An Yi Kira Ga Manoma Da ‘Yan Kasuwa Da Su Kara Sassauci A Farashin Kayayyaki
Published: 24th, February 2025 GMT
Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci.
Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo.
Basaraken ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta.
Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba.
“Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a yau, ya biyo bayan yakin da Gwamna Kefas ya yi da wajen tabbatar da ganin an shawo kan matsalar tsaro a Taraba, tare da wanzar da zaman lafiya, ba a Jalingo kadai ba, har ma a jihar Taraba baki daya, wanda ya baiwa jama’a damar samun hanyoyin samun kudaden shiga na yau da kullum“. Inji shi.
“A matsayina na babasaranaina shiga cikin damuwa matuka a duk lokacin da jama’ata suka gaza shiga gonakinsu ko gudanar da sana’o’insu saboda rashin tsaro. Ina son in yaba wa gwamna Agbu Kefas bisa gaggarumin yaki da rashin tsaro a Taraba, wanda sannu a hankali ana samun kwanciyar hankali a halin yanzu.
Tun da farko, shugaban taron, Alhaji Kabiru Marafa, da Lamido Bakundi, mai martaba Alhaji Kabiru Muhammad Gidado Misa, sun bayyana Galadima a matsayin basarake abin koyi, wanda ake alfahari da ayyukansa da jagororinsa.
Jamila Abba
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA