Karamar Hukumar Sule Tankarkar Ta Raba Kayayyakin Tallafi Ga Al’ummarta
Published: 26th, January 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin.
Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar.
Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban.
Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban.
Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar.
Wakilinmu ya aiko mana da rahoton cewar, an gudanar da rabon tallafin wanda ya hada da tallafin karatu ga matasa 80 da aka sama musu guraben karatu a manyan jami’o’i da kwalejoji a faɗin kasar nan, da rabon babura ga mutane 30, sai keken ɗinki da aka rabawa mata 30.
Kazalika, an raba kekunan hawa 30 ga ɗalibai, da injin niƙa guda 10 da aka rabawa matsakaitan ‘yan kasuwa.
Sai kuma tallafin jari na naira dubu dari 2 da aka rabawa ‘yan kasuwa har su 20 da tallafin jari na naira dubu 100 ga ƙananan ‘yan kasuwa guda 20.
Sauran su ne tallafin jari na naira dubu hamsin hamsin ga mutane 30, da kuma bayar da naira dubu ashirin ashirin ga mutane 100, domin rage radadin halin da ake ciki, da rabon shagunanan tafi da gidanka guda 3 ga matasa masu kasuwanci.
Har ila yau, an raba babura masu kafa 3, na daukan kaya guda 2 ga matasa, sai kuma bayar da mukullin gidaje masu ɗaki biyu ga matasa guda 4 daga sassa daban-daban na karamar hukumar Sule Tankarkar.
A don haka, Gwamnan ya yi kira ga sauran shugabannin ƙananan hukumomi na jihar da su yi koyi da irin wannan gagarumin aikin na Tasiu Adamu domin al’umma su ci gaba da sharbar romon mulkin dimokradiyya.
Ya bayyana cewar irin waɗannan ayyuka ne ke taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci da samar da ayyukan yi ga jama’a.
Taron ya samu halartar jama’a daga sassa daban-daban na jihar, inda aka bayyana wannan shiri a matsayin abin alfahari ga al’ummar Sule Tankarkar da Jihar Jigawa baki daya.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa.
Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum.
A wajen kaddamar da shirin a filin wasa na Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin yana da manufa ta musamman domin tallafa wa jama’a kai tsaye. Ya ce ƙungiyoyin NURTW da mahauta suna da matuƙar tasiri, ba kawai ga membobinsu ba, har ma da al’umma gaba ɗaya, shi ya sa gwamnatinsa ta ga dacewar tallafa musu.
Gwamnan ya kara da cewa taimakon da aka bai wa waɗannan ƙungiyoyi zai kara habaka tattalin arzikin al’ummar jihar. Ya yabawa ƙungiyoyin bisa yadda suka tsaya tsayin daka wajen kare muradun membobinsu.
Ya bukaci shugabannin ƙungiyar da su tabbatar da sa ido sosai da kuma ganin cewa an bi dukkan sharuddan shirin. “Hakan zai tabbatar da cewa motocin sun yi aiki daidai da manufa, tare da bai wa shirin damar dorewa da kuma faɗaɗawa don amfanar da wasu a nan gaba’. In ji shi.
Gwamnan ya yaba da rawar da NURTW ke takawa a tattalin arzikin jihar, yana mai bayyana su a matsayin muhimmin ɓangare na samar da kayayyaki, ko a fannin noma, masana’antu ko kasuwanci. Ya ce babu wata harkar rarraba kaya da za ta yi tasiri ba tare da haɗin guiwar NURTW ba.
A cewarsa, gwamnatinsa na saka jari mai yawa a fannin gina hanyoyin mota, inda aka kammala ayyukan hanya guda 26 da aka gada, da kudin da ya kai sama da naira biliyan 100. Haka kuma, an ƙara bayar da kwangiloli don gina tituna 50 masu tsawon fiye da kilomita 850, da kudinsu ya haura naira biliyan 300.
Gwamnan ya bayyana cewa an fara amfani da hanyoyin makamashi masu tsafta, inda aka kusa kammala cibiyar sauya motoci zuwa CNG a jihar. Ya ce wannan cibiya za ta taimaka matuƙa wajen rage farashi da kuma tsaftace muhalli, tare da fa’ida kai tsaye ga ƴan NURTW.
A wani ɓangare na shirin, Gwamna Namadi ya kaddamar da tsarin lamuni na naira miliyan 113 ga ƴan kungiyar mahauta. Shirin zai taimaka wa mutane 53, inda manyan ‘yan kasuwar dabbobi 15 za su samu naira miliyan 5 kowanne, sai sauran 38 da za su samu miliyan 1 kowanne.
Ya ce ana sa ran wannan tallafi zai taimaka wajen bunkasa harkar kiwon dabbobi da samar da nama a jihar, har da kasuwannin nama gaba ɗaya.
Don tabbatar da dorewar wannan ci gaba, gwamnan ya bayyana shirin kafa sabuwar ma’aikatar ci gaban kiwo a jihar.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa a matakin farko na shirin, an raba motoci 36 na kasuwanci da darajarsu ta kai naira miliyan 279.3, tare da inshora, ga membobin NURTW karkashin tsarin lamuni na juyi da hukumar Youth Economic Empowerment da Employment ta jihar ke jagoranta.
Usman Muhammad Zaria