Amurka Zata Fitar Da Dokar Hukunta Kotun Kasa Da Kasa Saboda Zargin Isra’ila Da Kotun Ya Yi
Published: 29th, January 2025 GMT
Majalisar Dokokin Amurka zata dauki matakin fitar da dokar da zata hukunta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya saboda kotun ta tabbatar da zarge-zargen manyan laifukan gwamnatin mamayar Isra’ila
Ana sa ran nan kusa kadan Majalisar Dattawan Amurka za ta fara kada kuri’a kan kakaba takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague, bayan da kotun ta tuhumi fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohun ministan yakinsa Yoav Gallant a watan Mayu da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Zirin Gaza.
A cewar jaridar Washington Post, ‘yan majalisar dokokin Amurka suna matsawa wajen zartar da dokar, wadda za ta sanya takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, yayin da wasu daga cikin manyan kawayen Amurka na kasashen Turai suke fargabar cewa: Dokar za ta gurgunta babbar kotun hukunta manyan laifukan ta duniya tare da baiwa masu aikata laifukan yaki damar cin karensu ba babbaka ba tare hukunta su ba, kuma hakan zai raunana mutuncin kasashen yamma”.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kotun hukunta manyan
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.