Matsalar “Fentanyl” Ba Laifi Ne Da Amurka Za Ta Iya Dora Wa Wasu Ba
Published: 4th, February 2025 GMT
A kwanan baya, kasar Amurka ta kakaba wa kayayyakin kasar Sin da ake neman shigar da su cikin kasuwanninta karin harajin kwastam na kaso 10%, bisa dalilin wai Sin na sayar da magani mai suna Fentanyl a kasar.
Hakika maganar Fentanyl din wani batu ne da kasar Amurka ta dade tana kokarin ruruta shi, inda wasu ‘yan siyasar kasar ke neman dora laifin yadda mutanen kasar ke amfani da maganin a matsayin miyagun kwayoyi kan kasar Sin, cewa wai “Sin na samar da sinadarin hada maganin Fentanyl, wanda aka sarrafa shi zuwa miyagun kwayoyi a Mexico, tare da kai su cikin Amurka”.
Sai dai a ganin Farfesa Li Haidong na jami’ar diflomasiyya ta Sin, gwamnatin Amurka ta yi sakaci wajen sa ido kan yadda ake amfani da maganin Fentanyl a cikin gidanta, abin da ya sa batun ya zama wata matsalar da ake fuskanta a kasar. Sa’an nan, da gwamnatin kasar Amurka ta ga ta kasa magance matsalar daga tushe, sai ta fara dora laifi ga sauran kasashe da suka hada da Sin da Mexico, don nuna wa jama’arta cewa tana daukar mataki. Ban da haka, ta mai da maganar Fentanyl a matsayin wani dalili na daukar matakin karin haraji kan kayayyakin kasar Sin. (Bello Wang)
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga Amurka, da ta gaggauta dakatar da shuka kiyayya, da haifar da tashin hankali, da rura wutar gaba a tekun kudancin kasar Sin, kana ta kyale a dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a yankin. Lin Jian, ya bayyana hakan ne yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka yi masa tambaya kan batun.
Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, a baya bayan nan, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya fitar da sanarwa dake cewa Amurka na goyon bayan kasar Philippines, game da watsi da ta yi da tsare-tsaren kasar Sin na kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin Huangyan Dao.
Lin ya ce “Mun gabatar da kakkarfan korafi a yau, dangane da kuskuren da Amurka ta tafka. Tsibirin Huangyan Dao yankin kasar Sin ne tun fil azal”, kuma kafa yankin kare muhallin halittu a tsibirin na karkashin ikon mulkin kai na Sin, wanda hakan ke nufin yana bisa turba, ya dace da doka, bai kuma cancanci suka ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp