Politico: Sojojin Ukiraniya Suna Fuskantar Matsin Lamba Da Karancin Mayaka
Published: 5th, February 2025 GMT
Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka.
Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da suke guduwa daga filin yaki suna karuwa.
Jaridar ta kuma kara da cewa; Babban hafsan hafsoshin kasar ta Ukiraniya ya bayar da umarnin a dauki sojojin sama 5000 a mayar da su na kasa.
Da akwai tsoron cewa kasar ta Ukiraniya tana rashin kwararrun sojojinta, da ba za ta iya maye gurbinsu a cikin sauki ba idan har aka tura su zuwa filin daga.
A gefe daya, ministan harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa; A halin yanzu Ukiraniya tana yin asarar mutanenta ba wai kudi ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Kakkabo Wani Jirgin Yakin HKI Samfurin F-35 Karo Na 3 Tare Da Kama Matukinsa
Na’urorin kakkabo jiragen sama na Iran sun kakkabo jirgin sama na HKI samfurin F-35 a yammacin kasar, wanda shi ne karo na uku a cikin sa’oi 24.
Kamfanin dillancin labarun Tasnim ya nakalto majiyar tsaro na cewa; dakarun kare samaniyar jamhuriyar musulunci sun harbo jirgin sama samfurin F-35,kuma matukinsa ya fito ta hanyar amfani da lemar ceto.
Bayan wani lokaci daga faduwar jrigin da kuma fitowar matukinsa daga ciki, sojojin kasa na jamhuriyar musulunci ta Iran sun kama shi.
A jiya Juma’a ma dai daakrun kare sararin samaniyar jamhuriyar musulunci ta Iran, sun kakkabo jiragen saman na ‘yan sahayoniya wadanda kirar Amurka ne, kuma daya daga cikin jiragen yakin da take alfahari da su.
Shi dai jirgin yakin na Amurka samfurin F-35 yana da layar zana, kuma da wuya na’urar hangen nesa-Radar- ta iya tsinkayo shi. Kudin kowane daya daga cikin wadannan jiragen shi ne dalar Amurka miliyan 100.