2025-09-18@03:49:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3170
«Jami ar Yakubu Gowon»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan damfara ne da suka damfari wani tsabar kudi har Naira Miliyan N1,030,000 ta hanyar ba saja da jami’an tsaro. Wadanda ake zargin sun hada da Nasiru Adamu mai shekaru 30 daga jihar Sokoto; Yusuf Sani, 49; da Aliyu Yusuf dan shekaru 25, dukkansu daga karamar hukumar Daura ta jihar Katsina, an kama su ne a ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 1:30 na rana a unguwar Dan’agundi ta Kano. Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Ƴan Ta’adda 15 A Borno Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a...
Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC. FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta. 2027: ’Yan adawa na ƙoƙarin sanya APC fara kamfe da wuri — Tinubu Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa Ya ce ya mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya bisa ayyukan ci gaba da ya ke gudanarwa. “Marar kishin Gombe ne kawai ba zai ga nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ke samu ba,” in ji Umar FK. Ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa za su mara...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da jan APC cikin harkokin siyasa kafin lokacin zaɓen 2027. Sai dai ya ce ba zai bari hakan ya karkatar da hankalinsa daga shugabantar Najeriya ba. NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 Za a koma rubuta jarabawar WAEC a komfuta Yayin da yake ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a Abuja, Tinubu ya yaba da ƙoƙrinsu wajen yaƙi da rashin tsaro tare da alƙawarin yin aiki da su kan batun ’yan sandan jihohi da kuma ayyukan gina hanyoyi. “A siyasa, ’yan adawa suna ƙoƙarin janyo mu mu fara kamfen da wuri. Amma duk da haka, ba zan bari a karkatar da hankalina ba. Na mayar da hankali...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karuwar hare-hare kan ’yan siyasa a kwanan nan ta sa wasu ’yan Najeriya sun fara fargabar abin da ka iya faruwa idan aka fara yakin neman zaben 2027. A kwanan nan ne dai wasu wadanda ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai hare-hare a kan tarurruka ko kadarorin jam’iyyu ko ma daidaikun ’yan siyasa. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Da Mutane Zasu Bi Wajen Neman Diyya DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda siyasar 2027 za ta kasance duba da yadda hali yake a yanzu. Domin sauke shirin, latsa nan
Nakore, memba ne na ƙungiyar Injiniyoyin Nijeriya (NSE), kuma ya taɓa rike muƙamin Sakataren Zartarwa na Hukumar Wutar Lantarki a karkara a Jihar Jigawa. Farfesa Kodage kuwa, kwararre ne a fannin ilimi da yake da gogewa a harkar koyarwa da al’amuran gudanarwa. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗen na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati take yi domin ƙarfafa shugabanci a tsarin ilimi da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin tafiyar da sababbin jami’o’in da aka ɗaukaka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babu aminci tsakanin kasar Iran da Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: An rasa amana tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, yana mai jaddada cewa; “Iran ba ta maraba da mayar da takunkumin kan kasarta, amma ta koyi yadda za ta 0kare mutuncin al’ummarta da fuskantar wannan yaki na rashin adalci.” Dangane da yiwuwar sake wani yaki kuwa, ya ce, “Iran a shirye take.” Hakan ya zo ne a wata hira da jaridar Guardian ta yi da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i. Game da sharuɗɗa uku da Turai ta sanar don yin shawarwari, Baqa’i...

Firaministan Senegal: Yadda Sinawa Ke Girmama Tarihi Da Kiyaye Labarun Abubuwan Da Suka Faru Da Su Na Da Matukar Burgewa
Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi. Abin da ya yi matukar ba shi mamaki shi ne yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye labarun abubuwan...

Qalibaf: Ya Bukaci Gwamnatocin Kasashen Musulmi Su Fito Su Yi Allah Wadai Da Ayyukan Isra’ila A Gaza
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Dole ne gwamnatocin Musulunci su dauki matakai na zahiri don dakile ayyukan kisan kare dangi ‘yan sahayoniyya a Gaza Muhammad Baqir Qalibaf, Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada bukatar da ke akwai ga al’ummar Musulmi da su yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi a Gaza ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen musulmi da su yi koyi da al’ummarsu da suka dauki matakai na zahiri don nuna rashin amincewa da duk wata hanyar aiwatar da kashe-kashen yahudawan sahayoniyya. A farkon taron majalisar a ranar Laraba, Qalibaf ya taya al’ummar musulmi murnar shigowar makon hadin kai, inda ya ce: A wadannan...
Sama da mutane dubu ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a yankin Darfur na kasar Sudan Sama da mutane 1,000 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta hallaka daukacin wani kauye a yankin Darfur na yammacin Sudan, a wani lamari da aka bayyana a matsayin daya daga cikin bala’o’i mafi muni da aka taba fuskanta a tarihin Sudan a wannan zamani, a cewar kungiyar fafatukar ‘yantar da al’ummar Sudan (SLM) da ke iko da yankin. Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, zabtarewar kasa gaba daya ta lalata kauyen Tarsin da ke gabashin Jebel Marra, kusa da yankin Soni, tare da kashe daukacin al’ummarta, wadanda aka kiyasta sama da maza da mata da yara sama da...
Kazalika, wannan biki na tunawa da nasarar fatattakar zalunci yana tunatar da mu mahimmancin waiwaye a kan tarihi. Fina-finai da aka yi game da hakan kamar “Dead to Rights”, da bikin nune-nunen a sassan yankin Macao, da faretin soja a birnin Beijing, hidindimu ne na sake duba tarihi, da sadaukarwar al’ummomin da suka gabata domin ci gaba da zaburar da na yanzu da wadanda za su zo gaba. Birnin Beijing ya cika da annashuwa da alfahari yayin da dandalin Tian’anmen ya shaida gagarumin faretin soji domin bikin na yau. An yi gaisuwar ban-girma ta hanyar harba bindigogi 80 a sassan babban birnin domin karrama mazan jiya da suka kwanta dama da kuma wadanda suke raye. Sojoji sun yi tattaki cikin...
Domin ya ce wannnan matsala ce da ta shafi ƙasa, kuma ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin sanin halin da ƙasar ke ciki. A cewarsa wannan babban zargi ne, don haka bai kamata a manta da shi ta hanyar yin jawabi ba tare da wasu gamsassun hujjoji ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Bakhae ya yabawa dan majalisar dokokin kasar Irish Michael McNamara dangane da aibata kasashen turai yadda suka dulmuya kansu a cikin kissan kiyanshin da HKI take aikatawa a Gaza, da kuma yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a kansu don tabbatar da zaman lafiya da adalci a duniya, amma suka ki sauke shi. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Bakhae yana fadar haka a a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X, inda ya nakalto Michael McNamana ya ke yin tar da HKI kan kissan kiayshin da yake aikatawa a gazam da kuma rushe-rushen da kuma korar Falasdinawa da take...
Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata. Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Wata kungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a jihar mai suna Katsina Security Community Initiative ce ta shirya taron na ranar Talata da nufin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaron da ta addabi jihar. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi Tinubu ya dawo da shugaban NTA da ya sauke Katsina dai ta shafe tsawon shekaru tana...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a rungumi akidun tabbatar da daidaito da adalci, tare da tsayawa tsayin daka kan tafarkin samar da ci gaba cikin lumana, da kara azamar inganta rayuwar al’umma a ko da yaushe. Shugaba Xi ya yi kiran ne a yau Laraba, yayin bikin taron tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Xi ya ce, shekaru 80 da suka shude, bayan shafe shekaru 14 ana gwabza kazamin yaki, al’ummar Sinawa sun yi nasarar murkushe dakarun mamaya na kasar Japan, tare da ayyana cimma cikakkiyar nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiya. Wannan muhimmiyar gaba...

Xi Jinping Ya Duba Faretin Rundunonin Sojoji Da Kayayyakin Soja, Shugabannin Kasashe 26 Su Ma Sun Halarci Bikin
Shekaru 80 da suka gabata, al’ummar kasar Sin sun samu gagarumar nasara a yakin kin hare-haren sojojin Japan bayan shekaru 14 masu cike da wahalhalu, tare da bayyana cikakkiyar nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. Sin ta fara yakin kin hare-haren ne tun daga farko har karshe a tsawon lokaci, kuma bisa gagarumar sadaukarwar al’ummun Sin, kasar ta bayar da goyon baya a babban fagen yaki na yaki da mulkin danniya a gabashin duniya, tare da ba da muhimmiyar gudummawa ga samun nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. (Amina Xu, Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Tarihi ya yi mana gargadi da cewa, makomar dan adam tana hade da juna, kuma kowace kasa, da kowace kabila dole ne su daidaita da juna, su zauna lafiya, su taimaki juna, domin ta haka ne kawai za a iya kiyaye tsaro na gama gari, da kawar da tushen yaki, da tabbatar da tarihi bai maimaita kansa ba! A jawabin nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, al’ummar kasar Sin babbar al’umma ce mai dogaro da kanta, wadda ba ta jin tsoron masu nuna karfin tuwo. A lokutan baya, an sha fama da gwagwarmaya tsakanin adalci da mugunta, tsakanin haske da duhu, tsakanin ci gaba da koma baya, kuma jama’ar kasar Sin sun hada kai sun tashi tsaye wajen yaki da...
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da...
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu. Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare...
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027. A ’yan kwanakin nan ne aka...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hakimin Bagaji Odo a Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi, David Wada. Rahotanni sun ce basaraken ya faɗa tarkon ’yan bindigar ne a ƙauyen Ojuwo Ugweche da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, yayin da yake dawowa daga taron sarakunan gargajiya a Abejukolo, hedikwatar ƙaramar hukumar. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Wani mazaunin yankin, Maji Ahiaba, ya bayyana cewa a ’yan kwanakin nan ƙauyen Ojuwo Ugweche na fuskantar hare-haren masu ta’adar garkuwa da mutane, duk da cewa a baya an taɓa tura jami’an tsaro da ’yan sa-kai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya kuma umarci da a maido da babban daraktan yada labarai, Mista Ayo Adewuyi ya kammala wa’adinsa na ragowar shekaru uku, wanda zai kare a shekarar 2027. Shugaba Tinubu ne ya nada Adewuyi a shekarar 2024. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman...
Bugu da kari, kasashe membobin kungiyar sun amince da kafa bankin bunkasa harkokin SCO, wanda a cewar Wang, zai yi matukar bunkasa samar da ababen more rayuwa, da raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashe membobin kungiyar. Dadin dadawa, kasar Sin ta sha alwashin kafa sabon dandalin hadin gwiwa, da cibiyoyi masu nasaba da makamashi, da samar da ci gaba marar gurbata yanayi, da tattalin arzikin dijital, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ilimi mai zurfi, da na koyar da sana’o’i da fasahohi. An kuma fitar da tsarin ingiza ci gaba mai inganci, wanda ya kunshi sassa irinsu na makamashi, da masana’antun sarrafa hajoji ba tare da gurbata yanayi ba, da tattalin arzikin dijital, da kirkirarriyar basira ko AI da...
Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta aukune bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin. Ya kuma kammala da cewa mutum guda ne kacal ya tsira da ransa a garin Marra dake kan tsaunin. Kungiyar ta bukaci taimakon MDD da kuma sauran kungiyoyin Agaji a duniya don fidda gawakin mutanen da zaizayar kassar ta bisne a kan tsaurin. Kasar Sudan dai tana cikin yaki fiye da shekaru...
Kan batun yiwuwar Obi zai koma PDP, Wike ya yi watsi da shi, ya ce hakan zai jawo wa jam’iyyar matsala. “Obi ya zargi PDP, ya ce jam’iyyar ta lalace. Yanzu kuma jam’iyyar ta gyara kenan a gare shi? Wannan zai kashe jam’iyyar,” in ji shi. Wike ya ce dawo da Obi saboda kawai neman mulki zai rusa ƙa’idoji da mutuncin jam’iyyar. Ya dage cewa hanyar da PDP za ta sake bi domin farfaɗowa ita ce bin tsarin rabon mulki, adalci da gaskiya, ta yadda shugabancin ƙasa zai koma Kudu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Rahotanni sun bayyana cewa Kotu a kasar Finland ta yanke wa dan Najeriya mai ‘rajin kafa kasar Biyafara’, Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci. Kotun ta same shi da laifin koƙarin harzuka jama’a da niyyar ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan kungiyar ta’addanci. Haka kuma ta same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara shida a gidan yari. Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi kokarin karfafa rajin kafa yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba, yana mai jaddada cewa: Iran na daukar muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian za...
Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Afghanistan ya haura 800, yayin da ake sa tsammanin karuwar wadanda suka jikkata Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa ran zai karu. Da sanyin safiyar yau Litinin ne, kamfanin dillancin labarai na RTA ya ruwaito hukumomin lafiya na kasar na cewa, suna ci gaba da kokarin gano hakikanin adadin wadanda suka mutu, yayin da suke ci gaba da kokarin isa wasu yankunan da lamarin ya shafa. Ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa, Girgizar kasar ta lalata kauyuka uku a gundumar Konar gaba...
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare. Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi. Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa...
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar. Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025 Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan Daje Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Neja Ya gode wa mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a duk inda makomar aiki ta kai su. Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa ya bar Sakataren Gwamnatin Jihar, da Shugaban Ma’aikatansa da kuma Mataimakinsa da wasu manyan jami’an ofishinsa a muƙamansu. Daga kanmu,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu. Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku. Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata An yi jana’izarta a fadar Sarkin Katsina ƙarƙashin jagorancin Imam Mustapha Gambo. Ɗaruruwan mutane sun halarci jana’izar, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da kuma al’ummar gari. Bayan kammala jana’izar, Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai tausayi kuma mai son zaman lafiya. Ya roƙi Allah Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta haƙurin wannan rashi. Haka kuma, Gwamnan...
Bugu da kari, a wannan rana shugaba Xi ya gana da shugabannin wasu kasashe da suka zo nan kasar Sin don halarar taron, ciki har da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, shugaban Azerbaijan Ilham Heydar oglu Aliyev, firayim ministan Armenia Nikol Pashinyan, shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da shugaban Maldives Mohamed Muizzu,da Firaministan Vietnam Pham Minh Chinh kana da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China. Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar...

Pezeshkian: Taron Kolin Shanghai Wata Muhimmiyar Dama Ce Ta Bunkasa Alakar Bangarori Da Dama Na Yankin
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Taron koli na Shanghai wata muhimmiyar dama ce ta bunkasa huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi la’akari da karfafa dangantaka da kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) daya daga cikin manufofin ziyararsa a kasar China da halartar wannan taro. Ya ce, taron kolin na Shanghai wata dama ce mai matukar muhimmanci da kuma dacewa don inganta huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya da sauran kasashe. Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya bayar da safiyar Lahadi a filin jirgin sama na Mehrabad na Tehran kafin ya tashi zuwa kasar China don halartar taron kolin Shanghai: Kasashe mambobin kungiyar Shanghai sun kai kimanin...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada ci gaba da gwagwarmaya soji kan makiya ‘yan mamayar Isra’ila Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Tafarkin al’ummar Yemen na goyon bayan al’ummar Falastinu yana ci gaba kuma tabbatacce kuma yana kara ruruwa. A cikin jawabinsa Sayyed al-Houthi ya ce: ‘Yan kasar Yemen suna fuskantar makiya a dukkan fagage: ta fuskar siyasa, soja, tattalin arziki da kuma ta kafofin watsa labarai, ba za su yi rauni ba sakamakon wuce gona da iri da ake yi kan su. Ya kara da cewa al’ummar kasar Yemen suna yin jawabi da ya hau kansu wajen taimakawa wa al’ummar Falastinu, yana mai bayyana cewa; Suna tare da...
A nata bangaren, darektar kula da yankin Asiya da Fasifik da Gabas ta Tsakiya a ma’aikatar kula da hadin kan Afirka da harkokin wajen kasar Senegal Cathy Diagne Thioye, ta bayyana dandalin FOCAC a matsayin abin koyi a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da yin aiki tare don aiwatar da muhimman ayyukan da suka sa a gaba a karkashin tsarin dandalin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yu ya ce, kasar Sin ta tafka asarar rayukan sojoji da fararen hula sama da miliyan 35 da kuma asarar tattalin arzikin da ya zarce dalar Amurka biliyan 600 a lokacin yakin duniya na biyu. Ya yi nuni da cewa, tsayin dakan da kasar Sin ta yi ya yi mummunar wargaza mulkin danniya, tare da ba da gudummawa mai tarihi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jakadan shugaban kasar Rasha na musamman kan al-amuran yaki a Ukraine ya bayyana cewa masu son yaki a cikin shuwagabannin kasashen turai suna zagon kasa ga kokarin shugaba Trump na kasar Amurka yake yi na kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kirill Dmitriev yana fadar haka, a shafinsa na X , inda yake zargin shuwagabannin kasashen turai da hana tsaida yaki a Ukraine. Dmitriev ya kara da cewa Brussels na zangon kasa ga shirin tsaida yakin tare da dorawa shugaban kasar Ukraine gabatar da bukatun ba zasu taba yiyuwa Rasha ta amince da sub a. Ya kara da cewa shuwagabannin kasashen Turai suna tsawaita yakin har zuwa lokacinda Al-amura zata sake komawa...
Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu. Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin taimakon kasashen da makamai da horo. Amma ganin yadda har yanzu kasashen ke ci gaba da fuskantar hare-hare, shin za a iya cewa alaka da Rasha ta yi musu rana? Sababbin kawayen Moscow Tun a 2021 Rasha ke tura dubban sojoji da makaman da suka kai miliyoyin Dala zuwa Mali da Burkina Faso da Nijar. Tana haka ne domin taimakon kasashen wajen yaki...
Cibiyar CDC Na Afirka Da WHO Suna Aiki Tare Don Kawo Karshen Cholera Cibiyar Africa Centres for Disease Control and Prevention (Africa CDC) da kuma hukumar lafiya ta Dunita (WHO) sun hada kai don ganin an kawo karshen cutar colera a nahiyar ta Afirk, tare da hada kai da kasashen Nahiyar. Kamfanin yana labarai ta interner Afriva News ya bayyana a ranar Jumma’a kan cewa, shirin wanda yake cikin shirye-shiryen kiwon lafiya na cibiyar Afrika CDC na shekara ta 2025-2026. Sannan manufar shirin itace rage cutar ta Colera da kasha 90 a wannan shekarar, sannan kawo karshen cutar kwata-kwata a kashe 20 na nahiyar nan da shekaru 2030. Cutar colera dai tana kama mutane ne ne saboda shan ruwa marasa...
Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta Bayer Liberkusen, wato Piero Hincapie. Chelsea Da alama har yanzu mai horarwa Enzo Maresca bai hakura da karin cefane ba kafin rufe kasuwar, yayin da yake neman Alejandro Garnacho na Man United da danwasan RB Leipzig Dabi Simons. Sai dai komai zai dogara ne da yawan ‘yanwasan da ta iya sayarwa kamar Nicolas Jackson da Christopher Nkunku da Tyrikue George, wadanda...
Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta? Dan wasan dan kasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a ‘yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga kungiyar kwallon kafa ta Brentford. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo 20 a gasar da aka kammala da kuma bayarwa a ci bakwai. Manchester United na tsaka da sake gina kungiyar karkashin mai horarwa Ruben Amorim bayan gama gasar a mataki na 15, wanda shi ne mafi muni a tarihin kungiyar na Premier League. Mbeumo zai fuskanci matsi nan take domin ya nuna kwarewarsa tare da Matheus Cunha da Benjamin Sesko wadanda duka kungiyar ta sayo a wannan kakar domin kara karfin...
A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a birnin tashar ruwa na Tianjin dake arewacin kasar Sin. Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Masar na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, ya kuma yi kira da a yi amfani da damar bikin cika shekaru 70 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekara mai zuwa, wajen cimma nasarar gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai daya a sabon zamani, da kara bayar da gudummawa don wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, da bunkasa ci gaba da walwalar sassan kasa da kasa. A dai yau din, shugaba Xi ya gana da firaministan Cambodia Hun...
Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in. An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana. Abin da nake nufi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da zai iya wargaza dangantakar abokantaka tsakanin Iran da Armeniya. Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa, damuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin Caucasus na baya-bayan nan, musamman kasancewar dakarun kasashen waje a wannan yanki mai matukar muhimmanci, an kawar da su sosai bisa la’akari da fayyace da kuma tabbacin da jami’an kasar Armeniya suka bayar. Ya ce, “Dole ne su...
Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya gana tare da tattaunawa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya a safiyar yau. A cikin wannan taro, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana gamsuwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi kan matakin tattalin arziki, siyasa, tsaro da kasar Armeniya, tare da jaddada hadin gwiwa da...
Watan Mayu 1956,aka gabatar da kudurin niyyar yin doka a majalisar Kudu maso gabashin Nijeriya, suka gabatar da kudurin zai bada dama ta a amince da Sarakunan gargajiya, wanda ta haka ne aka samu damar kafa majalisar Sarakunan Kudu maso gabashin Nijeriya, duk kuwa a lokacin da akwai turjiyar da aka samu daga masu fafutukar tafiyar da lamurra yadda suka dace, saboda sun ki goyon bayan a sa su masu Sarautun gargajiya a harkokin yadda ake tafiyar da gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan. Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye. Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu...
‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi. Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma, kuma dole doka kullum ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babbar manufarta. Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan taro wajen tattauna muhimman batutuwan da suke tsara makomar Nijeriya.” “Ya ce, ‘Ina fatan wannan taro zai ba ku damar tattauna batutuwan da suka shafi makomar al’ummarmu. Abubuwa uku ne manya: Ci gaba da kokari wajen gyaran dokoki domin a hankali...
Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar. Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi. Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar...
“A yayin aikin ceto, wanda aka sace din ya sami raunin harbin bindiga a kafarsa ta hagu bayan ‘yan ta’addan sun bude wuta lokacin da suke kokarin tserewa,” in ji sanarwar. An garzaya da wanda aka ceto zuwa asibiti, kuma a halin yanzu yana samun sauki. Kwamishinan ‘Yansanda, Bello M. Sani, ya yaba wa jarumtar jami’an da ‘yan sa-kai bisa saurin daukar mataki, tare da sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Kebbi. “Wannan aikin ceto ya nuna jajircewarmu wajen kawar da miyagun laifuka a jihar. Ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron kowace al’umma,” in ji Sani. ...
A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas. Hotuna: Bassey Willie
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci. Wasu sun rasa matsugunansu saboda rashin tsaro. Wasu kuma suna asibiti ba tare da kulawa ta gari ba—ko kuma ba za su iya zuwa ba saboda babu kuɗi a hannunsu. “Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba...
Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021. Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin dala biliyan 1.46 zuwa yau daga dala biliyan 39.54 a ranar daya 19 ga watan Agustar shekarar 2025, suka karu zuwa i dala biliyan 41.00. Wannan ya nuna yadda karuwar Asusun ta kai zuwa kaso 3.69 a kasa da makwanni uku, da suka gabata. Bugu da karu, Asusun ya samu wannan karuwar ce, saboda yawan shigowar kudaden musaya na waje cikin kasar da...
“Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi. Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta. “Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare,...
Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja. Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar. Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro. Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi Ya ruwaito...
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar. Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...

Sin Ta Sanar Da Rukuni Na Hudu Na Abubuwa Da Wuraren Tunawa Da Yakin Kin Jinin Mamayar Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima, rashin saka rigar iyo, amfani da jiragen ruwa marasa inganci, da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro. Duk da wannan, gwamnati ba ta ɗauki matakan tsaro ba. A halin yanzu, magidanta a Shagari da ƙauyuka maƙwabta na cikin tashin hankali suna jiran labari game da ‘yan uwansu da suka ɓace, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen yakin HKI suka cilla a kan motarsa a kauyen Sair cikin lardin Nabadiyya. Tashar talabijin ta Al-mayaddeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, sojojin yahudawan sun jefa boma-bomai har guda hudu a kan garin Kafar Kila a kudancin kasar ta Lebanon. Labarin ya kara da cewa a garin kafar kila, sojojin yahudawan sun kai hare hare da dama a yau Jumma’a bayan wadanda muka bayyana amma basu kai ga kashe ko raunata wani ba. A jiya Alhamis ma jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hare hare a wurare da dama daga...
Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike mai ƙarfi na ƙwararrun jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar rundunar ‘sojan Najeriya, domin gano abin da ya jawo aka kashe wani jami’in soja da wani sifeton ’yan sanda ya yi a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), CSP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu a hedikwatar rundunar da ke Bauchi a ranar Juma’a. Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Wakil ya ce, an ɗora wa kwamitin alhakin tattarawa da...
Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, manyan tituna, tashoshin ruwa da wutar lantarki, gadojin kan hanyar ruwa da masana’antu, duk wadannan an tanade su ne don su zama hanyar rage talauci da tallafawa al’umma. Ta hanyar inganta yanayin rayuwa da samar da damarmakin tattalin arziki, kasar Sin ta yi nuni da cewa, tana kara karfafa martabar jama’ar Afirka ta hanyar samar musu da ci gaba. ’Yancin Cin Gashin...
Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi. Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su dukufa da yin addu’o’in neman zaman lafiya a yankin. Da yake magana da kafar BBC bayan taron, mai ba da shawara ga ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, kungiyar ta yi nazari da bitar matsalolin da suke addabar arewa tare da cimma matsayar cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa. “Matsalolin nan ga su nan a zahirance, kuma dole ne a tursasa gwamnati ta...
Da aka tuntubi Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed mai ritaya, ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce; jami’an tsaro sun shawo kan lamarin. Haka zalika, mazauna Ndanaku da ke Karamar Hukumar Patigi a Jihar Kwara, sun kauracewa wurin sakamakon hare-haren ‘yan bindiga. Kazilika, harin na zuwa ne makwanni kadan bayan faruwar makamancin haka a garin Babanla da ke Karamar Hukumar Ifelodun. Kwamandan ‘yan banga, Gina Gana; wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa; an kai hare-hare guda biyu ne kwanaki uku da suka gabata, wanda ya tayar wa da kowa hankali a garin. Har wa yau, a makon day a gabata ne Gwamna...
Kungiyar Marafa ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da watsi da tsarinsa na siyasa da kuma rashin tallafawa al’ummar da ke fama da matsalolin tsaro. Daga ƙarshe, ta bayyana cewa Marafa da dukkan magoya bayansa a kananan hukumomi da mazabu 147 na Zamfara sun fice daga APC, kuma nan gaba za su bayyana sabon matsayar siyasar da za su bi. — Wannan sigar za ta fi ja hankalin masu karatu a yanar gizo. Kana so in ƙara ƙaramin taken ƙasa (sub-headline) da ke ƙara jan hankali, irin na jaridu, misali: “Tsohon Sanatan Ya Ce Zamfara Ta Fi Kowa Fama da Sace-Sace Amma Gwamnati T a Yi Watsi da Ita”? Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar. Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi. Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin...
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya soki gwamnatin tarayya kan ƙarin kuɗin fasfo da aka sanar cikin makon nan. Ya bayyana cewa wannan ƙarin ya nuna rashin la’akari da halin da talakawa ke ciki a yau. A cewar Obi, sabon farashin fasfo na – ₦100,000 mai shafuka 32 da ₦200,000 mai shafuka 64 – ya fi sabon albashin ƙasa na ₦70,000, abin da ya ce bai dace ba da halin da ma’aikata ke ciki. Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000 Ya zargi gwamnati da ƙara ƙaƙabawa jama’a ƙarin nauyi maimakon sauƙaƙa musu, musamman a lokacin da tattalin arziƙin...
Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda ka ke tare da shi ya fahimci me kake faa ba.” Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), Dakta Sunusi Yakubu Ahmed, ya bayyana jin dadinsa matuka bisa zabar kwalejin don gudanar da wannan taron. Dakta Sunusi ya ce: “Tun lokacin da na ga an yi irin wannan taron a Jami’ar Northwest, na bukaci nima ina da burin...
Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar. Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki. Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa. Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke shirin, latsa nan
Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna. Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta tarayya, domin kokarin gano musabbabin faruwar al’amarin. A cikin sanarwar da NRC ta fitar a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa; jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan hanyarsa. Kazalika, hukumar ta bayyana cewa; daga cikin fasinjojin, mutum akalla 14 ne suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuma,...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dangantaka tsakanin Iran da China na dauke da dabarun manufofi masu kyau Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasar Iran na da sha’awar gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana da kasar China, musamman a fannin raya dabarun kiyaye hanya, yana mai bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin kyaukyawar dabara. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis don daidaita yin nazari kan fannoni daban-daban na dangantaka da hadin gwiwa, da kuma bayyana ajandar ziyarar shugaban kasar China. Taron ya samu halartar manyan jami’ai da shugabannin hukumomin zartarwa da abin ya shafa. A yayin wannan taro, an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi...
Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma suna farin ciki da arangama kai tsaye da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan soji na goyon bayan Gaza muddin gwamnatin ta ci gaba da yakin da take yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan birnin Sana’a ba zai shafi goyon bayan da al’ummar Yemen ke yi ga...
Yanzu haka a nan kasar Sin ana ta shirye-shiryen gudanar da babban bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar sojojin Japan, da nasarar yakin kin tafarkin murdiya, wanda shi ma wani lokaci ne da zai dada tabbatarwa duniya zahirin abubuwan da suka wakana, tare da karyata sassan dake kokarin lullube gaskiya, da kaucewa daukar alhakin ta’asar da aka aikawa al’ummar Sin a yayin mamayar birnin Nanjing. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Manyan Jami’ai A Ma’aikatar Tsaro Ta...

Baki Kusan 50 Daga Kasashe 30 Na Turai Za Su Halarci Bikin Tunawa Da Nasarar Yakin Turjiyar Sinawa Kan Zaluncin Japanawa
A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya. Wannan ya nuna niyyarsu ta hada hannu wajen tunawa da tarihi da kiyaye zaman lafiya da adalci. Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil...
An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89. Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya. Kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tekun duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Teku ta Duniya, Hukumar Kwastam ta Duniya, da tsarin Majalisar Dinkin Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare. Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen...

Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Shigo Da Su Daga Kasashe Masu Karancin Ci Gaba Na Afrika Ya Karu Da Kaso 10.2 Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata
Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce daga watan Junairu zuwa Yulin bana, darajar abubuwan da Sin ta shigo da su kasar daga kasashe masu karancin ci gaba na Afrika, ta kai dala biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 kan na bara. Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, inda ta ce wani rahoto da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa, karkashin jagorancin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika ya zama wani muhimmin karfi mai ingiza ci gaban tattalin arziki a nahiyar. Ta ce cinikayya tsakanin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun DRUZHBAC Na Kasar Rasha Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa farashin man ya tashi a jiya laraba, amma kuma tare da wannan fatan ya sake tashi. A cikin makonnin da suka gabata ne sojojin kasar Ukraine suka kai hare-hare kan bututun man tare da amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa. Labarin ya kara da cewa tuni kamfanonin man fetur a kasashen Slovakia da kuma Hungary sun bayyana cewa...
3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka. Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci. Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na...
’Yan Majalisar Dattawan kasar Mexico sun yi naushe-naushe a ranar Laraba lokacin da muhawara ta yi zafi a zauren majalisar. Rahotanni sun ce an fara ba hammatar iska ne bayan shugabannin ’yan adawa a majalisar sun bukaci sojojin Amurka su shiga kasar su taya su yaki da dillalan miyagun kwayoyi. Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makare Shugaban marasa rinjaye a makalisar, Alejandro Moreno, shi ne dai ya je wajen yin jawabi a fusace bayan kammala zaman majalisar, inda ya tunkari shugaban majalisar, Gerardo Fernandez Norona, saboda hana shi damar yin Magana. A cikin wani bidiyo a kafafen sada zumunta dai, an ga...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Ofone Modupe Alasin, a karamar hukumar Efon-Alaaye da ke jihar. Kakakin rundunar a jihar, SP Sunday Abutu ne ya tabbatar da kisan matar, inda ya ce an kama mijinta yayin da ake ci gaba da bincike. ’Yan sanda sun ceto yara 3 da aka sace a Kaduna Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai Binciken farko-farko dai ya nuna mijin ne ya lakada wa matar tasa duka saboda ta ki zuwa gonarsu a kan lokaci. Wani makwabcin gonar ya ce ya jiyo marigayiyar tana ihun neman taimako, amma duk da haka mijin nata ya ci gaba da nada mata na jaki. Kazalika,...

Wakilin Kasar Rasha A Vienna Ya Sanar Da Sake Dawo Da Ayyukan Hukumar IAEA A Cibiyar Busharhr Na Iran
Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna ya sanar da cewa: An sake dawo da ayyukan IAEA a cibiyar Bushehr Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya sanar da dawo da ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a cibiyar makamashin nukiliya ta Bushehr dake kudancin kasar Iran. A cikin wani sako da ya aike a shafinsa na X, Ulyanov ya rubuta cewa: Iran ta sake tabbatar da cewa, ko da bayan hare-haren da sojoji suka kai wa cibiyoyin nukiliyar kasarta na zaman lafiya da ke gudana karkashin hukumar ta IAEA ba bisa ka’ida ba, abin kunya ne, a matsayinta ta mamba ta hukumar...
Jami’ar kasa da kasa a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Kananan Yara masu fama da yunwa a Gaza suna mutuwa sannu a hankali Inger Ashing, shugabar kungiyar Save the Children, ta tabbatar da cewa: “Yaran Gaza da ke fama da yunwa sun kai ga mataki mai tsanani,” inda ta bayyana dalla-dalla kan mutuwarsu a hankali, kuma sun kai ga matakin da ba su iya yin kuka. Inger Ashing ta fadawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba cewa: Yunwar da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a Gaza a makon da ya gabata, ba wai kawai “kalmomi ne na fasaha ba,” ta kara da cewa: “Lokacin da babu isasshen abinci, yara suna fama da rashin abinci mai...
Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana a cikin wani rahoto na baya-bayan nan cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fama da babbar matsala ta soji da tsaro, bayan da ta kasa dakatar da hare-haren da Yemen ke kai mata hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki tun daga ranar 19 ga Oktoban shekara ta 2023. Jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila sun bayyana bangaren Yemen a matsayin “wanda ya fi kowa hauka a yankin,” suna masu gargadin cewa shiga fafatawar da suke yi da su zai haifar da mummunan sakamako ga haramtacciyar kasar Isra’ila, ganin yadda suke ganin dakarun Yemen...
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ta ceto wasu yara guda uku da aka sace tare da kama mutum uku da ake zargi da sace su. A ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025, wani mutum ya kai rahoton cewa an sace ’ya’yansa uku. An kashe mutum 3 a faɗan ƙungiyoyin asiri a Legas ’Yan bindigar da suka sace ma’aurata a Katsina na neman N600m Yaran sun haɗa da Aslam Umar Lukman mai shekaru 14, Suleiman Umar Tanko mai shekaru 12 da Aliyu Umar Tanko mai shekaru 10. Waɗanda suka sace yaran sun nemi a ba su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa. ’Yan sanda sun yi amfani da dabaru inda suka cafke shugaban ƙungiyar, Richard Philip. Yayin bincike, ya...
An kai shi asibiti, inda aka kula da shi sannan aka sallame shi domin halartar jana’izar iyalan nasa. Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Bello Garba, ya ce ba su samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma sun shirya gudanar da bincike kan lamarin. An binne mamatan bisa tanadin addinin Musulunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa. Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda. Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata. A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su. Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar...
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a. Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya...