HausaTv:
2025-11-03@08:49:14 GMT

Kisoshin Rayuwa: Imam AlHassan (a)

Published: 1st, February 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasan ce tare da mu.

///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), sannan dan Fatimah(a) diyar manzon All..(s) na farko.

A cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar cewa bayan da manzon All..(s) ya tabbatar da cewa wafatinsa ya kusa, ta hanyar ayoyin da suka sauko masa, wadanda suka hada ta Suratun-Nasr, sai ya fara tunanin al-ummarsa a bayansa.

Bayan dukkan wahalhalun da ya sha, har zuwa lokacin da mafi yawan kasashen larabawa suka karbi addinin musulunci, duk da cewa wasu sun sallama ne, amma imani bai shiga zuciyarsu ba, kamar yadda All..ya bayyana a cikin alkur’ani mai girma.

Amma da ya fahinci cewa wafatinsa(s) ya kusa, sai ya kira musulmi gaba daya, wadanda suke da ikon zuwa su je aikin hajji tare da shi, to su fita. A dukkan khubobin da yayi, sai ya fada masu cewa, wannan itace shekara ta karshe gareni a nan duniya, mai yuwa ba zamu sake haduwa da ku ba. Amma ina bari nauyaya guda biyu, alkur’ani mai girma, da kuma iyalan gidana, zurriyata, Ahlubaiti ba, da sauransu.

Yayi khuduba a ranar arafah inda ya ce masu kada ku zama kafirai a bayana sashenku yana dukan wuyan sace, sannan ya ce nanata masu riko da alkur’ani da kuma iyalan gidansa.

Amma a khubarsa ta karshe wanda ta kasance a Alhamis 18 ga watan Zulhajji a wani wuri tsakanin Makka da Jufah, wanda ake kira Ghadir Khum.

Mun bayyana cewa aya ta 67 na suratul Ma’ida ta sauka ta umurceshi da ya isar da sakon All..idan kuma baiyi ba to kamar bai iasar da sakonsa gaba da ya ba, sai ya tsaya nan take, aka yi masa mimbari ya hau ya kuma yi khuduba mai tsawo inda a cikinta ya kawo cika-cikan imani, gaba dayansu. Sannan yayi khudubar ya kammala inda kafin ya kammala ya daga hannun Aliyu (..wanda ni shugabansa ne to wannan Aliyun shugabansa ne).

Da wannan khuduba ta gadir ce manzon All..ya kammala isar da sakon All.., sannan bayan wannan bikin na nada Aliyu dan Abitaklib (a) a matsayin sai All..T ya sake aika mala’ika Jibruli ya tabbatar masa cewa ya isar da sakonsa, kuma da wannan sakon All..ya kammala addininsa, ya kuma cika ni’imarsa a kan al-ummar musulmi ya kuma yarje masu addinin musulunci ya zama addini.  Kamar yadda ya zo a cikin wannan yar itama a cikin surarul Ma’ida inda All..yake cewa

{… A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni’imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. …}

Amma ita khudubar ghadir me ta kunsa, kuma da wani tsari manzon All..(s) ya gabatar da ita.

Da farko bayan ambaton sunan All..ya yabonsa kamar yadda ya saba a khudubobinsa, sai ya kawo masu irin ni’iman da All..yayi masu na aiko shi da kuma yadda ya sha wahala wajen bayyana masu gaskiya, da kuma kubutar da su daga bautar gumaka, sannan ya mabici, wasu hukunce-hukuncen sharia da ladubba wadanda ya bukace su su aiwatar da shi a cikin rayuwarsu.

Daga baya, yazo kan cikekken abinda yake son fada a khudubatsa. Sau yace masu {Ku dubi yadda zaku kula da nauyaya biyu da zan bari a cikinku}. Sai wani daga cikinsu ya daga murya yace: Menee Thaqlaini ya manzon All..), sai ya amsa masa da cewa: Nauyi babban shi ne Littafin All…(kamar igiya ce) dayan bangaren na hannun All…mai girma da daukaka, sannan dayan bagaren kuma yana hannunku, ku yi riko da shi ba zaku bata ba.

Sannan dayan kuma (wato nauyi na biyu) shi ne karami, zurriyata. Hakika,(All..T) mai ludufi kuma masani ya fada mani cewa su biyu din nan ba zasu rabu ba har sais un riskeni a taki, kuma na roki Ubangijina kan hakan, kada ku yi gaba da su ku halaka, kada kuma ku yi baya da su ku halaka,

Sannan ya kama hannun Aliyu (s), ya daga, har sai da hasken hamarsu ya bayyana, kuma kowa daga cikin mutane suka gano shi, sannan sai yace: Ya ku mutane, wa yafi cancanta da muminai a kan kawokansu, sai suka ce: All..da manzonsa ne suka sani. Sai manzon All..(s) yace: Lalle All..shi ne shugabana, ni kuma nine shugaban muminai, Kuma ni nafi cancanta da su kan kawukansu, To wanda na kasance shugabansa, to Aliyu shugabansa ne, ya maita hakan har sau ukku, ko kuma har sau hudu.

Sannan yace : Ya ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi ka yi adawa da wanda yake adawa da shi, ka so wanda ya so shi, ka kuma ki wanda ya kishi, ka taimakawa wanda ya taimaka masa, ka taabar da wanda ya taabar da shi, ka jujjuya gaskiya tare da shi , ta duk inda gaskiyar ta juya. Ku saurar, Lallewanda ya ji isarwa baya nan. ! ».

A lokacinda manzon All..(s) ya kammala khudubarsa, mau daukaka, wanda ya cikata da girmama amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), da kuma dora masa, khallifanci mafi girma, sai Haasan Dan Thabit ya tashi zuwa wajen manzon All..(s), inda ya nemi izininsa na tsara wasu baitoci,  don don ambatun wannan manasaba, ko al-amari mai girma da ya faru a wannan ranar, sai yayi masa izini. Sai hassan ya tashi a cikin mutane yana cewa :

Annabinsu yana kiransu a ranar Gadiri-A Khummin, kuma ka saurarri manzon Yana Kira

Sai yace waye shugabanku kuma annabinku-Sai suka ce, basu bayyana Rashin saninsani ba a lokacin.

Ubangojinka shugabammu kuma kaine annabimmu-Ba zaka tarar da masu saba maka ranar kiyama masu saba maka a shugabanci ba-Duk wanda na kasance shugabansa to wannan shugabansa ne-Ku kasance masa mabiya na gaskiya masu bi

A nan sai ya roki Ubangiji, ya jibinci Majibancinsa-Kuma ka kasance makiyin ga wanda yaki Ali.

Sai daga nan musulmi daban-daban suna ta zuwa suna masa mubaya’a, kan khalifanci, suna masa barka-barka, da zama shugaban muminai. Manzon All..(s) ya umurci dukkan matansa ‘Ummahatul Muminin su 9, su wajensa su taya shi murna, Umar dan Khaddabi yana daga cikin wadanda suka bashi hannu, yana cewa: Murna gareka ya kai Dan Abitalib ka kasance shugaba na, kuma shugaban dukkan muminai…

Sannan a wannan rana mai albarka ne, wannan ayar ta sauka, tana cewa

{A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni’imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku} Alma’idah 03.

Hakika ni’imar All…babba ta tabbata, kuma addini ya cika, tareda shugabancin Amirul muminina kuma shugaban masu tsoron All….

Manzon All..(s) ya tabbatar da mataki na karshe, don kare al-ummar musulmi, da kuma shari’ar musulunci, bai bar mutane cikin dimwa, wacce wacce zata jefasu cikin rudu basu san wa yakama, ko ya zama dole su bi shi ba. Sai dai ya nada masu mai shiriyatar da su zuwa hanya madaidaiciya.

Lalle, bai’ar Ghadir tana daga ciki, dalilai masu inganci, kuma wanda yake mafi bayyanar dalili na tabbatar da cewa Khalifanci, da shugabanci bayan manzon All..(s) ta Imam Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Shugabanci a bayan manzon All…(s) ta kebanta a gareshi shi kadai.

Kuma Imam Hassan (a) bayan shahadar mahaifinsa, ya kafa hujjar cewa shugabanci nashi ne bayan mahaifinsa.  

Yayi haka ne a cikin khudubar da Imam Hassan (a) yayi bayan sulhun da yayi da mu’awiya dan Abu sufyan, inda yake cewa :

Mu Ahlul Bait, All..ya girmamamu da addinin musulunci, ya zabemu ya kuma sake zabemmu, ya tafiyar da dauda daga garemu, Ya kuma tsarkakemu tsarkakewa. Kuma mutane ba zasu rabuba sai All..ya sanya mu a cikin mafi alkhairinsu. Wannan daga annabi Adama har zuwa Kakana muhammad (s).

A lokacinda ya aiki shi tare da annabci, ya kuma zabeshi da manzznci, ya sauko masa da littafi, sannan ya umurceshi da kira zuwa ga All..mai girma da daukaka, babana ya kasance na farko wanda ya amsa kira ga All..da manzonsa. Shi ne na farko wanda ya yi imani sannan gaskata All..da manzonsa (s).

Hakki All..ya fada a cikin littafinsa da ya saukar ga annabinsa  manzo.  {Shin wanda yake kan bayyanennen Al-amari daga Ubanginsa, sannan wani mai shaida daga gareshi ya bishi}. Kakana shi ne wanda yake ban baiyanennen al-amari daga ubangijinsa, kuma babana ne ya bishi kuma shi ne mai shaida daga wajensa….har zuwa inda yace.. Hakika wannan al-ummar ta ji kakana, yana fada masu yana fada : Alumma ba zata shugabantar da wani mutum a cikin ta ba, alhali akwai wanda ya fi shi ilmi ba, sai al-amarinsu ya kasance yana yin kasa-kasa, har sais un koma zuwa ga inda suka bari.

Kuma sun ji shi yana fadawa babana : Matsayinka da ni kamar matsayin Haruna da Musa,sai dai kawai babu annabi a bayana, kuma hakaki sun ganshi, kuma sun ji shi a lokacinda ya riki hannun babana a Ghadir Khum, ya fada masu : Duk wanda na kasance shugabansa ne to Aliyu shugabansa ne.

Ya Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi, ka tabar da wannan ya tabar da shi, sannan ya umurcesu da isar da shi ga wanda baya nan.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: masu sauraro wadanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.

Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.

Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin  noma daban daban.

A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.

Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.

Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.

Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.

Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.

Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.

Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam  yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.

Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.

A garin Chuwasu  dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.

Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.

Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.

Yace da farko suna da shakku akan amfani  da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.

Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.

Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar  Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.

A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.

A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.

Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.

Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma