HausaTv:
2025-11-02@17:01:43 GMT

Iran ta aike da kayayyakin jin kai tan 100 zuwa Afghanistan

Published: 6th, September 2025 GMT

Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Iran ta ce kasar ta aike da kayayyakin jin kai zuwa yankunan da girgizar kasa ta shafa a gabashin Afghanistan.

Razieh Alishavandi, jami’i daga kungiyar, ya bayyana cewa, Iran ta tura sama da tan dari na kayayyakin ceton rai zuwa Afghanistan.

A cewar Alishavandi, wannan agajin ya hada da abinci, tantuna, barguna, tufafi, da dai sauran abubuwa masu muhimmanci na matsugunin gaggawa da tallafi ga mutanen da girgizar kasar ta shafa a Afghanistan.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran “Koyaushe kamar yadda ta saba, za ta tsaya da dukkan karfinta ga mutanen Afghanistan a cikin wnnan lamarin,” in ji shi .

A ranar Lahadin da ta gabata, ce girgizar kasa mai karfin maki 6.0 ta afku a kasar Afganistan, daya daga cikin girgizar kasar mafi muni a ‘yan shekarun nan.

Girgizar kasa ta biyu mai karfin awo 5.5 a ranar Talata ta katse ayyukan ceto tare da haifar da zabtarewar kasa, tare da katse hanyoyin shiga kauyuka da dama tare da sanya isar da kayan agaji cikin wahala.

Gwamnatin Taliban ta tabbatar da mutuwar mutane 2,205, yayin da a kalla 3,640 suka samu raunuka, ko da yake Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa adadin na iya karuwa yayin da mutane da dama suka makale a karkashin baraguzan gine-gine.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ammar Hakeem ya gana da larijani a nan birnin Tehran . September 6, 2025  HKI Ta Kashe Falasdinawa 50 A Harin  Da Takai A Yankin Gaza September 6, 2025 An yi Kira Ga El-rufai Da Ya yi Hattara Da Kalamansa September 6, 2025 An Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Shirin Amurka Na Kwace makaman Hizbullah. September 6, 2025 Manyan Jami’an Kungiyar Hamas sun Gana Da Minister Harkokin Wajen Iran September 6, 2025 Afirka za ta iya samun tagomashi wajen habaka tattalin arzikin dijital – IFC September 6, 2025 Araqchi: Kasashen Turai Suna Nuna Son Kai A Kan Batun Hana Kera Makamin Nukiliya September 6, 2025 Kasar Iran Ta Bayyana Lokacin Sabon Zagaye Na Tattaunawa Tsakaninta Da Hukumar IAEA September 6, 2025 Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinu: Barazanar Katz Kira Ne Zuwa Ga Kisan Kare Dangi September 6, 2025 Asusun “UNICEF” Ta Jaddada Takaicinta Kan Hana Yaran Falasdinawa Samun Ilimi September 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka

Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da cewa, Iran ta gudanar da yakin kwanaki goma sha biyu da wannan gwamnati mai wuce gona da iri, kuma ta hana ta ci gaba da mummunar manufarta ta mamaya a yankin.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na  Al- Jazeera, Araqchi ya yi nuni da cewa: Gwamnatin masu wuce gona da iri ta yi kokarin fadada yakin zuwa yankin ta hanyar kai hari kan cibiyoyin man fetur na Iran, amma Iran ta yi nasarar shawo kan yakin kuma ta hana aukuwan hakan.”

Yayin da yake fayyace shirye-shiryen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tattaunawa don kawar da damuwar da ake da ita game da shirin makamashin nukiliyarta na zaman lafiya, Ministan Harkokin Wajen ya jaddada cewa: “Sun shirya wa duk wani abu da zai faru kuma suna tsammanin duk wani hali mai tsauri daga ‘yan sahayoniyya.” Ya bayyana cewa Iran ta samu kwarewa mai yawa daga yakin da ta yi kwanan nan kuma ta samu damar gwada makamai masu linzaminta a wannan yaƙi na gaske.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta