Amurka Za Ta Fice Daga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam Ta MDD
Published: 4th, February 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai rattaba hannu kan wasu takardun bayar da umarni na bangaren zartaswa, game da janyewar Amurka daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya (UNHRC) da kuma dakatar da bayar da tallafi ga hukumar bayar da agaji ga Falasdinu ta majalisar dinkin duniya (UNRWA).
Wata kafar yada labarai ta cikin gida a Amurka ta bayar da rahoton haka, daga wata majiya ta hukuma a fadar White House.
Yau talata kuma Trump na ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya dade yana sukar hukumar ta bayar da agaji ga Falasdinu ta UNRWA.
A lokacin wa’adin farko na mulkin Trump a watan Yunin 2018, Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya, tana mai cewa hukumar ta bayar da damar zama mamba a cikinta ga kasashen da ba su cancanta ba, kuma ta kafa kahon zuka da kuma nuna muguwar kiyayya mara iyaka ga Isra’ila.
Tun dai bayan hawansa mulkin AMurka a karo na Biyu Trump ya sanar da soke yarjejeniyoyi da dama da kuma janye kasarsa daga wasu kungiyoyi na kasa da kasa.
Na baya baya nan ita ce hukumar lafiya ta Duniya, WHO, da kuma soke tallafin da Amurka ke baiwa kasashen ketare in ban da na kawar kasar Isra’ila da kuma Masar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Dangane da sanarwar da Amurka ta fitar ta kakaba takunkumi kan jami’an hukumar kare hakkin Falasdinawa da mambobin kungiyar ‘yantar da Falasdinu, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin ta kadu da hakan, kuma tana nuna takaici da rashin fahimta cewa, Amurka ta yi watsi da kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya ga Falasdinu. Kuma kasar Sin ta dage wajen goyon bayan tsari mai adalci ta al’ummar Falasdinu don maido da halastaccen hakkin al’ummar, kuma za ta ci gaba da yin namijin kokari a wannan fanni tare da sauran kasashen duniya.
Dangane da umarnin da shugaban Amurka Trump ya bayar na kara haraji kan kasashen duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin na adawa da cin zarafi na kudaden haraji ba zai canza ba, domin babu wanda zai yi nasara a yakin haraji, kuma ra’ayin amfani da kariyar cinikayya yana cutar da muradun kowane bangare.
Dangane da rahotannin da ke nuni da cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare ta yanar gizo kan kasar Sin, Guo Jiakun ya ce, wannan ya fallasa munafuncin Amurkan na koken “kama barawo” a fannin tsaron intanet. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare tsaron intanet.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp