Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi
Published: 22nd, February 2025 GMT
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun fara raba kayayyakin tallafi ga mutum 507 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar a 2024.
An gudanar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a a Ƙananan Hukumomin Kibiya da Madobi, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa kayayyakin ga waɗanda suka ci gajiyar shirin.
Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ne, ya wakilci gwamnan.
Gwamnan, ya gode wa NEMA bisa goyon bayan da ta ke bai wa jihar, tare da yaba wa SEMA saboda jajircewarta wajen tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda abin ya shafa.
“Muna da niyyar ci gaba da aiki tare da hukumomin da suka dace don inganta shirye-shiryen daƙile iftila’i a Kano,” in ji shi.
“Gwamnati za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa don kare lafiyar jama’a.”
Daraktar Janar na NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta ce wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na taimaka wa waɗanda ambaliya ta shafa.
Ta hannun Kwamandan NEMA a Kano, Dokta Nura Abdullahi, ta bayyana cewa an amince da tallafin ne bayan Gwamnatin Tarayya ta karɓi rahoto kan ɓarnar da ambaliyar ta haifar.
“Gwamnatin Tarayya tana jajanta musu kan yanayin da suka shiga,” in ji ta.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhu 500 na shinkafa mai nauyin kilo 25, buhu 500 na masara mai nauyin kilo 25, katan 45 na tumatirin gwangwani, katan 45 na man girki, katan 45 na maggi, da buhu 20 na gishiri.
Sakataren Zartarwa na SEMA, Alhaji Isyaku Kubarachi, ya buƙaci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya dace.
Wani daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Nura Sani, ya nuna jin dadinsa.
“Wannan tallafi zai taimaka mana sosai a wannan mawuyacin lokaci. Muna godiya ga gwamnati bisa ƙoƙarinta,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya ƙaryata zargin da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya yi masa, dangane da mutuwar wasu marasa lafiya sakamakon katse wutar lantarki da aka ce kamfanin ya yi.
Asibitin na AKTH ya bayyana damuwarsa a ranar Lahadi kan abin da ya kira abin takaici yana mai cewa mutanen da suka mutu za su iya tsira da ransu da ba a ɗauke wutar ba.
Amma a martanin da ya bayar, Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, ya ce asibitin na ƙoƙarin ɓata sunan kamfanin ne kawai, domin an dawo da wutar tun kafin asibitin ya fitar da wannan sanarwar.
Sani ya bayyana cewa matsalar ta samo asali ne daga wani yunƙurin da ake yi na raba ginin asibitin da cibiyoyin lafiya daga gidajen ma’aikatan asibitin.
“Cibiyar asibitin da cibiyoyin lafiya suna da alaƙa da layin 33kV na Zariya Road wanda aka fi ba fifiko wajen raba wuta, kuma suna samun kimanin sa’o’i 22 na wutar lantarki a kullum ƙarƙashin tsarin Band A.
“Amma, shugabannin AKTH sun dage cewa sai gidajen ma’aikata sun ci gaba da kasancewa a layin wutar lantarki ɗaya da cibiyoyin lafiya. Wannan ya janyo barazana ga inganci da kwanciyar hankali na wutar da aka ware wa asibitin.
“An yi ƙoƙari sau da dama don raba gidajen ma’aikata daga cibiyoyin lafiya, amma haƙarmu ba ta kai ga cimma ruwa ba saboda ƙin amincewar shugabannin asibitin. Abin takaici, wannan ya haifar da matsala mai tsanani da ta janyo katsewar wutar da muke ƙoƙarin kaucewa,” in ji KEDCO.
Don tabbatar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba ga asibitin, kamfanin KEDCO ya ce yana ci gaba da aikin raba layukan wutar lantarkin biyu. Ya ce annan mataki ya zama dole don tabbatar da inganci, tsaro da kyautata lantarki ga asibitin.
Kamfanin ya kuma zargi asibitin da rashin biyan kuɗin wutar lantarki da gidajen ma’aikata ke amfani da ita, wanda ke shafar ingancin ayyukan samar da wuta na kamfanin.
KEDCO ya ce a cikin wata wasiƙa da ya aike ranar 12 ga Agusta, 2025, Babban Jami’in Kasuwanci na kamfanin, Muhammad Aminu Ɗantata, ya sanar da Shugaban Asibitin AKTH game da shirin dakatar da samar da wutar lantarki ga gidajen ma’aikata da wuraren da ba su da muhimmanci, sakamakon rashin cikakken biyan kuɗin wutar wata-wata.
Wasiƙar ta bayyana cewa:
“Duk da roƙon da aka yi sau da dama, asibitin ya ƙi biyan cikakken kuɗin wutar da yake sha a duk wata.
Wannan ya haifar da bashin wutar lantarki da ya kai ₦949,880,922.45 a watan Agustan 2025.
“An bukaci asibitin ya biya kuɗin watan Agusta 2025 na ₦108,957,582.29 gaba ɗaya cikin kwanakin aiki 10, don kaucewa yanke wuta a wuraren da abin ya shafa,” in ji wasiƙar.
Kamfanin ya ƙuduri aniyar ci gaba da samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba ga AKTH a matsayin babbar cibiyar lafiya.
A ƙarshe, KEDCO ya roƙi shugabannin asibitin da su ba da haɗin kai a aikin raba layukan wutar, wanda ya ce yana da amfani ga marasa lafiya, ma’aikata, da al’umma baki ɗaya.