Aminiya:
2025-11-03@03:22:32 GMT

Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Published: 2nd, February 2025 GMT

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa.

Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10.

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu

Aminiya ta ruwaito cewa, an bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda suka samu lambobin yabon sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa kuma a dalilin haka an samu ci gaba musamman wajen inganta rayuwa da tattalin arzikin Jihar Kano da Nijeriya gaba ɗaya.

Abba ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa gwiwa da waɗannan zaƙaƙurai domin tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma ci gaban Jihar Kano.

Gwamnan ya kuma hori matasa masu tasowa da su ɗauki waɗannan fitattun mutane a matsayin madubi wajen karkatar da alkalar rayuwarsu a fannonin ilimi daban-daban domin ɗaga martabar Kano a nan cikin gida da ƙetare.

Ya miƙa godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar gudanar da taron ciki har da Gwamnatin Tarayya ta ba da goyon baya.

Daga cikin waɗanda aka karrama akwai mace ta farko a Arewacin Nijeriya da ta zama Farfesa a fannin likitancin mata da ƙananan yara da mace ta farko a matsayin Kwamishinar ’Yan sanda da kuma Bakano kuma ɗan Nijeriya na farko da ke riƙe da muƙamin Shugaban Ƙungiyar Injiniyoyi ta Duniya.

A nasa jawabin, Shugaban Limaman Nijeriya, Sheikh Nasir Muhammad Adam, ya ƙalubalanci waɗanda aka karrama da su kasance alƙiblar da za ta zama haske ga matasa masu tasowa kafin cikar wa’adinsu a ban ƙasa.

Fitattun Kanawan da aka karrama sun haɗa da Air Marshal Hassan Bala Abubakar, Manjo-Janar M S Ahmed, Manjo-Janar IS Ali, Manjo-Janar A M Garba, Manjo-Janar Sani Sumaila Ibrahim, Manjo-Janar B U Yahya, Manjo-Janar S Y Bashir, Manjo-Janar U B Abubakar, Manjo-Janar Faruk Mijinyawa da Manjo-Janar Jamal Abdulsalam.

Sauran sun haɗa da Air Vice Marshal M Yusuf, Air Vice Marshal G A Bello, Air Vice Marshal B R Mamman, Air Vice Marshal SK Usman, Air Vice Marshal M S Ibrahim, Air Vice Marshal KM Umar, Rear Admiral Abdullahi Ahmad, Rear Admiral Aliyu Gaya da Rear Admiral Idi Abbas.

Ragowar waɗanda suka samu karrramawar sun haɗa da Farfesa Shehu Ahmad Said Galadanci, CON, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, Yakubu Adamu Kofar Mata, DIG Dasuki Galadanchi, DDG DSS, Alhaji Ado Muazu, Farfesa Umma Abdullahi, Farfesa Hadiza Galadanci, Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, Farfesa Hamisu Armayau Bichi, Farfesa Sagir Adamu Abass da Kwamishinar ’Yan sanda, CP Hajiya Hauwa Ibrahim.

Akwai kuma Rislanuddeen Muhammad, Injiniya Mustafa Balarabe Shehu, Arc. Hauwa Hassan Tudunwada, Ado kabiru Minjibir Mni da kuma Marwan Mustapha Adamu mni.

Bikin ya samu halarcin dattawa da kuma fasihai a fannonin rayuwa daban-daban daga garin na Kano.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Injiniya Mustafa Balarabe Shehu Jihar Kano kanawa Air Vice Marshal Manjo Janar

এছাড়াও পড়ুন:

An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano

Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar  Christopher Musa 
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure