HausaTv:
2025-05-01@03:38:39 GMT

Jagora: An Murkushe Dukkanin Daidaito A Gaban Mutanen Kudancin Kasar Lebanon

Published: 27th, January 2025 GMT

Jagoran juyin juya halin Musulunci: An murkushe dukkanin daidaito a gaban mutanen kudancin Lebanon

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana abin da ya faru a kudancin kasar Lebanon a matsayin murkushe dukkanin daidaito na siyasa da lissafin abin duniya.

A cikin wani rubutu a dandalin “X”, Ayatullahi Sayyid Khamenei ya nuna cewa an murkushe wadannan daidaito a gaban mutane masu aminci da aminci a kudancin Lebanon.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la’akari da cewa: Al’ummar kudancin kasar Labanon ba su damu da sojojin yahudawan sahayoniyya da suka yi kaca-kaca da su ba, suna kuma kai rayukansu zuwa fagen fama da rashin son kai da kuma dogaro da alkawarin Ubangiji.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya.

A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran mai girma. Qalibaf ya yi nuni da cewa, wannan mutum mai rauni yana son canza haryar tafiyarsa a kullum rana saboda tsoron kada a kama shi sakamakon kasancewarsa mai laifi da yafi zama abin ki a tarihin wannan zamani.

Qalibaf ya kara da cewa; Bayan shafe shekaru da dama Netanyahu yana yaudarar kafafen yada labarai, a halin yanzu gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta fito fili kuma ta bayyana hakikanin fuskar wannan azzalumi ga duniya, musamman ga matasan Amurka da Turai. Qalibaf ya kara da cewa babu wani abin da wannan gwamnatin ta cimma sai kai hare-haren bama-bamai kan makarantu da asibitoci, kuma ba ta cimma burin da ta ayyana a farkon yakin ba, kuma halin da ake ciki yana da matukar rashin tabbas.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Munafunci Dodo Ya Kan Ci Mai Shi
  • Saudiya Ta Yi Allawadai Da Kissan Kiyashin Da HKI Take Yi A Gaza A Gaban Kutun ICJ
  • Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
  • Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasu
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
  • Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
  • Jagora Ya Bada Umurnin A Gudanar Bincike Mai Zurfi A Fashewar Tashar Jiragen Ruwa Na Shaheed Rajae
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut