2025-09-17@22:19:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 37
«rabon kayayyakin»:
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250 ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi. Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar. Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki. Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa...
Rahotanni sun bayyana cewa kasar iran ta bayyana sabbin kayayyaki guda 5 da ta kera a wajen babban taron kere-kere na kasa da kasa karo na 23,kuma dukkansu kamfanonin kasar iran ne suka yi su domin rage dogaro da kayyakin kasashen waje. Taron ya samu halartar mataimakin shugaban hukumar kula da kimiya da fasaha ta kasa da sauran shuwagabannin kamfanoni inda ya nuna irin karfin iran wajen kere-kere da kuma mayar da hankali kan kamfanoni dake filin shakatawa na pardis technology park. Daga cikin magungunan da aka gabatar a wajen akwai Sirolimus wanda Zist takhmir company ya kera, kuma magungunan rigakafi ne da ake amfani da su wajen hana dashen gabobin jiki da kuma kula da cututtuka da ba kasafai...
Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Iran ta ce kasar ta aike da kayayyakin jin kai zuwa yankunan da girgizar kasa ta shafa a gabashin Afghanistan. Razieh Alishavandi, jami’i daga kungiyar, ya bayyana cewa, Iran ta tura sama da tan dari na kayayyakin ceton rai zuwa Afghanistan. A cewar Alishavandi, wannan agajin ya hada da abinci, tantuna, barguna, tufafi, da dai sauran abubuwa masu muhimmanci na matsugunin gaggawa da tallafi ga mutanen da girgizar kasar ta shafa a Afghanistan. Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran “Koyaushe kamar yadda ta saba, za ta tsaya da dukkan karfinta ga mutanen Afghanistan a cikin wnnan lamarin,” in ji shi . A ranar Lahadin da ta gabata, ce girgizar kasa mai...
Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da Hukumar FAAN ta shirya domin sanar da shirin fara jigilar kayayyaki a Filin Jiragen Sama na Ƙasa da Ƙasa na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilori. A cewarsa, wannan shiri na nufin kara inganta matsayin jihar tare da ƙarfafa rawar da take takawa a harkokin kasuwanci na cikin gida da waje. Ya jaddada cewa aikin ya yi daidai da manufofin wannan gwamnati na buɗe sababbin...
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara a watan Yuli 2025 ya kai kashi 22.74%, wanda ya ragu da maki 16.79% idan aka kwatanta da kashi 39.53% da aka samu a Yulin 2024. NBS ta danganta wannan raguwa mai yawa da sauyin shekarar wajen lissafi. Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Kashi 34.80 A Disamban 2024 – NBS Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan...
Kungiyoyin kasa da kasa guda 100 sun koka kan yadda gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi watsi da bukatu har 60 kan ba da damar shigar da agaji zuwa Gaza Sama da kungiyoyi masu zaman kansu 100 ne suka bayyana a wata wasika ta hadin gwiwa da aka buga jiya alhamis cewa, ana kara amfani da sabbin dokokin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta tsara kan ayyukan kungiyoyin agaji na kasashen waje wajen kin amincewa da bukatarsu ta shigar da kayayyaki zuwa zirin Gaza. Wasikar ta ce: “Hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila sun yi watsi da bukatar da kungiyoyi masu zaman kansu da dama suka gabatar na kawo kayayyakin ceton rai, lamarin da ya bar miliyoyin daloli na agajin jin kai da suka...
Ejodame ya rahoto CAS, yana cewa “Tare da ingantattun jirage da ke da ingantattun tsare-tsaren kai hare-hare na dare, jirgin NAF ya kai hare-hare guda 798”. A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yabawa NAF bisa ci gaba da bayar da tallafi ta sama wajen gurgunta karfin ‘yan ta’adda da kuma kare al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Talata 12 ga wata cewa, bisa dokoki ko ka’idojin da suka shafi saka wasu sassa cikin wadanda aka sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, ma’aikatar ta fitar da sanarwa mai lamba 21 da ta 22 a ranar 4 da kuma ranar 9 ga watan Afrilun bana, inda ta saka wasu sassa 28 na Amurka cikin wadanda ta sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, wato hana sayar musu kayayyakin amfanin jama’a da ake iya amfani da su a bangaren soja. Har wa yau, domin tabbatar da matsayar da aka cimma a wajen shawarwarin manyan jami’an Sin da Amurka a bangaren tattalin arziki da cinikayya, an yanke shawarar cewa,...
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza. Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin kwace birnin Gaza tare da mamaye shi, Shugaban gwamnatin Jamus Merz ya ce Berlin na ci gaba da ba da goyon baya ga ‘yancin “Isra’ila” na kwance damarar Hamas tare da ganin an sako fursunoni, amma kuma duk da haka basu goyon bayan duk wani mataki zai kai ga kara tabarbarewar lamurra na jin kai a Gaza. “Gwamnatin Jamus ta yi imanin cewa matakin soji...
A karon farko, filin baje hajoji masu nasaba da taron ya kai sama da sakwaya mita 70,000, kana adadin kamfanoni mahalarta taron sun haura 800, yayin da aka gabatar da kayayyaki sama da 3,000, wadanda suka hada da manyan na’urori da masu amfani da fasahar AI, da mutum-mutumin inji. Kana an gabatar da sabbin kayayyaki sama da 100 da aka gabatar da su a karon farko. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Mun kasance muna jiran a ba mu garin alkama, saboda muna jin yunwa sosai, muna neman abin sha da abinci, kwatsam tankokin sojan Isra’ila suka zo suka kewaye mu, suka fara harba bindiga a kanmu, ba mu iya motsawa ba. Ba mu samu gari ba, an kuma kewaye mu na tsawon sa’a daya da rabi zuwa biyu, wasu sun gudu, wasu an kashe su, wasu kuma sun ji raunuka.” In ji wani dan Gaza game da abin da ya faru gare shi a ranar 21 ga wata. Tsawon kwanaki 140 ke nan da Isra’ila ta rufe hanyoyin shiga Gaza. A halin yanzu, kashi 93% na iyalai a Gaza ba su da ruwan sha, kuma fiye da kashi 87% na yankunan...
Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe, sun fara rabon kayayyakin gini ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomi 13 na jihar. Wannan taimako na da nufin tallafa wa mutanen da ambaliya ta rushe musu gidaje. Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano A lokacin da aka fara rabon kayayyakin a Damaturu, wakilin babban daraktan NEDC, Farfesa Ibrahim Ali Abbas, ya ce hukumar ta kawo kayayyakin rufin gida da sauran kayan gini don taimaka wa mutane su gyara ko sake gina gidajensu. Baya ga wannan, hukumar ta kuma bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa...
Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai wajen tabbatar da tsafta da kuma bayar da rahoton duk wani da ake sayarwa da ba bisa ka’ida ba, ko kuma cikin rashin tsafta. Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan kira ya zama wajibi sakamakon nasarar da hukumar ta samu na kwace gurbatattun kayayyakin na sama da naira miliyan 14 a lokacin sintiri da binciken kayayyaki a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025. Alhaji Adamu Sabo ya kara da cewa, mafi yawancin kayayyakin da aka kwace na...
A yau Jumma’a 27 ga watan Yunin ne a hukumace aka bude hanyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa da za ta rika aiki a kai a kai, daga Urumqi, yankin jihar Xinjiang ta kasar Sin zuwa Addis Ababa na kasar Habasha. Wannan kuma ita ce hanyar jigilar kayayyaki ta farko daga Xinjiang zuwa Afirka da kuma tasowa daga can. Hanyar jigilar kayayyakin daga Urumqi zuwa Addis Ababa na gudanar da tafiye-tafiye na zuwa da dawowa kowace Litinin da Alhamis. Bude sabuwar hanyar ba wai kawai ya kaddamar da wata hanya ce mai sauri ta yadda ‘ya’yan itatuwa masu inganci da sauran kayayyakin aikin gona na musamman na jihar Xinjiang za su isa Afirka kai tsaye ba ne, har...
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin. Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa. “Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga...

Kwastam Ta Kama Jirage Marasa Matuka Da Sauran Kayayyaki Da Darajarsu Ta Haura Naira Biliyan 921 A Legas
Ya bayyana cewa, ziyarar da ya kai a tashar ruwa ta PTML da Tin Can na da nufin sanin irin kalubalen da jami’an sa ke fuskanta wurin amfani da sabuwar na’urar zamani domin binciken kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Ya kuma kara gargadin jama’a game da karuwar kwararowar magunguna kasar da ba su da rajista, musamman magungunan inganta jima’i, inda ya yi gargadin cewa irin wadannan abubuwa na da matukar barazana ga kiwon lafiyar jama’a. Ya yi gargadin cewa, yin amfani da wadannan magungunan ba tare da kulawar likitoci ba zai iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jiki, ciki har da haɗarin cututtukan zuciya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar. Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar. A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai. Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu. Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa...
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu kansu biyo bayan maida martani da China tayi na ramuwar gayya. Domin kuwa sai da gwamnatin America ta kashe kimanin dala biliyan 30 wajen tallafawa manoman kasar kan asarar da suka tafka, biyo bayan harajin da China ta kakabawa wasu daga cikin amfanin gonar America da ake shigar da su China. Sabo da haka a nan za mu iya bugun gaba mu ce “Kwalliya...
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA, ta yi nasarar kama hodar iblis wadda aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi. Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas Hukumar ta bayyana cewa ta kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini. NDLEA ta ce jami’anta sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata. Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki karkashin manufofin Trump. Domin mayar da martani, Tarayyar Turai za ta aiwatar da ayyuka, galibi an saita su a kashi 25%, kan nau’oin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka, wanda zai fara daga ranar Talata mai zuwa a matsayin martani na musamman ga harajin karafa na Amurka. Kungiyar har yanzu tana kimanta tsarinta na magance tasirin karin haraji. Kayayyakin na Amurka da tsarin...

Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni. Ban da haka kuma, ma’aikatar ta ce kasar ta kara sunayen wasu kamfanonin Amurka 6, cikin jerin sassan da ba za a iya dogaro da su ba. Ma’aikatar wadda ta bayyana hakan a Larabar nan, ta ce kamfanonin su ne Shield AI, da Sierra Nevada Corporation, da Cyberlux Corporation. Sai kuma Edge Autonomy Operations LLC, da Group W and Hudson Technologies. Tun daga karfe...

Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko ta fannin a duniya. Har wa yau, daga cikin tashoshin jiragen ruwa 10 da suka fi hada-hadar kayayyaki a duniya, akwai tashoshin jiragen ruwan kasar Sin guda 8, ta fannin hada-hadar kwantenoni kuma, guda 6 na kasar Sin ne. (Mai fassara: Bilkisu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata. Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu na bana, masana’antar samar da kayayyaki na samun saurin bunkasa, inda ribar da kamfanoni da masana’antu da ke iya samun ribar da ta zarce dala miliyan 2.7 a duk shekara, ta karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, masana’antar ba da hidima ta fi samun bunkasuwa, inda alkaluman ci gabanta suka karu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin bara, kuma...
A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare. Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta kaddamar da rabon kayayyakin noman rani da kayan abinci na watan Ramadan ga manoma da al’ummar jihar, inda ta umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana sayar da kayan abinci da na aikin noma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon, gwamnan jihar, Kwamared Nasir Idris ya bayyana cewa, matsakaitan manoma 200,000 a fadin kananan hukumomin jihar 21 ne za su ci gajiyar shirin. Gwamnan ya bayyana cewa, samar da kayan aikin gona ga manoma zai taimaka wajen bunkasa samar da abinci a jihar. Ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da kuma jami’an gwamnati da ke da alhakin rabon kayayyakin, da su tabbatar da an yi adalcin wajen rabon kayayyakin....
Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci. Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo. Basaraken ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta. Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba. “Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun fara raba kayayyakin tallafi ga mutum 507 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar a 2024. An gudanar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a a Ƙananan Hukumomin Kibiya da Madobi, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa kayayyakin ga waɗanda suka ci gajiyar shirin. Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ne, ya wakilci gwamnan. Gwamnan, ya gode wa NEMA bisa goyon bayan da ta ke bai wa jihar, tare da yaba wa SEMA saboda jajircewarta wajen...
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
“Jami’anmu na kara zage damtse wajen ganowa tare da wargaza ma’ajiya da wuraren ajiya ba bisa ka’ida ba inda ‘yan fashin suka rika tara kayayyakin da aka sace. Dole ne FCT ta kubuta daga hannun wadannan miyagun abubuwa.” Aikin dai ya biyo bayan nasarar da aka samu a makon da ya gabata inda rundunar tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya kafa, suka kama tare da kwato kayayyakin more rayuwa da aka lalata. Disu ya yaba wa mazauna yankin bisa ci gaba da ba su goyon baya, ya kuma bukace su da su kasance cikin taka tsan-tsan, yana mai jaddada cewa kare kadarorin jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyansu....
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda. A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin da wadanda abin ya shafa ke ciki. Babbar Daraktar wanda shugaban NEMA shiyar Sokoto, Aliyu Shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce tallafin ya hada da kayan abinci kamar buhunan shinkafa, da masara, da man girki, da kayayyakin amfani gida. A baya dai Hajiya Zubaida Umar ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda har yanzu suke ci gaba da karbar magani a asibitin...
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis. Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin. Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa...
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara? Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba. Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....