Bikin Bazara Na Sinawa Ya Zama Biki Na Al’ummar Duniya
Published: 29th, January 2025 GMT
Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya.
A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a fadin duniya sun hadu domin a dama da su cikin bikin murnar sabuwar shekarar ta Sin.
Hakan ba ya rasa nasaba da yadda al’adar ta taba kowanne bangare na rayuwa da kuma sakonnin da take dauke da su kamar na kyautata zumuncin iyali da girmama manya da tausayawa yara, wanda abubuwa ne dake da saukin fahimta ga jama’ar dukkan kasashe. A lokacin guda, ta hanyar bikin bazara, duniya ta ga kasar Sin dunkulalliya mai bude kofa, haka kuma ta shaida nasarorin da kasar ta samu wajen zamanantar da kanta.
Sinawa na mika fatansu na ban kwana da tsohuwar shekara da maraba da sabuwa ga duniya ne ta hanyar bikin bazara. Bikin bazara ba na Sin ba ne kadai, na daukacin duniya ne. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
কীওয়ার্ড: bikin bazara Bikin bazara
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama.
A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar da kisan kare dangi kai tsaye a tauraron dan Adam a Zirin Gaza.
Ta kara da cewa, “Sun ga kasashe kamar babu abin da zasu iya saboda da rauni” tare da nuna cewa “gwamnatin mamayar Isra’ila na kashe dubban Falasdinawa maza da mata, ta hanyar kisan kiyashi kan dukkanin iyalai da suka hada da kananan yara, da lalata gidaje, rusa cibiyoyin tsare rayuka, rusa asibitoci da cibiyoyin ilimi.