Masana’antar Kera Kayayyakin Laturonin Sadarwa Ta Sin Ta Samu Ci Gaba Mai Sauri A 2024
Published: 8th, February 2025 GMT
Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis.
Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.
Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa yuan biliyan 640.8.
Daga cikin manyan kayayyaki, an samar da jimillar wayoyin salula biliyan 1.67 a shekarar 2024, karuwar kashi 7.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023. Kana, an kera kimanin wayoyin salular fasahar zamani biliyan 1.25, wanda ya karu da kashi 8.2 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
কীওয়ার্ড: ya karu da kashi shekarar 2023
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu.
Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba da tafiyarsu cikin tsaro.
Shugaban Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tsayin daka kan aiki.
Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp