2025-12-13@21:15:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 786

«jiragen yaki marasa»:

    A gaban al’ummar kasarta, tawagar Morocco na da burin samun makoma irin ta Ibory Coast, wato nasara a gida amma ba tare da fargabar da ta fuskanta a zagayen farko ba. Amma karbar bakuncin gasar ba lallai ba ne ya zame riba ba. A cikin karo 34 da aka gudanar da gasar tun daga shekarar 1957 (ciki har da gasar farko), sau 12 ne kacal kasar da ta karbi bakuncin gasar ta yi nasara, wato kusan kashi 35% cikin dari. Tun daga 2000, Tunisia (2004), da Masar (2006) da Ibory Coast (2024) ne kawai suka yi nasara a gida. Kasar da ta fi fice a Afirka na da burin lashe kambu na takwas don kawar da bakin cikin kashin da...
    “An zabo Abubakar Dantsoho ne, daga cikin sauran wadanda aka karamma da lambar yabon bisa kokarin da yake ci gaba da yi, na bunkasa fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasar wanda hakan ya sanya, aka kara samun fitar da kaya daga kasar nan, ta hanyar Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa dIMODantsohoa tsarin NSW ta hanyar yin amfani da dabarar PCS domin janyo ra’ayin masu zuba jari daga ketare a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar nan, da aka samar da kayan aiki na zamani, ” Inji sanarwar. “Akawi kuma batun kara daga darajar Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar a tsakanin hukumomin Jiragen Ruwa da ke a Afirka ta Yamma wato PMAWCA da kuma zabar Dantsoho, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar masu...
    “Dawo Nijeriya a cikin rukunin na C a kungiyar ta IMO hakan ya nuna irin zagewar kasar nan na iya tafiyar da tsare-tsare da bin ka’idojin gudanar da sufurin Jiragen Ruwa da wanzar da tsaro da kuma samar da kyakyawan yanayi, ga fannin,” Inji Dantsoho. “Wannan ci gaban, ba wai ga kasar nan ne kadai ba, har da ma ci gaban daukacin Afirka ta Yamma musamman a bangaren kara bunkasa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a nahiyar da samar da hanyoyin kara habaka safarar kaya zuwa ketare da kuma kara bunkasa fannin tattalin arziki na teku'” A cewar shugaban. “Nijeriya a yau, ta kai wani babban mataki da duniya ke sauraronta a saboda haka, ina kara taya Nijeriya da...
    Allah Ya yi wa Farfesa Adamu Baikie, wanda ya kasance Farfesa na farko a fannin Ilimi daga Arewacin Najeriya, rasuwa. Farfesa Adamu Bakie ya rasu yana da shekaru 94 ne a daren Jumma’a a gidansa da ke Zariya, Jihar Kaduna. Babban ɗansa, Manjo Muhammad Adamu (Ritaya), ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a sanar da jama’a cikakkun bayanai da lokacin da za a gudanar da jana’izarsa daga baya. Baikie ya shahara sosai wajen gina fannin ilimi a Najeriya, inda ya yi aiki a manyan makarantu da dama. Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta Ya taɓa zama Shugaban Jami’a a wasu jami’o’in Najeriya, kuma...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 2.6 domin gudanar da ayyukan Hajjin shekarar 2026. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da naira biliyan 2 da miliyan 651 domin ayyukan Hajjin 2026, biyo bayan gabatar da bukatar da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) ya yi. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce za a yi amfani da kudaden ne a bangarorin sufuri da jijigilaAlhazai, jin dadinsu, ayyukan lafiya da kuma shirye-shiryen gudanarwa. Sauran bangarorin...
    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan. Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma. NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin. Ta ce wannan lamari...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pazeshkian, a ganawarsa da tokwaransa na kasar Turkmenietan Gurbanguly Berdimuhammedow a birnin Ashg’abat ya ce, a halin yanzu, fiye da duk wani lokaci – tana bukatar amintaccen madogara, zaman lafiya da kuma hadin kai. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana yabawa kasar Turkmenistan kan shirinta karban bakwancin taro dangane da hadin kai da kuma amintaccen madogara da kuma zaman lafiya nan gama a birnin Ashg’abad . A zantawar shuwagabannin kasashen biyu sun bukaci karfafa diblomasiyya tsakanin kasashen biyu, da tattaunawa tsakanin kasashen yankin a kan duk wani al-amari da ya taso a tsakaninsu. Shugaban Pezeshkian ya ce, wannan shi ne abinda duniya ta rasa kuma take bukata a yau. Dole ne...
      A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000.   Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar Oko (Hausa), Midwifery Market da Ogbogonogo Market, sai dai a kasuwannin mako-mako na kauyuka. Bincike a babban birnin jihar ya nuna cewa farashin muhimman kayan abinci ya dan daidaita, amma ‘yan kasuwa da masu sayayya sun nuna damuwa kan karancin kudin da ake da shi don sayayya. Kwandon tumatir da ake sayarwa Naira 5,000 a wasu watanni da suka gabata, yanzu ya sakko Naira 4,000....
    Daga Usman Muhammad Zaria  Hukumar bunkasa ilimin manya ta jihar Jigawa tace za ta kashe naira milyan 400 wajen gudanar da harkokin ta a sabuwar shekara ta 2026. Shugaban hukumar. Dr. Abbas Abubakar Abbas, ya bayyana haka lokacin kare kiyasin kasafin kudin hukumar a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa. Dr Abbas Abubakar Abbas ya ce hukumar za ta yi amfani da kudaden wajen inganta shirye shiryen koyon karatu da rubutu ga manya maza da mata da na ci gaba da karatu don kammala karatun sakandare da na masu son sake jarrabawar sakandire da koyon karatu ta Rediyo da cibiyoyi daban daban da ke fadin jihar. Shi ma da ya ke kare kiyasin kasafin kudin hukumarsa...
    Suleiman-Jibia ya ƙara sanar da cewa, majalisar ta amince da kafa Cibiyoyin Horar da Malamai a Katsina, Daura, da Funtua.   “Cibiyoyin za su taimaka wajen haɓaka tsarin koyarwar malaman domin samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai a faɗin jihar,” in ji shi ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja December 11, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ne Ya Sanya Ni Komawa Jam’iyyar Accord – Adeleke December 11, 2025 Manyan Labarai Za Mu Yi Hisabi Da Buhari A Gaban Allah — Sheikh El-Zakzaky December 11, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Nijeriya Ta Himmatu Wajen Inganta Tsarin Karatun Allo December 11, 2025 Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja December 11, 2025 Labarai Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 11, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato December 11, 2025
    Daga Aliyu Lawal  Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, wadda ya rabawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja. Alhaji Iliyasu Zakari, wanda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne ginshikin mulkinsa, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, hukumomin tsaro da Gwamna Mohammed Umar Bago bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da sakin dalibai ɗari da aka...
    Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta. Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania. Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba. A...
    Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan daliban sun gama jarabawar ƙarshe. Sai dai ba a bayyana sunan dalibin ba. DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka Majiyar ta ce motar ta yi ƙoƙarin wuce wata mota kafin ta kwace ta kuma...
    A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya. Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi. Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki. Yara ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukansu a manyan dandanli 10 ciki har da TikTok da Snapchat. Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar. Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.
    Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin. Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda iyaye ke bada hadin kai da goyan baya ga shirin. Ya kuma ja hankalin ma’aikatan rigakafin da su sanya kishi da kwazo wajen samun nasarar aikin. A sakon da ya aike da shi a taron tattara bayanan aikin rigakafi na yankin, Shugaban Karamar Hukumar, Mallam Badamasi Garba Dabi ya jaddada kudirin Karamar Hukumar na ci gaba da bada gudunmuwa wajen samun nasarar shirin rigakafin.  ...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja Lamarin ya faru ne a wani gida mai faɗin kafa 25 da 20 wanda ya kama da wuta. Ma’aikatan kashe gobara sun ceto wata yarinya mai shekara 10 daga a cikin gidan, amma daga baya ta rasu a asibiti. An bai wa iyayenta gawarta. Hatsari na biyu ya faru ne a Ƙauyen Badume Kanawa da...
    Kungiyar ‘yan wasan  ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda ya sami halartar ‘yan wasa 452 daga kasashe 75. A ranar ta karshe ta wasan, dan wasan Iran Muhammad Aizadeh, ya sami azurfa, sai kuma wani dan wasan “Matin Rizayi wanda ya sami tagulla. Wadanda su ka sami zinariya kuwa su ne Abul Fadl Zandi, da Radin Zinalu sai kuma Amir Riza Gulami.  Kasar Turkiya ta zo ta biyu da ta sami zinariya biyu da...
    Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa  dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN). Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar. Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan...
    Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi. Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai. Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta  bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare guda ta kasa da kasa wacce ba’a dade da samar da ita a farkon wannan shekarar. Isma’el Baghaei ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Alhamis, inda yayi tir da Amurka wace ta fara fara dorawa JMI takunkuman tattalin arziki tun fiye da shekaru fiye da 40 da suka gabata. Kuma hakan take hakkin bil’adama. Yace a farkon wannan shekarar ne dai...
    Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gwamna Abba, ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF, domin ganin yadda suke shirin kare al’umma daga hare-haren ’yan bindiga a yankunan Tsanyawa da Shanono. Ya roƙi al’ummar yankunan da abin ya shafa da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani game da duk...
    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC). Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin. Sanarwar...
    Wata fitacciyar sinima a Faransa, Cinematheque Francaise, ta rufe ɗakunan kallonta na tsawon wata guda saboda yaɗuwar kuɗin cizo da aka gano a cikinta Cibiyar wadda ke gabashin birnin Paris ta ce rufe sinimar zai ba ta damar tabbatar da cewa masu kallo sun samu “aminci da kwanciyar hankali” bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi na cewa ƙwarin suna cizon mutane a lokacin kallon fina-finai. Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32 Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku A farkon watan Nuwamba, wasu daga cikin masu kallo sun shaida wa kafafen yada labarai cewa ƙwarin sun cije su bayan wani taro da aka yi da shahararriyar ’yar fim ɗin Hollywood, Sigourney Weaver. Wani daga cikinsu ya...
    Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila. Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon. A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghai ya jadda game da hakkin kasashe a yammacin asiya na kare martabar su da yankunansu game da wuce gona da irin Isra’ila. Har ila yau yayi suka game da kasa tabuka komai da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan hare haren da isra’ila ke kai wa kan wasu kasashe kamar labanon da siriya wanda...
    Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun sanarwa da hukumar kwallon kafa ta duniya fifa cewa wannan matakin ba shi da wata alaka da wasanni , kuma wakilan kasar iran din ba za su halarci gasar kofin duniya ba . Wannan yazo ne bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa Amurka ta hana wasu daga cikin jami’anta visa shiga Amurka ciki har da shugaban hukumar Mahdi Taj, Ana...
    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci. Hukumar ta bayyana cewa...
    Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe. An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti na 32 da fara buga wasan a filin wasa na Khalifa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi A hanyarta ta kaiwa  wasan ƙarshen, Portugal ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Austria ta fitar da Italiya bayan lallasa ta da ci 2-0....
    Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
    Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne da babu sulhu a kansu, don haka duk wata tattaunawa da Amurka dole ne ta zama cikin yanci da daidaito, za’a iya tattaunawa amma ta gudana ba tare da nuna fifiko ba. Amurka tana kokarin nuna kanta a matsayin wadda za ta kawo sauyi a kowanne lamari na duniya, amma wannan wani nau’i ne na yaudarar kai, don haka mun yarda da tattaunawa ta gaskiya...
    Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan Boko Haram sun file kan mata 2 a Borno Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78. Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18,...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno A ranar Alhamis ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifukan ta’addanci. Sai dai Obi ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kuskure tun daga farko wajen tafiyar da lamarin, kuma bai kamata ya kai wannan mataki ba. Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da dama ciki har da...
    Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
    Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin  ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce  Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin.   BBC
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar. Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu. Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025 Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025 Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025
    Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu. Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata. Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin...
    Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi. A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba...
    Gwamnatin Beirut ta ce za ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban Majalisar Dinikin Duniya game da gida katangar siminti a kan iyakar Kudancin Lebanon. A cikin wata sanarwa data fitar fadar shugaban Lebanon ta sanar da cewa Beirut za ta shigar da kara a Majalisar Dinkin Duniya game da gina katangar. Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umarci Ministan Harkokin Wajen kasar Youssef Radji da ya umurci tawagar Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ta shigar da karar gaggawa a kwamitin Tsaro kan gwamnatin Isra’ila saboda gina katangar siminti a kan iyakar kudancin Lebanon, wadda ta wuce ‘’Layi Shuɗi’’ da aka zana bayan janyewar Isra’ila a shekarar 2000. Hukumomin Lebanon sun ce katangar simintin da sojojin Isra’ila...
    Rahotanni sun bayyana cewa jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeid Iravani yayi gargadin cewa Tehran ba za ta taba mika wuya ga matsalin lmbar soji ba, ko ta siyasa ko kuma takunkumin tattalin Arziki, kuma ta yi tir da Amurka da Isra’ila game da harin da ta kai kan tashoshin nukiliyarta da ya sabama doka, da kuma yin fuska biyu a matakenta na kasa da kasa Wannan bayani na Iravani yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman tankiya ke kara Kamari bayan hari da Amurka da isra’ila suka kai  a watan yuni shekara ta 2025 da muke ciki, wanda iran tace wurare ne dake karkashin kulawar hukumar nukiliya ta Duniya IAEA. Kamalan nasa sun nuna cewa bisa mahangar...
    An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025 Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025
    El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.” Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin...
    Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya. A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani. Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a...
    Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...
    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
    Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.   Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, Suleja, Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule...
    Wani kamfanin hakar ma’adinai na Biritaniya ya sanar a jiya Laraba cewa, an gano tarin zinari a karkashin kasa a gundumar Kakamega da ke yammacin kasar Kenya, wanda darajarsa ta kai sama da dalar Amurka biliyan 5.28 kwatankwacin shilin kasar Kenya biliyan 683, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi ga fannin hakar ma’adinai na kasar. Kamfanin ShantaGold Kenya Limited ya sanar da cewa, an gano hakan ne a hanyar Lerehanda, wanda ya ratsa cikin kananan hukumomin Kakamega da Fihiga, bayan kwashe tsawon shekaru ana bincike. A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce aikin yana da nufin samun lasisin da ya dace don hakar albarkatun zinare a mahakar Isolo-Bushiangala don...
    Babban abin lura a nan shi ne irin alfanun da Nijeriya za ta samu tare da sauran kasashen Afrika daga wannan bikin baje koli. Na farko dai Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su kara kaimi wajen noman irin waɗannan amfanin gona domin fitar da su zuwa Sin, hakan kuwa zai kara samar da aikin yi ga dubban ‘yan Nijeriya, abin da zai habaka kudaden shiga ga kasa. Alfanu na biyu kuma shi ne fadada damar ingantawa da kara daga darajar irin wadannan amfanin gona da Nijeriya ke samarwa. Sannan kuma akwai batun bunkasa dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka. Sabo da haka wannan irin lamari na bude kofar cudanya tsakanin Sin da sauran kasashen...
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
     A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An sami tsaiko a yadda kungiyar take tafiyar da ayyukan nata, saboda bullar Korona, amma ta ci gaba da aiki a karkashin wani tsari na musamman  ( IranDoc.). Aikin wannan cibiyar shi ne tsara gudanar da nazarori da bincike na ilimomi mabanbanta da kuma hana yin maimaici akansa. A halin yanzu da akwai mutane 20 da suke aiki a karkashin wannan kungiyar daga asalin su 20...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja November 7, 2025 Siyasa Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha November 4, 2025 Labarai “Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump November 3, 2025
    Pars Today – Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, yana Allah wadai da fashewar da ta faru a babban birnin Pakistan, ya ce ta’addanci barazana ce ga dukkan yankin kuma fuskantar wannan mummunan lamari yana buƙatar haɗin gwiwa, ƙuduri, da haɗin kai daga dukkan ƙasashe. Reza Amiri-Moqaddam, Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Pakistan, a ranar Talata, yayin da yake Allah wadai da fashewar ta’addanci a birnin Islamabad – wanda ya kashe mutane 12 tare da raunata aƙalla wasu 30 – ya ce: “Ta’addanci makirci ne na matsorata waɗanda ke neman wargaza yankinmu da kuma sanya cikas a hanyarsa ta zuwa ga ci gaba mai ɗorewa.” A cewar jaridar Pars Today, jakadan Iran a Pakistan ya jaddada cewa: “Wannan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da adalci da yadda ake rarraba jami’an tsaro a ƙasar. A halin da ake ciki, yawancin unguwanni da kauyuka na fama da ƙarancin jami’an ‘yan sanda, yayin da mutum guda ko wasu ‘yan kaɗan ke da ɗaruruwan masu tsaro a gefensu. Ko yaya tasirin tura ‘yan sanda tsaron wasu daidaikun mutane maimakon tsaron alummar kasa gaba daya? NAJERIYA A YAU: Dalilan Malaman Jami’oi Masu Zaman Kansu Na Shiga Ƙungiyar ASUU DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga...
      Bugu da kari, abu mafi muhimmanci shi ne, kasar Sin ta ba da jagoranci ga kasashen duniya ta fuskar kara bude kofa ga waje. Ta hanyar shigowa da kayayyaki da fitar da kayayyaki, kasar Sin ta ba da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya, da kara yawan kayayyakin da kasashen duniya suke fitarwa, tare da ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kyautata harkokin masana’antu. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta ba da taimako wajen shigar da mambobin WTO su 130 cikin yarjejeniyar samar da sauki a ayyukan zuba jari domin neman ci gaba, ta yadda kowa zai cimma moriyar sakamakon dunkulewar duniya cikin adalci. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Ya...
    Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
    ‘Yan Iraki sun kada kuri’a don zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki wadda za ta fayyace alkiblar siyasar kasar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Kimanin ‘yan kasar miliyan 21 ne aka tantance domin kada kuri’a ga ‘yan majalisar dokoki 329, Wadannan za su zabi shugaban kasa kuma su amince da sabuwar gwamnatin, wadda sabon firaminista zai kafa. A cewar jami’an zabe, za a sanar da sakamakon cikin sa’o’i 24 bayan kammala zaben. Firaminista Mohammed Shia al-Soudani ya bayyana zaben a matsayin wanda ya gudana “a cikin yanayi mai aminci da kwanciyar hankali,” yana yabon jami’an tsaro saboda kiyaye tsarin. Al-Soudani, wanda aka zaba a shekarar 2022, yana neman wa’adi na biyu kuma zai bukaci samun rinjaye a majalisar. A Iraki,...
    Allah Ya yi wa Hajiya Ɗayyabatu, mahaifiyar Ministan Muhalli, Balarabe Lawal Abas, rasuwa tana da shekara 93. Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da jinya, a gidanta da ke unguwar Bambale da ke birnin Zariya. Ta rasu ta bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Lakurawa sun kashe jami’in kwastam a Kebbi NAJERIYA A YAU: Dalilan Yaɗuwar Cututtuka A Irin Wannan Lokaci Ana sa ran gudanar da Sallar jana’izarta a safiyar Litinin daina nan da misalin ƙarfe 11, a gidan nata da ke Bambale, Birnin Zariya.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da zarar damuna ta fara bankawana, yanayi na sanyi da zafi kan fara sallama, wanda hakan kan zo da rashin lafiya dake yaduwa a cikin alumma.   Ko wadanne dalilai ne suka sa ake samun yaduwar rashin lafiya a wannan lokaci? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar. Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani. Ranar Foliyo Ta...
    Hare-haren daukan fansa da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar janyo hasarar dala miliyan 200 Harin da aka kai wa matatun mai na Haifa na ɗaya daga cikin ayyukan da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin da Isra’ila ta kai a lokacin yaƙin kwanaki 12. Shirin “Lambar” a cikin ɓangarensa na “Sa ido”, ya magance wannan aikin. Waɗannan matatun mai suna daga cikin muhimman wurare na dabaru a Isra’ila, waɗanda ke cikin ɗaya daga cikin muhimman tashoshin jiragen ruwa kuma suna aiki a matsayin babbar cibiyar jiragen ruwa da ke jigilar mai zuwa ƙasar. A cewar ƙididdiga da ƙayyadaddun fasaha, matatun mai na Haifa suna da ƙarfin samar da tan miliyan 9.8 a...
    Ya ƙara da cewax gwamnatinsa ta fara gyara daga tushe, inda ilimi ya zama ginshiƙin farko. “Shekaru takwas kafin mu hau mulki, ɗalibanmu ba su samun takardun WAEC, sannan tsawon shekaru biyu suna fama da matsalar NECO. Na biya Naira Biliyan huɗu don magance wannan matsala,” inji shi.   Gwamnan ya bayyana irin matsalolin da ya gada, yana mai cewa: “Na samu asusun gwamnati da naira miliyan huɗu kacal. Ma’aikata suna karɓar albashi cikin rashin tabbas, babu ruwa, asibitoci kuwa suna cikin mummunan yanayi.”   Lawal ya ce, ya sake fasalin tsarin gwamnati, inda ya rage yawan kwamishinoni da manyan sakatarorin don rage ɓarna da ƙara inganci. “Yanzu muna daga cikin jihohi mafi ci gaba wajen tara haraji, inda kuɗaɗen...
    Wani yaro ɗan shekara biyu mai suna Danjuma Salman, ya rasu bayan ya faɗa cikin rijiya a Jihar Kano. Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Gwale. Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Rahotanni sun nuna cewa yaron ya zame ne sannan ya faɗa cikin rijiyar wadda murfinta ya lalace. Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:05 na safe daga wani mai suna Saminu Dayyabu, wanda ya sanar da su cewa wani yaro ya faɗa cikin rijiyar. “A lokacin da jami’anmu suka isa wajen, sun tarar...
    Cin zarafin da Babban Jami’an tsaro (CSO) na Gwamnan Yobe,  CSP Yakubu Zakari Deba ya yi ga wakilin Talabijin NTA da ke Damaturu, Babagana Kolo a harabar Majalisar Dokokin Yobe da ke Damaturu a ranar Alhamis ya tada ƙura. Lamarin ya faru ne yayin da wasu ’yan jarida ke jiran a shigar da su cikin zauren domin su bayar da rahoto kan gabatar da kasafin kuɗin 2026 da Gwamna Mai Mala Buni ya yi a gaban Majalisar Dokokin. An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC Shaidu sun ce Babban Jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba, ya afka wa Kolo ya buge shi...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya yaba da juriyar da kasar ta nuna yayin hare-haren Amurka da Isra’ila, wanda ya tilasta musu rokon a tsagaita wuta ba tare da shiri ba. Da yake jawabi a yammacin ranar Laraba a taron Majalisar Gudanarwa ta Lardin Hamadan, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa abokan gaba sun gaza a dukkan manufofinsu a lokacin yakin na kwanaki 12.   Kalaffafen yakin na kwanaki 12 ya bamu babban darasi inji shi, saboda mun fi karfi da a ranar 13 ga watan Yuni. A karon farko, an yi amfani da makamai masu linzami na Iran a wani rikici na gaske, wanda hakan ya ba da damar gano ƙarfi da rauninsu. A yau, Iran tana...
      “Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.   Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.   A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.   An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan...
    Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.   Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A...
    Ya lura cewa kasashe kamar China, Japan, da Indiya sun cimma gagarumin ci gaba a fannin kimiyya da fasaha ta hanyar amfani da harsunan asali don koyarwa a matakin ilimi na farko.   A cewarsa, koyarwa a cikin harshen Hausa zai inganta fahimta tsakanin dalibai, rage yawan faduwa, da kuma rage yawan wadanda ake kora daga makaranta sakamakon faduwa a jarrabawa.   Bayan tattaunawa, shugaban majalisar Jibrin Ismail Falgore, ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar mai kula da harkokin ilimi domin ci gaba da bincike da neman shawarwari. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana...
    Iran ta sanar da yi wa ‘yan faransa nan guda biyu da take tsare saki bisa sharadi a zarginsu da akeyia da yi wa tsaron kasar Iran zagon kasa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya fitar da bayanin sakin yana mai cewa na yi shi ne  “bisa umarnin alkali.” Ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar shari’a har sai an ci gaba da shari’a. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana mutanen biyu a matsayin Cécile Kohler da Jacques Paris, wadanda aka tsare a Iran bisa zargin leken asiri. A halin yanzu suna Ofishin Jakadancin Faransa da ke Tehran. A ranar 21 ga Oktoba, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na gyaran tattalin arziƙi da kuma dawo da amincewa ga tsarin kwangilolin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025 Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86 November 5, 2025 Manyan Labarai Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025
    Pars Today – Wakilin Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kalaman shugaban Amurka game da gwajin makaman nukiliya a matsayin abin tsoro. A cewar Pars Today, Amir Saeed Iravani, jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, ya rubuta a ranar Talata ga Shugaban Majalisar Tsaro da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a matsayin martani ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da barazanar nukiliya, yana mai kiran su “abin damuwa ne kwarai da gaske.” Iravani ya yi gargadin cewa irin wadannan kalamai suna wakiltar babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya kuma suna nuna keta hakkokin Amurka a karkashin dokokin kasa da kasa. Shugaban Amurka ya sanar a ranar 29 ga Oktoba cewa...
    Carlos Alcaraz da Jannik Sinner za su buga wasan baje koli a Koriya ta Kudu a watan Janairu, kwanaki takwas kacal kafin fara gasar Australian Open. ’Yan wasan biyu kuma za su hadu a babban wasan Hyundai Card Super Match a Incheon, a ranar 10 ga Janairu, yayin da za a fara babbar gasar Australian Open a Melbourne a ranar 18 ga Janairu. Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano Kafin hakan dai ’yan wasan biyu, wadanda suka hadu a wasanni uku daga cikin hudu na Grand Slam a shekarar 2025, sun lashe kofuna tara cikin manyan gasa 10 da suka...
    A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36.   Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024.   BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon...
    Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara.   Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka.   Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don...
    Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya. Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa. “Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
    Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025
    Rundunar Sojojin Nijeriya (AFN) za ta gudanar da bikin kammala aiki na tsohon Shugaban Tsaron Ƙasa (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a ranar Jumma’a, 31 ga Oktoba, 2025, domin girmama ayyukan da ya gudanar a lokacin hidimarsa. A cewar sanarwar da shalƙwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta fitar a ranar Alhamis, an shirya bikin Pulling Out Parade ɗin ne da ƙarfe 09:00 na safe, inda manyan hafsoshin Soja, da jami’an gwamnati da ƴan uwa za su halarta. Wannan biki na nuni da kammala aikin Soja a matakin ƙoli, kuma yana ɗaya daga cikin manyan al’adun da ake yi wa manyan jami’an da suka yi aiki da ƙwarewa da sadaukarwa. Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa. Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar  suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i. Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran...
    Za a gudanar da kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC karo na 32 a Koriya ta Kudu. Eduardo Pedrosa, babban daraktan sakatariyar APEC, ya bayyana cewa tun bayan shigarta APEC, Sin ta kasance mamba mai himma da kwazo. Kuma a halin yanzu, tana taka muhimmiyar rawa wajen ba da jagoranci a karkashin tsarin APEC, haka kuma tana mai da hankali kan yadda za a inganta samar da manyan ci gaba a yankin da kuma duniya baki daya. Eduardo Pedrosa ya bayyana haka ne kwanan nan yayin wata hira da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG a birnin Gyeongju dake Koriya ta Kudu. Ya kuma yaba da nasarorin da Sin ta samu a tafarkinta na zamanantar da kanta.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU...
    Bugu da kari, shaidu na zahiri sun tabbatar da cewa alakar ci gaban kirkire-kirkiren fasahohin Sin da sauran sassan duniya, ya kunshi kafa tushe na samar da karin daidaito a fannoni da dama, ciki har da hada-hadar cinikayya ta dijital, da ilimi da jagoranci.   Ta hanyar rage gibin dake akwai tsakanin mabanbantan sassan duniya, sashen kirkire-kirkiren fasahohin Sin na kara fadada damar raya masana’antun duniya, da samar da guraben ayyukan yi, musamman a yankunan duniya da aka jima da yin watsi da su, wanda hakan zai yi matukar amfanar da tsarin kasuwancin duniya.   A fannin raya fasahohin cin gajiyar makamashi marar dumama yanayi ma kasar Sin na kara taka rawar gani, inda alal misali Sin ke bayar da...
    Wata babbar kotun Jihar Ekiti da ke zamanta a Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataye wani mai suna Stephen Adamu mai shekara 34 bisa laifin kashe ɗan uwansa. An gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban mai shari’a Adekunle Adeleye a ranar 31 ga watan Junairu, 2025, kan tuhumar kashe wani David Adamu, a sashi na 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti 2021. Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Domin tabbatar da ƙarar sa, mai gabatar da ƙara Funmi Bello, ya kira shaidu shida da waɗanda ake ƙara da su gabatar da jawabi, da fom ɗin shaida da kuma wuƙa a matsayin nunin...
      Dr. Alausa ya ce, za a fitar da kudaden ne ta Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF), wanda hakan ke nuna kudirin Shugaba Bola Tinubu na biyan basussukan da ya gada domin karfafa kwarin gwiwar ma’aikata a manyan makarantu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro October 29, 2025 Labarai Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya October 29, 2025 Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025
    Asalin tsarin shari’ar da ake amfani da shi game da kare muradun al’umma ya bai wa masu gabatar da kara damar yin aiki na neman hukunta masu laifi a madadin sauran al’umma a shari’o’in da suka shafi laifukan gurbata muhalli, da rashin kiyaye tsaftar abinci, da kuma rashin da’a ga gwamnati wadanda dukkansu idan aka bar su kara-zube, za su tauye hakkokin galibin jama’a. Amma a halin yanzu, sabon daftarin dokar da ake son kafawa ya fayyace nau’ikan dokoki 16, ciki har da karin wasu muhimman abubuwa guda biyu da suka shafi al’adun gargajiya da kuma tsaron kasa, wanda ke nuna kara fadada tsarin dokar.   Domin ganin ba a tauye hakkin kowane bangare tsakanin mahukunta da mabiya ba, a...
      Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin. Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin. An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Waɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
      “Bayan gano alamun karkatar da kudaden tallafin a matakin farko, mun gabatar da matakai don tabbatar da cewa kudin ya isa ga wadanda aka yi niyya,” in ji shi.   Wasu daga cikin matakan da aka dauka sun hada da kafa kwamitin mambobi 20 a kowace karamar hukuma, wanda ya kunshi sarakunan gargajiya, shugaban karamar hukuma, shugaban jam’iyya, da sauran mambobi.   Ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kudaden ta hanyar kafa kananan kasuwancin kashin kansu domin inganta yanayin samun kudinsu da zamantakewarsu domin habaka tattalin arzikinsu da kuma na iyalansu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28,...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar.   Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta. Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata. Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga...
    Mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kwamitin shugaban ƙasa kan ba da tallafi ya ƙaddamar da rabon naira miliyan 50, inda mutum miliyan 1 za su samu naira dubu hamsin kowanensu tare da wasu shirye-shirye na bunƙasa ƙananan sana’o’i.  Ya ƙara da cewa ƙanana da matsaƙaitan sana’o’i a Jihar Katsina za su samu 250,000 daga gwamnatin tarayya wanda zai taimaka wa sana’o’insu wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya  Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya wajen ƙirƙirar ayyuka, wanda yanzu haka an samar da kuɗaɗai har naira biliyan 5.5, inda aka raba biliyan ɗaya ga mutane 701 a faɗin jihar.  Gwamna Raɗɗa...
    Dasuki, wanda shine shugaban rikon kwarya na Shirin Makomar Matasa A Yanzu, wani shiri na hada matasa da harkokin siyasa da aka kaddamar a ranar 1 ga Oktoba, 2025 a Abuja, ya bayyana cewa sanarwar shirin na cewar kashi 70% na kujerun majalisar wakilai a zaben 2027 su kasance na ‘yan Nijeriya kasa da shekaru 40, ba kawai magana ce ta fafutuka ba, har ila yau kalubale ne ga shugabanni.   Matakin Dasuki ya kasance wani muhimmin lamari a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ’yan siyasa kalilan ke ja da baya daga mukaman su. Sanarwar sa an fassara ta sosai a matsayin wakilcin  gwagwarmayar adalci tsakanin tsararraki wanda ya taimaka wajen jagoranta, wanda ke nufin rage gibin da ke tsakanin tsofaffi...
    Ya ƙara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta  jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba. A cewarsa, “ABU tana ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta kimiyya da fasaha don ci gaban ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta hanya mai amfani da jama’a.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 ...
    Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira  ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu. Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa...
    Aƙalla shugabanni 15 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Zamfara sun sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).   An gabatar da waɗannan waɗanda suka sauya shekar ne a gaban Ministan Harkokin Tsaro na Ƙasa, Dr. Bello Mohammed Matawalle, a Abuja ranar Laraba, ta hannun Shugaban APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Umar Danfulani, tare da Sanata Tijjani Yahaya Kaura da Alhaji Lawal M. Liman.   A cewar wata sanarwa da Mai Magana da yawun jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, Minista Matawalle ya tarbi sabbin ’yan jam’iyyar da farin ciki, inda ya tabbatar musu da daidaito da damar ci gaba da aiki a cikin jam’iyyar.   Dr. Matawalle ya bayyana matakin da suka...