Rundunar Ƴansandan Kano Ta Kori Wani Jami’in Saboda Karɓar Na Goro
Published: 30th, January 2025 GMT
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta kori wani jami’in sa-kai, Ado Abba, bisa zargin gudanar da bincike ba bisa ƙa’ida ba da kuma karɓar kudin haram daga jama’a.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ake ganin korarren jami’in tsaye a gefensa domin tabbatar da an san shi.
Ya kara da cewa za a kwace kayayyakin sa-kai daga hannunsa, sannan ya buƙaci jama’a su riƙa kai rahoton duk wani laifi da jami’an ‘yansanda suka aikata. SP Kiyawa ya yaba wa sauran jami’an sa-kai bisa ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro a Kano, tare da yin kira da su ci gaba da aiki da gaskiya da ƙwarewa.
এছাড়াও পড়ুন:
‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.
Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.
Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.
BBC