Hisbah Ta Kama Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Aure A Asirce
Published: 30th, January 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta damke wasu matasa a jihar Kano bisa laifin yin aure a asirce ba tare da sanin iyayensu ko amincewar iyayensu ba.
A cewar Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ma’auratan sun yi aure ne a wani wurin shakatawa bayan wani ya dauki nauyin biyan sadaki.
Abubakar ya yi Allah-wadai da wannan auren, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai dace da addinin Musulunci ba, kuma ba a yarda da shi ba.
“Hukumar ta kama ma’auratan kuma za ta ci gaba da bincike tare da kame abokansu da kuma wadanda suka taimaka wajen auren sirri.”
Abubakar ya yabawa wadanda suka sanar da hukumar auren sirri, sannan ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ba a yarda da shi ba+ ga hukumomin da abin ya shafa.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar Hisbah ta jihar Kano na ci gaba da tabbatar da bin doka da oda a jihar.
Daga Khadija Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su.
Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse.
Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban Kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama, Alhaji Sani Sale Zaburan ya bayyana bukatar ganin jami’an ma’aikatar da ke kula da kananan hukumomi a shiyya shiyya suna gudanar da ayyukan su ba tare da jingina da shugabannin kananan hukumomi ba a ko da yaushe amma Kuma su na yiwa kananan hukumomin jagoranci wajen gudanar da sha’anin mulki da harkokin Kudi kamar yadda ya kamata.
Daya daga cikin ‘yan kwamatin Malam Ibrahim Sabo Ahmad Roni ya duba kundin bayanan sha’anin mulki yayin da Oditoci su ka duba kundin bayanan harkokin Kudi tare da yabawa da kuma bada shawarwari da za su inganta ayyukan ma’aikatar.
Da ya ke mayar da jawabi, kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa wanda Babban Sakatare na maikatar ya wakilce shi, Alhaji Muhammad Yusha’u ya ce ma’aikatar ce ke uwa da makarbiya wajen yiwa kananan hukumomi jagoranci a sha’anin mulki da harkokin Kudi da zamantakewa domin kawo cigaba a yankunan karkara.
Kazalika, a daya bangaren kuma, karamin Kwamatin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa ya kafa bisa jagorancin wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza domin duba aikin gyaran gidajen kananan hukumomin jihar 27 da ke kan titin Bypass a Dutse ya mika rahoton sa ga babban kwamatin.
Alhaji Yahaya Muhammad Andaza Wanda sakataren Kwamatin Alhaji Yusha’u Muhammad ya wakilta, ya ce karamin Kwamatin ya duba gidajen Inda ya dauki samfur din yanayin da su ke ciki.
Ya ce daga cikin gidajen akwai wadda ke funskatar matsaloli kamar na tsagewar bango da sanya darduma da kujeru da kayan amfani a dakin girki marasa inganci yayin da ba a mayar da na’urar sanyaya daki a wasu gidajen ba.
Yusha’u wanda shi ne mataimakin Akawun majalisar, ya lura cewa akwai rashin kyawun flasta a wasu gidajen yayin da kan dakin wasu ke yayyo sai Kuma rashin fankar sama da karayyayun kujeru da rashin hada wasu gidajen da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rashin kyawun kofofi da magudanin ruwa da ke kawo barazanar ambaliyar ruwa ga wasu gidajen.
A nasa jawabin, shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomin jihar da su dauki nauyin cikakkiyar kulawa ga gidajen bisa la’akari da dinbin kudaden da aka kashe wajen gyara gidajen.
Usman Mohammed Zaria