Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu
Published: 2nd, February 2025 GMT
Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa.
Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci.
Marigayi Shehin Malami a Sashen Harshen Larabci na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina, inda a nan ya samu matsayin Farfesa.
Ya kasance Shugaban Sashen Larabci (HOD) na Jami’ar na farko tun da aka kirkiro ta a shekarar 2006, inda ya yi wa’adi biyu na tsawon shekara goma zuwa 2016.
Shi ne mutum na farko ɗan asalin Jihar Katsina da ya samu muƙamin Farfesa a fannin harshen Larabci.
Haka kuma yana daga cikin malaman da suka ƙaddamar da Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Ka Ikamatis Sunnah (JIBWIS) a Jihar Katsina.
An haife shi a ranar 15 ga Fabrairu, 1953 unguwar Adoro da ke garin Katsina, kuma ya rasu yana da shekara 72, ya bar ’ya’ya 10 da jikoki 32.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Katsina
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunan da aka yanke wa hukuncin kisa ya tsere daga gidan yari a Yobe
Wani fursuna mai suna Abba Hassan, wanda aka yanke wa hukuncin kisa, ya tsere daga gidan gyaran hali na Potiskum da ke Jihar Yobe.
Rundunar ’yan sanda ta Jihar, ta tabbatar da wannan lamari a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Asabar.
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan AmurkaA cewar sanarwar, Abba Hassan, wanda asalinsa ɗa Jihar Borno ne, ya gudu daga gidan yarin a ranar 31 ga watan Oktoba, bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa.
DSP Abdulkarim, ya roƙi jami’an tsaro, direbobi, sarakunan gargajiya, ’yan banga da al’ummomin Jihar Yobe da maƙwabtan jihohi da su taimaka da bayanai da za su taimaka wajen sake kama shi.
Ya kuma gargaɗi jama’a da kada su kusanci fursunan da ya tsere, domin hakan na iya zama hatsari.
“Domin kare lafiyarku, idan kuka ga wani da kuke zargi shi ne, ku sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa ko gidan gyaran hali, ko kuma ku kira lambar 08038452982,” in ji sanarwar.