2025-09-17@23:26:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7238
«Ruwan Sama»:
Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa Samun Lambar Tantance Haraji (Tax ID) zai zama wajibi ga duk ƴan Nijeriya da ke hulda da bankuna da sauran ayyukan hada-hadar kudi daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon umarni yana cikin Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya, 2025, wacce shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kwanan...
A cewar sanarwar, bisa wannan sanarwar, fadar ta shugaban ƙasa, ta yanke duk wata huɗɗa da Umunubo. Sanawar ta kuma jaadda cewa, ya zama wajbi ɗaukacin masana’antun da ke a ƙasar nan, su nesanta kansu, da yin dukka wata huɗɗa da Umunubo da sunanan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu. Idan za a iya tunawa, Jaridar...
An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar...
Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!. Da daman mutane ba sa zaɓar wani kansila...
“Shawarar tsarin shugabancin duniya” ta zama kalmar da aka sha karanta a rahotannin kafofin watsa labaru na duniya cikin kwanakin baya. Shugabannin wasu kasashe da dama suna ganin cewa, wannan shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin taron koli na SCO da aka gudanar a kwanan baya a birnin Tianjin, tana...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
Misali, ya sauya lokacin da aka tsara yin wasan sada zumunta da ƴan ƙasa da shekara 20 na ƙungiyar Flamengo a lokacin da Leɓerkusen ta je atisaye a Brazil. An buga wasan kwana biyar kafin ranar da aka tsara tun farko, inda Leɓerkusen ta sha kashi da ci 5-1. Haka nan a kusan wannan lokacin...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta raba wa mutum 2,261 da ambaliyar ruwa ta shafa a Potiskum, Nangere da Jakusko a Jihar Yobe, kayan agaji. An raba kayan ne a unguwanni 21 na Potiskum, ƙauyukan Kolo da Ajim a Nangere, da kuma kauyukan Dachia, Yim, Saminaka, Garin Maji da Amshi a Jakusko. Gwamnati...
An karrama fitattun fina-finai daban daban a bikin “Golden Panda” da ya gudana jiya Asabar a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kasar Sin. A bana, an gudanar da bikin ne a karo na biyu, wanda kuma gungun sassan bunkasa harkokin adabi da al’adu da gwamnatin lardin Sichuan suka dauki nauyin shirya shi. Bikin na...
A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri. “Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin...
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi cewa jihohi 11 na iya fuskantar ruwan sama mai yawa wanda ka iya haddasa ambaliya daga ranar Lahadi zuwa Alhamis. A cikin sanarwar da Cibiyar Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli, ta fitar, jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Adamawa, Benuwe, Nasarawa, Taraba da Delta. An yi...
A cewar kakakin ‘yansandan, jami’an sun tare wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka mai lamba GGE 473 BH bayan direban ya kasa bayar da kwakkwaran bayanin kansa da kuma motar. Ya bayyana cewa binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano wata bindiga da aka kera a cikin gida,...
Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba 001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma...
An yi wa ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Jihar Akwa Ibom ruwan kuɗi, bayan sun yi fice a gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa da aka yi wa laƙaba da IBOM 2025, wacce aka kammala a ƙarshen makon nan. Gwamna Umo Eno, ya bai wa gwarazan ’yan wasan da suka lashe kambin Zinare kyautar...
Hakazalika, sojojin na Brigade 12 tare da hadin gwiwar dakarun hadin gwiwa da ’yan banga a wannan rana, sun ceto fasinjoji 17 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi. Hakazalika, dakarun Sashe ta 1 ‘Operation Whirl Stroke (OPWS)’ sun ceto wani a karamar hukumar Katsina-Ala...
Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan...
Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya ne daga cikin jiga-jigan da aka kafa masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood da su. A cikin wannan tattaunawar, ya bayyana cewa bai taɓa yin da-na-sanin shigarsa sana’ar ba, sannan ya bayyana dalilin da yanzu ba a cika ganin sa sosai a fina-finai ba, da...
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin...
Kona mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, a cikin dare mai wahala ga zirin Gaza Da sanyin safiyar Lahadi 14 ga watan Satumban shekara ta 2025 jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, musamman birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata...

Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba
Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar...
Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya,...
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar korar Falasɗinawa sama da mutum 250,000 daga birnin Gaza tun bayan da suka fara zafafa kai hare-hare a yankin. Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an Falasɗinu suka ce da dama sun gaza ficewa daga kudancin ƙasar saboda cunkoso. Najeriya ta daɗe tana fama da...
Aƙalla mutane 19 ne suka mutu a yayin da suka ɗauko wata amarya zuwa ɗakin mijinta bayan motarsu ta faɗa a ƙarƙashin gadar Gwalli da ke yankin Fass a Ƙaramar Hukumar Gummi a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar da misalin ƙarfe 4:45 na yamma, lokacin da motar, da ke ɗauke da...
Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar...
A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata. Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba...
Haka kuma, kamfanonin gwamnatin tarayya da suka durƙushe a jihar sun haɗa da: Nigeria Paper Mill, Jebba; Nigeria Sugar Company, Bacita; da Nigeria Yeast and Alcohol Manufacturing Company, Bacita. Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin Arewa Wajen Amincewa Da Kafa Ƴansandan Jihohi...
A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan. Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta...
Rahotanni sun bayyana cewa kasar masar ta bayyana cewa Isra’ila na shirya makarkashiyar kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta, don haka ta gargadi tel aviv da cewa duk wani hari dai dai yake da shelanta yaki kuma za su daga mata kafa ba, Wata majiyar labarai ta bayyana cewa jami’an kasar masar sun yi kira...
Gwamnatin Jihar Kuros Riba, ta ce ta gano ma’aikatan bogi har guda 800 a wasu ma’aikatun jihar. Tun da farko, an daɗe ana zargin gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Farfesa Ben Ayade da biyan albashi ga wasu mutane da ba ma’aikatan gwamnati ba, musamman a ƙananan hukumomin jihar. HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun...
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta fara bincike kan kisan wasu mutum huɗu da ’yan bindiga suka yi lokacin da suke zaman makoki. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa masu makokin wuta ne a ranar Alhamis a garin Ogidi, da ke Ƙaramar Hukumar Idemili. Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200...
Sojojin Nijeriya a ƙarƙashin Operation ACCORD III sun kashe wani fitaccen shugaban ƴan ta’adda mai suna Babangida Kachala a jihar Kogi. Wannan na zuwa ne bayan samun bayanan sirri da aka samu kan motsin ƴan ta’adda a dajin Ofere da yankin Ayetoro Gbede. Bayanin da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na Sojoji, Laftanar Hassan Abdullahi,...
Dokar Tsabtace Amfani da Wuta ta Ƙasa. Dokar Gyara Yanayi ta Ƙasa. Hanzarta Ba da gargaɗi. Wayar da kan jama’a kan haɗarin ambaliyar ruwa. Tilasta dokokin muhalli. Horarwa da sabunta ƙwarewar jami’ai ƙwararru. Shigar da kayan aiki na zamani, da sauransu. Har ila yau, ya bayyana cewa za a iya sarrafa ambaliyar ruwa ta hanyoyi...
Dokar ta ba da damar dakatarwa na ɗan lokaci ko kuma cire rajistar Tax ID gaba ɗaya idan mai riƙe da shi ya daina gudanar da kasuwanci. A gefe guda, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Nijeriya, 2025, ta ba Shugaban Zartarwa na Hukumar babban ikon, wanda zai kasance shugaban Kwamitin Gudanarwa na hukumar. Kwamitin zai...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya...
Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da...
Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani...
Fitaccen ɗan wasan ya tuna wani lokaci da aka kama shi bayan ya tsaya wa wani a kotu wanda ya gudu, amma aka sake shi saboda shahararsa. Duk da ɗansa na daga cikin manyan masu gyaran hotunan Fim (editing ), ya ce matsayin da Allah ya ba shi a harkar fim alheri ne na ƙaddara....
Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina...
Tabbatar da dakatar da amfani da HCFC-141b a tsarin sandwich panel, spray, da block a ayyukan cikin gida na Vitapur. Daraktan Zartarwa na Vitapurs Ltd, Mista Taiwo Adeniyi, a jawabin maraba da ya yi, ya bayyana cewa cibiyar za ta ƙara ƙwarewa wajen gwaje-gwaje, bincike, da horo tare da amfani da sinadarai masu ƙarancin GWP,...
Chef Hilda Baci mai shekara 28 ta kama hanyar kafa sabon tarihin girka shinkafa dafa-duka (Jollof) ’yar Najeriya mafi yawa a duniya. Hilda Baci ta kafa wannan sabon tarihi ne inda ta girka shinkafa basmati buhu 200 a wata katafariyar tukunya a bainar jama’a. Ta yi wannan sabon abin bajinta ce shekara biyu kacal bayan...
“Haka zalika, shi ma matuƙin babur ɗin; ruwan ya yi awon gaba da shi,” a cewar tasa. Ganau ɗin ya ci gaba da cewa, wani ƙwararre a fannin iya ruwa; nan da nan ya garzayo tare da yin sufa a cikin ruwa, domin ƙoƙarin ceto su, amma tuni ruwan ya riga ya yi awon gaba...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo...
Akalla Falasdinawa 64,756 sukayi shahada a kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da ke kewaye. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce an kawo gawarwakin mutane 38 da suka hada da biyu da aka zakulo daga baraguzan gine-gine a cikin sa’o’i...
Ya ƙara da cewa a faɗin Afirka, bashi ya zama babban ƙalubale ga tattalin arziki, inda ƙasashe da dama ke kashe fiye da kuɗin kiwon lafiya wajen biyan bashin da suka ci. Ya ce kashi 35 cikin 100 na bashin ƙasashen Turai na daga masu ba da rance masu zaman kansu ne, kashi 39 daga...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama buhu 150 maƙare da tabar wiwi a yayin da ake tsaka aikin ceto bayan wani hastarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano. Hukumar ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne tsakanin wata mota ƙirar Volkswagen Golf da wata...
Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka. A cewar ma’aikatar, bangarorin...
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama jabun magungunan zazzaɓin cizon sauro (maleriya) da darajarsu ta kai sama da Naira biliyan ₦1.2bn a Legas. Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a a shafinta na sada zumunta X, inda ta ce...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara. Za a raba Naira...