasdinu sun fice daga zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, bayan da shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” zai fara gabatar da jawabinsa mai kunshe da bayanai neman tunzura jama’a, wanda kuma bayanai suka haifar da cece-kuce a tsakanin wadanda suka zauna suka saurara.
A cikin jawabin shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” ya bayyana cewa; Akwai yiwuwar samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu a wajen yankunan Falasdinu, musamman a biranen London da Paris na kasashen Birtaniya da Faransa.
Wannan matakin na nuna rashin amincewa da yadda yahudawan sahayoniyya suke adawa tare da yin watsi da hakikanin samuwar Falasdinawa da kuma kokarin tauyaye hakkin al’ummar Falasdinu.
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ne ya jagoranci tawagar ‘yan majalisun dokokin kasar Iran zuwa wajen taron da ya hada shugabannin majalisun dokokin duniya karo na shida a birnin Geneva na kasar Switzerland.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba July 31, 2025 Sojan Amurka Ya Bada Ruwayar Yadda Sojojin Sahayoniyya Suka Kashe Wani Yaro Balasdine July 31, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku July 31, 2025 Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025 Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci