Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Nemi Maniyyata Su Kammala Biyan Kudinsu Kafin Cikar Wa’adi.
Published: 5th, February 2025 GMT
Yayin da Hukumar Kula da Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudin Hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta umarci dukkan ofisoshin da suke alhakin yin rajista su tabbatar da an yi wa duk masu sha’awar tafiya Hajji rajista kafin ƙarshen wa’adin da aka ƙara.
Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya kuma yi kira ga dukkan maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗinsu ba da su gaggauta yin hakan.
Ya jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin bayan ranar 10 ga Fabrairu ba, don haka ya bukaci maniyyata su yi amfani da wannan damar su kammala rijistarsu kafin ko zuwa Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Biyan Cikar Hukumar Jihar Maniyyata Wa adin Rajista
এছাড়াও পড়ুন: