Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu
Published: 2nd, February 2025 GMT
Kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid ta zargi Manchester City da karfafa gwiwa ga daya daga cikin ‘yan wasanta, Juma Bah domin ya soke yarjejeniyarsa ya koma buga Premier League da buga wasa. Dan wasan mai tsaron baya, ya sanar da kungiyar ta Sifaniya ranar Talata cewar yana so ya katse yarjejeniyarsa, saboda ya koma Manchester City kan kankanin kudi.
Tun a baya Manchester City ta nemi izinin Balladolid, domin tattaunawa kan sayen matashin mai shekara 18, domin ya koma buga mata wasa amma sai kungiyar ta ce tana son dan wasanta kuma ba na sayarwa bane. Bah bai halarci atisaye ba ranar Laraba ba, inda hukumar kwallon kafar Sifaniya ta tabbatar cewar ya biya sauran kunshin kwantiraginsa a kungiyar, domin ya kara gaba.
Hadin Lemon Tsamiya (Tamarin Juice) AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Fafata Da Tunisiya A Wasannin RukuniBalladolid ta ce matakin da matashin ya dauka Manchester City ce da wakilin dan wasan suka kitsa komai, ta kuma yi Alla-wadai da wannan lamarin. Dan wasan mai shekara 18 ya koma kungiyar kwallon kafa ta Balladolid daga AIK Freetong, domin buga wasannin aro a bara, inda a watan nan Balladolid ta mallaki dan wasan bayan ya yi kokari kuma ya burge masu koyar da kungiyar. Sai dai Bah yana kan tsarin yarjejeniya ta matashin dan wasa, amma bai amince ya saka hannu ba kan kwantiragi a matakin kwararren dan wasa ba.
Balladolid ta ce za ta dauki mataki na shari’a kan Bah, za kuma ta yi dukkan abin da ya kamata domin ta kare martabarta amma kuma har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ba ga ce komai ba a kan zargin da ake mata na hurewa Bah kunne
এছাড়াও পড়ুন:
Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?
Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu.
A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0.
Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin.
Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai.
Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp