Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka.

Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje.

Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani da dabar barun yaki a tsakaninsu, inda da dama daga cikinsu sojojin kasashen waje ne.

Yace a cikin wadannan atisai daban-daban sun yi amfani da sabbin makamai da kasar ta kera da kuma sabbin dabarbarun yaki. Daga karshe Sayyari ya bayyana cewa mai suna ‘Zulfikar’ sojojin kasar Iran zasu nuna karfinsu a fagen kayakin aikin zamani da kuma sabbin dabarbarun yaki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi  yanki

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza.

Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Gabas, Mohamed Khaled Khari, ya tabbatar da cewa an kashe Falasdinawa kusan 300 a kusa da wuraren raba kayan agaji tun bayan jawabinsa na karshe a watan jiya.

“Mummunan halin da ake ciki a Gaza yana kara tabarbarewa tare da karuwar hasarar rayuka. Dole ne a daina yakin Gaza kuma a sako mutanen da aka yi garkuwa da su. Ayyukan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Deir al-Balah ya haifar da karuwar ‘yan gudun hijira.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fiye Da  Falasdinawa 111 Ne Su Ka Yi Shahada Saboda Yunwa A Gaza
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Fara Tattaunawa kan Masifar Zirin Gaza Na Falasdinu
  • Iran Tace Tawagar Kwararru Daga Hukumar IAEA Zata Ziyarci Kasar Nan Ba Da Dadewa Ba
  • Yan Majalisar Dokokin Kasashen Iran Da Iraki Sun Amince Da Ra’yin Ficewar Sojojin Amurka Daga Iraki
  • Iran Ta Zargi Amurka Da HKI Da Wargaza Dokokin Kasa Da Kasa Da Kuma Yarjeniyoyin Kasa Da Kasa
  • Brazil Ta Shiga Yaki Da HKI, Inda Ta Kudurin Anniyar Goyon bayan Afirka Ta Kudu A Kotun ICJ
  • Sin Ta Yi Mu’amala Da Kasashen Dake Kan Karshen Kogin Yarlung Zangbo Dangane Da Batun Gina Tashar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Kogin
  • Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
  • Zhao Leji Da Wang Huning Sun Gana Da Shugaban Majalisar Dattijan Kasar Madagascar
  • Ministocin Tsaron kasashen Rasha Da JMI Sun Hadu A Birnin Mosco