2025-06-20@23:04:53 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2038
«sinadaran man fetur na»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun yi maganar rikice-rikicen da ke faruwa a yankin da kuma hanyar warwaresu. Taron oslo na shekara shekara dai a wannan karon ya maida hankali ne kan abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya da kuma hanyoyin da yakamata abi don rage halin da ake ciki a yankin. Musamman matsalar yaki da kima kissan kiyashin da ke faruwa a...

IPOB A Najeriya Ta Jawo Asarar Rayuka Kimani 700 Da Kuma Kudade Kimani Naira Triliyon N7.5 Tun Shekara ta 2021
Mutane kimani 776 ne suka rasa rayukansu sannan kudade kimani naira Triliyon N7.6 ne aka yi a sararsu a cikin shekaru 4 da suka gabata a yankin kudu maso gabacin Najeriya sanadiyyar zaman gida wanda kungiyar IPOB ta tilasta masu. Jaridar Premium time ta Najeriya ta bayyana cewa rahoton hukumar tsaro na SBM Intelligence ta fitar a watan Mayon da ya gabata ya nuna cewa, da farko Kungiyar ta IPOB ta tilastawa mutanen yankin zama gida na don ganin an saki shugaban kungiyar Namdi Kano, amma daya baya sai ta zarce zuwa yanzu. Kuma hakan ya hana abubuwan ci gaba da kuma harkokin kasuwanci makarantu da kuma ayyukan gwamnati tafiya. IPOB dai tana bukatar warewa daga tarayyar Najeriya don kafa...
A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya kusa da doron kasa a lardunan Jiangxi, Sichuan da Guangxi inda ake fuskantar dimbin kalubalen fadada hanyoyi saboda yanayin tsaunukansu. Tabbas, duka wadannan sun zo da wani irin sabon salo a duniya da kasashe za su yi koyi da kasar Sin wajen zamanantar da sha’anin jigilarsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar. LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar gundumar Langai ta karamar hukumar Mangu a yayin harin. Kokarin jin ta bakin jami’im yada labarai na rundunar ‘Operation Save Haven (OPSH)’, Manjo Samson Zhakom ya ci tura domin wayarsa a kashe take a lokacin rubuta wannan rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato. Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a ƙaramar hukumar ta Mangu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin a wannan makon tsakanin yan kabilar Mwaghavul da Fulani. Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar...
Cherki ya buga wasansa na farko a Lyon yana da shekara 16 a watan Oktoban 2019 kuma ya bar kungiyar inda ya ci kwallaye 29 sannan ya taimaka aka jefa 45 a wasanni 185 da ya bugawa kungiyar ta Faransa. Cherki ya wakilci kasar Faransa kuma ya lashe lambar azurfa a gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a bara. Daraktan kwallon kafa na Manchester City, Hugo Viana ya ce, “Babu shakka a yanzu Cherki yazo inda ya dace kuma zai cigaba a karkashin jagorancin Guardiola, kuma na yi imani zai iya zama babban dan wasa a duniya tare da goyon bayan abokan wasa da masu horarwa”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Don haka, a cikin sanarwar da aka fitar a wannan karo, kasashen Afirka sun nuna yabo kan jajircewar kasar Sin, da kuma kudurin da kasar ta dauka na kare adalci, da kuma ingancin tsare-tsaren tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Har ila yau, kasar Sin ita ma ta nuna godiya ga kasashen Afirka, kan yadda suke bin ka’idojin kare ‘yancin kai, da adalci, tare da tsayawa kan matsaya guda wajen fuskantar matsin lamba da aka sanya musu. Hakika idan mun tantance kwarin gwiwar Sin da Afirka, za mu ga da farko ya zo daga dangantakarsu mai dorewa ta hadin gwiwa da juna. Za mu iya daukar misalin bangaren ciniki: daga shekarar 2000, lokacin da aka kafa dandalin tattaunawar...
Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, ta dakatar da shugabar Ƙaramar Hukumar Bekwara, Hon. Theresa Ushie, na tsawon wata uku, domin a gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake mata. An ce kimanin wakilan ƙaramar hukumar 10 daga cikin 11 ne suka yi ƙarar shugabar, inda tara daga cikinsu suka rattaba hannu suna goyon bayan a dakatar da ita. Gwamnatin Kano za ta binciki musabbabin gobarar kasuwar Farm Center Za a dauke wa jihohin Arewa maso Gabas wutar lantarki na tsawon kwana 4 Ɗaya daga cikin wakilan ne kawai bai yarda ba. Ana zargin Hon. Ushie da amfani da kuɗin Ƙaramar Hukumar ba tare da shawarar majalisar jihar ba, tare da yin wasu muhimman ayyuka ba tare da tuntuɓar ’yan...
Bayanai sun nuna cewa, harin na faruwa, aka sanar da jami’an tsaro. Sun isa cikin gaggawa da motocinsu da jirgin sama mai saukar ungulu. Amma maharin ya ƙi miƙa wuya, hakan ya sa aka bindige shi. Daga cikin waɗanda suka mutu, mata shida ne, maza uku, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga. Hukumomi sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike don samo ƙarin bayani game da wannan mummunan al’amari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin Dakon Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cewa za a dauke wutar lantarki a ilahirin jihohin yankin Arewa maso Gabas guda shida na tsawon kwana hudu. A cikin wata wasika da ya aike wa kamfanonin rarraba wutar lantarki da ke kula da jihohin shida, TCN ya ce yayin da a wasu jihohin wutar za ta dauke gaba daya, wasu yankunan kuwa karancin wutar za a samu a tsakanin kwanakin. Jihohin da lamarin zai shafa sun hada da Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe. Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000 DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Wasikar wacce ke dauke da sa hannun...

Iran Ta Sami Nasara Akan Korea Ta Arewa Akarkashin Share Fagen Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Na Kwallon
Kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasarar akan abokiyar karawarta ta kasar Korea Ta Arewa da kwallaye uku masu kyau a wasan da aka yi a filin wasa na “Azadi” na Tehran. Kasashen biyu dai suna a karkashin; bangare na uku a Asiya saboda share fagen kai wa ga shiga gasar cin kofin kwallon duniya na 2026. Dan wasa mai suna Muhammad Muhibbi ne ya ci kwallon farko, a mintuna 74 da fara wasan, sai kuma Mahdi Darimi a mintuna 77, sa Amir Husain Husain zadeh, a minti 3 da aka kara, bayan cikar mituna 90. A bangaren kungiyar kwallon kafa ta Korea Ta Arewa kuwa, ta kammala wasannin nata da ‘yan wasa 10 bayan da aka kori daya...
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓe shi kaɗai. “Ku bai wa Kudu tikitin, ku ga sakamako. Amma idan PDP ta ci gaba da tafiya a kan wannan kuskure, to, za ta fuskanci babbar matsala a 2027,” Yusuf ya bayyana. Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ba ɗa jam’iyyar PDP ba ne a yanzu, yana tare da wata sabuwar tafiyar haɗin gwiwa ta siyasa. Yusuf ya ɗora alhakin faɗuwar jam’iyyar a zaɓen 2023 kan rashin kyakkyawan shugabanci da kuma rabon tikiti ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce rikicin cikin gida da kuma gazawar PDP wajen kulawa da ‘yan Kudu ne suka sa jam’iyyar ta faɗi. Ya kuma nuna takaicinsa game da sauya sheƙar Gwamnan...
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000. Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan neman bukatar janye karar da aka daukaka. Bukatun dai na kunshe ne a cikin wasu kararraki masu lamba CV/395/M1/2025 da kuma CV/395/M2/2025, wadanda aka shigar a ranakun uku da kuma 25 ga watan Mayun 2025, wanda a cikinsu aka ambaci sunan Akpabio a matsayin mai daukaka kara. DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Rikicin Filato:...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa. A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya. Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’an kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka. NAJERIYA...
Akpabio ya shigar da buƙatu a gaban kotun inda ya nemi ƙarin lokaci don ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Maris, 2025. Wannan shari’a ta haɗa da Sanata Natasha da ke ƙarar Sakataren Majalisar Tarayya da wasu mutane uku kan dakatar da ita. Haka kuma, Akpabio ya nemi kotu ta ba shi izini ya ɗaukaka ƙara da kuma dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar a Babbar Kotun har sai an yanke hukunci a kotun ɗaukaka ƙara. Sai dai yanzu da aka janye ƙorafe-ƙorafen kuma kotu ta yi watsi da su, hakan na nufin waɗannan bukatu na Akpabio ba za su ci gaba da sauraron su a...
Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare da makamai masu linzami kan tashar Jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) a safiyar yau Laraba. Kuma makaman sun sami inda ake bukata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistet a hare-haren, kuma sun kaisu ne tallafawa Falasdinawa a Gaza wadanda HKI takewa kissan kare dangi. Labarin ya kara da cewa daya daga cikin makamai masu linzamin ya sami tashar jiragen kai tsaye ba tare da an kakkabishi ba. Makaman sun hargitsa zirga-zirgan jiragen sama, a tasahr na wani lokaci sannan ya sa yahudawa tsakiyar Yafa (Telaviv) da yankin yamma da kogin Jordan da birnin Qudus...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bada sanarwan kakabawa ministocin HKI guda biyu takunkuman tattalin arziki saboda ra’yinsu na wuce gona da Iri wanda zai bata duk wani shirin da kasashen duniya suke da shin a tabbatar da zaman lafiya a yanking abas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kira-kirayen ministocin na kara mamaya da kuma korar falasdina daga yankin yamma da kogin Jordan ne yasa burtaniya ta nuki wannan batakin. Bezalel Smotrich dai , wanda shi ne ministan kudi na HKI ya ce HKI zama kara mamayar yankin yamma da kogin Jordan, kafin zaben shekara ta 2026, sannan ya rantse kan cewa za’a share falasdinawa a gaza, kuma zasu wargaza kungiyar Hamas a cikin...
Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa yanzu ya nuna irin yadda hukumar IAEA take mika bayanan da ta samu daga cibiyoyin Nukliya na kasar Iran ga HKI. Wanda ya kaiga kissan masana da kwararrun a fasahar makamacin Nukliya a baya. Bayanan sun bayyana yadda hukumar ta IAEA take mikawa dukkan takardun sirri na shirin makamashin nukliya na kasar Iran ga makiyanta don su yi aiki a kai. Banda HKI wadannan bayanan...
Mahara sun kone gidaje akalla 96 a yankin Gyenbwas na gundumar Langai da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato. Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa maharan sun kuma kwashe musu kayan abinci da katifu da kuma shanu da sauran kayayyaki. Alhaji Yakubu Umar, wanda kuma shi ne Madugun Langai ne ya shaida wa Aminiya hakan a ranar Talata. A hanzarta kwangilar yashe Madatsar Ruwa ta Alau — Gwamnatin Borno Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara Ya kuma ce bayan mutum biyun da aka kashe musu ranar Litinin, sun kuma kara samo gawar mutum daya a yankin, wanda hakan ya kai adadin mutanen da aka kashe yayin harin zuwa uku. Mazauna yankin dai na zargin ’yan kabilar...
Bayan kammala aikin Hajjin bana, Saudiyya za ta fara bayar da bizar umara daga gobe Laraba. Kazalika mahukuntan ƙasar sun ce dakatarwar shiga birnin Makkah ba tare da takardar izini ba zai ƙare daga ranar Larabar 11 ga watan Yunin 2025. Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobara Ma’aikatar Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ce za ta fara karɓar sabbin baƙi masu shigar ƙasar da bizar Umarah daga gobe Laraba, 11 ga watan Yuni. Sanarwar na zuwa bayan kammala aikin Hajjin bana wanda kimanin mutum miliyan 1.6 daga faɗin duniya suka halarta. Saudiyya takan dakatar da bayar da bizar umara makonni gabanin aikin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jajanta wa al’ummar kasuwar katako ta bayan kara da ke Birnin Kebbi bisa ibtila’in gobara da ta auka musu. Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa. A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya A lokacin da ya zagaya domin duba irin ɓarnar da wutar ta yi a kasuwar, Mataimakin Gwamna ya yi kira da su mayar da lamarin ga Allah da kuma ɗaukar wannan ibtila’in a matsayin jarabawa daga gare Shi. Haka kuma, ya miƙa wa ’yan kasuwar gudumawar...
Masu bayar da agajin gaggawa sun isa wurin jim kadan bayan karfe 9 na safe, inda hargitsi da firgici ya da baibaye mazauna harabar makarantar. A cewar ‘yansandan yankin, dan bindigar ya shiga ajin karatun ne dauke da bindiga inda ya bude wuta kan mai uwa da wabi, sannan kuma ya harbe kansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani taron sauraron bayanai da aka gudanar a kwanan baya, ‘yar majalisar wakilan kasar Amurka Madeleine Dean ta yi wa ministan kasuwanci na kasar, Howard Lutnick tambayoyi game da yanayin ciniki da manufofin harajin kwastam na kasar, inda ta tono shirmen da ke cikin matakan haraji da Amurka ta dauka a kan kayayyakin da take shigarwa daga kasa da kasa. Kasancewar ayaba tana girma ne a sassa masu zafi, galibin yankunan kasar Amurka ba su dace da nomansu ba. Ko a jihohin Hawaii da Florida da sauran sassan kasar Amurka da suka fi zafi ma, yawan ayabar da ake samarwa ba zai iya biyan bukatun kasuwannin Amurka ba, sabo da wasu dalilai na yanayi da kasuwanci. A hakika, a...

Jami’in Makamashin Nukiyar Iran Ya Ce; Zarge-Zargen Da Ake Yi Kan Shirin Makmashin Nukiliyar Iran Siyasa Ce Kawai
Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba. Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba. Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun...
Wannan ita ce shekara ta biyu a jere da ‘yansandan Jihar Kano na haramta hawan sallah, wanda suka ce hakan na da nasaba da tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani samame da aka kai a Mallamfatori, cikin Karamar Hukumar Abadam, sojojin sun gano ƙarin gawarwakin ‘yan ta’adda da kuma tarin makamai. Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47, babura, harsasai masu yawa, ma’ajin harsasai, bututun roka, bom na hannu, rediyon hannu da wasu kayayyakin soji. Rundunar sojin ta ce waɗannan hare-hare na baya-bayan nan na nuna ƙwazon da ake yi wajen murƙushe Boko Haram da ISWAP tare da dawo da zaman lafiya a yankin Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Fadar mulkin Rasha ” Kremlin” ta sanar da cewa; Kasar Rasha tana fadada fafagen yin aiki da kasashen Afirka da su ka hada da fagage masu muhimmanci na soja da tsaro. Kakakin fadar ta “Kremlin” Dmitry Viskov da yake amsa tambaya akan tasirin shigar Rasha cikin nahiyar Afirka, ya ce; Sannu a hankali Rasha tana kara shiga cikin nahiyar ta Afirka’ sannan kuma ya yi ishara da azamar da Rashan ta yi na ganin wannan alakar ta bunkasa tare da mayar da hankali akan tattalin arziki da kuma zuba hannun jari.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
A baya, irin wannan mummunan abu ya faru a yankin, inda sojoji da dama suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai. Hakan na ƙara nuna irin barazanar da matsalar tsaro ke ci gaba da haifarwa a Jihar Sakkwato, inda mazauna ke roƙon gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen hare-haren ‘yan ta’adda, musamman masu tayar da bama-bamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kididdigar ci gaban tattalin arzikin bangaren tekun kasar Sin, wadda take muhimmin ma’aunin duba ci gaban tattalin arzikin tekun kasar, ta karu da kashi 2.3 bisa dari a bisa mizanin shekara-shekara, inda ta koma zuwa kaso 125.2 a shekarar 2024, lamarin da ya nuna cewa an samu ci gaba mai karfi a fannin teku. Ma’aikatar albarkatun kasa ce ta fitar da wannan kididdigar a jiya Lahadi albarkacin bikin ranar teku ta duniya. Bayanai sun nuna cewa, an inganta tsarin sabbin masana’antun bangaren teku na kasar Sin a shekarar 2024, tare da samun ci gaba a fannin fasahar kere-kere. Haka nan, an samu habakar amfani da tattalin arzikin teku da inganta karamin sashen kididdigar da ake yi da kaso 131 cikin...
– Bayanan al’umma da tarihin yankin – Sahihancin hannun sarakuna da shugabannin al’umma Gwamnatin ta jaddada cewa wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin bunƙasa al’adu da ƙarfafa zaman lafiya ta hanyar inganta tsarin mulkin gargajiya. Dukkan al’ummomin da ke da ra’ayin ƙirƙirar sabon masarauta ko gunduma ana ƙarfafa su su gabatar da buƙatunsu a cikin waɗannan kayan da aka kayyade. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana, ma’aunin farashin sarrafa kaya na cikin gida, watau PPI shi ma ya ragu da kaso 3.3 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma adadin ya ragu da kaso 0.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Afrilun bana. Duk da cewa ma’aunin CPI na watan Mayu ya ragu kadan, amma farashin kayayyaki a wasu bangarori ya canza, al’amarin da ya shaida rawar da...
Tsohon gwamanan Jihar Zamfara kuma Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammed Matawalle ya bayyana cewa, kofar Jam’iyyar APC abude take idan gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal na Jamiyyar PDP na bukatar shigowa Jamiyyar. Ministan ya bayyana haka ne a Mahaifarsa Maradun a lokacin ziyar Sallah da magoya bayan Jam’iyyar APC na Kananan Hukumomi 14 suka kai masa a gidansa da ke Maradun cikin Jihar Zamfara. Matawalle ya bayyana cewa, muna jin rade-radin cewa , gwamna Dauda zai dawo Jam’iyyar APC sakamakon Jam’iyyar su ta PDP na fama da matsalar rikice-rikice. Domin yanzu haka da Sallar nan daya daga cikin gwamnonin PDP ya dawo APC A Legas. Don haka, Kofarmu a bude take ga gwamna Dauda Lawal, zuwansa APC dan bamu kyama,...
Tare da cewa giwaye suna cikin dabbobin da masu yawon bude ido suke son gani, said ai gwamantin kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yanka 50 daga cikinsu domin rabawa mutanen karkara namansu. Wannan matakin na gwamnatin Zimbabwe ya zo ne saboda yadda giwayen suke kara yawa sosai a cikin shekarun bayannan. Haka nan kuma wuraren da ake killace su, sun yi kadan. Majiyar dake kula da gandun dajin kasar ta ce; adadin giwayen ya rubanya har sau uku, wannan ne ya sa mahukuntar kasar su ka yanke shawarar yanka 50 daga cikinsu saboda a rabawa mutanen karkara. A baya gwamnatin na Zimbabwe ya yi kokarin warware matsalar karuwar dabbobin ta hanyar sauya musu gandun daji da wuraren da aka killace...

Ministan Harkokin Kiwon Lafiya Na Iran Ya Bukaci A Yawaita Sayar Da Kayakin Likita Zuwa Kasashen Waje
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fara sana’a na cikin manyan jerin kalubalen da ’ƴan Najeriya suke fuskanta sakamakon wasu dalilai wadanda suka hada da rashin ilimi, ko Rashin wanda zai ba su shawara ko kuma, uwa uba, rashin jari. Wasu bayanai da Hukumar Ƙididdiga Ta Kasa – NBS – ta fitar sun nuna cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na matasan Najeriya suna sha’awar fara sana’a, amma sun kasa saboda rashin jari. Haka kuma, wani bincike da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gudanar ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na matasa masu so su fara kasuwanci suna fuskantar babbar tangarda wajen samun jari daga bankuna ko hukumomin gwamnati. Shin ko akwai wata hanya da matasa...
Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Matawalle ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, a garinsu Maradun, yayin da dubban magoya bayansa suka kai ziyarar gaisuwar Sallah. Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000 Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce APC jam’iyya ce ta mutanen kirki da masu kishin ƙasa. Ya ce maimakon a ci gaba da takun-saka tsakanin gwamnati da ’yan adawa, zai fi kyau Gwamna Dauda ya fito fili ya rungumi jam’iyyar da ke da madafun iko domin ci gaban jihar da ƙasar gaba ɗaya....
Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Ministan Bunƙasa Harkokin Ƙarafa, Shuaibu Abubakar Audu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na samun ci gaba wajen farfaɗo da tsohon kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi. Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kogi a garinsu Ogbonicha da ke Ƙaramar Hukumar Ofu. Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka Ministan, ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da za su samar da kayan aikinkamfanin. Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙara neman masu saka hannun jari daga ƙasar China domin su zuba jari a kamfanin. “Muna yin aiki...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghae ya zargin gwamnatin Amurka da yin ba daidai ba saboda karin takunkuman tattalin arziki wanda ta dorawa kasar, wanda kuma yake nuna irin kiyayyar da takewa mutanen kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Esmael Baghae yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa bayan da hukumar baitul malin Amurka ta bayyana sunayen mutane 10 wadanda ta dorawa takunkuman tattalin arziki da kuma kamfanoni 27 mafi yawansu a hadaddiyar daulolin larabawa wato UAE. Labarin ya kara da cewa wadan nan mutane suna taimakawa Iran a ayyukan Banki da jigilar manfetur a madadin Iraniyawa. Baghae ya bayyana wannan labarin a kan kariya kuma mummunan siyasar Amurka ce...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine. Ya ce Sin na daukar amincewa da manufar kasar daya tak da Faransa ta yi da muhimmanci, kuma tana fatan ganin hakan a aikace. Bugu da kari, ministan ya...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025. A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025. Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa...

Rundunar Sojin Mamayar Isra’ila Ta Yi Furuci Da Karancin Sojoji Saboda Raguwarsu Sanadiyyar Mutuwa Ko Rashin Lafiya
Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta amince da samun tauyaya a yawan adadin sojojin mamayar Isra’ila sakamakon halakar wasu daga cikinsu Rundunar sojojin Isra’ila ta yarda cewa: Suna fama da matsanancin karancin sojoji masu yawa, a halin yanzu akwai yawan 10,000, da aka rasa kuma ana neman fiye da rabinsu a fagen gudanar da yaki, a ci gaba da gudanar da ayyukan soji a zirin Gaza. Rundunar sojin ta ce suna fuskantar karancin sojoji fiye da 10,000, ciki har da kusan 6,000 na rukunonin yaki,” wannan rashin sojojin rashi ne maim ai tsanani da ake bukatar samunsu cikin gaggawa, don haka rundunar soji take gudanar da duk matkn da suka dace don toshe wannan gurbin, in ji kakakin rundunar sojin mamayar...
Gobara ta tashi a otal ɗin Imaratus Sanan da ke birnin Makkah a ƙasar Saudiyya, inda sama da alhazan Najeriya 48 suka sauka yayin aikin Hajjin shekarar 2025. Otal ɗin yana unguwar Sharamansur a birnin Makkah. Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa dukkanin alhazan sun tsira kuma babu wanda ya ji rauni. A cewar NAHCON, hukumomin gaggawa na Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin sun gaggauta kashe wutar kafin ta bazu. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, ya ziyarci otal ɗin tare da wasu jami’an hukumar domin duba halin da ake ciki. Ya bayar da umarnin a kwashe alhazan zuwa wani sabon otal cikin gaggawa,...
Shugaban ya ci gaba da cewa, idan har zamu rage nauyin aikin da ke a kan Tashar ta Lekki, wajen biyan kudade, ya kamata ima Tashar ta san da cewa, muna da bukatar kudade da dama, domin mu sawo kayayyaki da dama na gudanar da ayyuka a Tashar, musamman domin mu tabbatar da cewa, ma’aikatan mu, na ci gaba da gudnar da ayyuakansu, a Tashar, kamar yadda ake bukata. Dantso ya kara da cewa, za a yi aiki da tsarin NSW na kasa, inda zai samar da kaso 95 a cikin dari na gudanar da ayyuka a Tashar, wanda ya jaddada cewa, hakan zai kara rubunya, kudaden shiga, ga Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar. “Gudanar da hada-hadar kudade ta hanyar yin...
Sojojin Rasha sun kai hare-hare mafi muni akan cibiyoyin soja da muhimman cibiyoyi a kasar Ukiraniya da su ka hada da birnin Kiev. Sojojin na Rasha sun yi amfani da kamamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki masu kai harin kunar bakin wake da su ka haddasa tashin gobara. Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kharikiev ya bayyana cewa; A kalla mutane 10 su ka jikkata a bisa kididdigar farko. Ita kuwa rundunar sojan saman kasar ta Ukiraniya ta sanar da cewa; an yi amfani da makamai masu linzami samfurin “Cruise” wajen kai harin. Su ma sojojin na Rasha sun sanar da cewa, sun kai wa Ukiraniya hare-hare akan sansanonin soja da kuma muhimman cibiyoyin kasar ta hanyar...
A shekarar da ta gabata, kamfanin Dangote ya biya haraji N450 biliyan – wanda ya fi dukkan bankunan Nijeriya suka hada jarin harajin da suka biya. Wannan shiri na gina hanyoyi yana cikin shirye-shiryen gwamnati na ba da rangwamen haraji domin inganta kayayyakin more rayuwa a kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Gwamnatin ta yi hakan ne, sakamakon tabbatar da ganin an fara aiki a kamfanin daga nan zuwa karshen watan Mayun shekarar 2025. “Gwamnatin Jihar da shude ce ta bai wa kamfanin kwangilar da kuma wani kamfani da ke Kasar Indiya aikin, inda gwamnatin ta zuba dala biliyan 12 a kamfanin,” in ji Hamza. Sai dai, ya bayyana cewa; saboda kasancewar wasu dalilai, ba a samu cimma wata gagarumar nasarar a zo a gani ba a kan aikin. Ya sanar da cewa, a watan da ya gabata ne, gwamnatin jihar ta sake yin nazari kan yarjeniyar ta baya da aka kulla, wadda kuma za a dawo, domin a ci gaba da yin aikin. Babban Sakaren ya kara da cewa, manyan batutuwan...
Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati. Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar...
A yau Jumma’a, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, a duk irin kalubalen da za a iya samu daga waje, masana’antun kasar Sin za su ci gaba da zama ababen nema a duniya, kuma kasuwannin kasar za su kasance a ko yaushe masu jan hankali wajen zuba jarin waje. An ba da rahoton cewa, a yanayin tangardar da tattalin arzikin kasa da kasa ke fuskanta, huldar kasuwanci da tattalin arzikin kasar Sin da sauran kasashen duniya na nan daram ko gezau. A cikin watanni biyar na farkon wannan shekara, kasar Sin ta bude hanyoyin sufurin jiragen sama na dakon kaya na kasa da kasa guda 101, kuma an kara yawan zirga-zirgar jiragen sama na...
Akalla mutane hudu ne, ciki har da wani matashi dan shekara 13, an ce an harbe su tare da fille kawunansu a ranar Alhamis a yankin Gangaran Kwata da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mazauna yankin sun ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe biyu na tsakar daren ya haifar da tashin hankali a yankin na Mangu. Sojoji sun dakile hare-haren ‘Yan Boko Haram biyu a Borno Gwamnan Akwa Ibom ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Abdullahi Maicibi, shugaban addini a yankin Kwata, ya tabbatarwa da wakilin Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce an dauki gawarwakin wadanda aka kashe zuwa babban masallacin Mangu da ke garin Mangu domin yin sallar jana’iza. Shagari Madaki, another resident, said...
Ministan harkokin wajen Faransa ya jaddada aniyar birnin Paris na amincewa da kasar Falasdinu Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya tabbatar da aniyar Faransa na amincewa da kasar Falasdinu, yana mai jaddada cewa wannan amincewa ba zai kasance na bai daya ba, sai dai a matsayin wani bangare na kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe. Hakan ya zo ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo kasa makonni biyu gabanin taron hadin gwiwa tsakanin Faransa da Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya. Barrot ya bayyana cewa, makasudin taron shi ne hada kasashe da masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da hukumar Falasdinawa da kasashen Larabawa don ciyar da shirin zaman lafiya gaba. Ya...

Adadin ‘Yan Jaridar Falasdinu Da Suka Yi Shahada Sun Karu Zuwa 226 Tun Bayan Fara Kisan Kare Dangi A Gaza
Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah. Ofishin ya bayyana cewa: Yawan ‘yan jaridan da suka yi shahada ya karu zuwa 226 tun farkon yakin kisan kare dangi kan zirin Gaza, bayan sanar da shahadar daya daga cikin ‘yan jaridan Falasdinawa: Ahmed Qaljah, wanda ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto na gidan talabijin na Al-Arabiya. Ofishin ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai hare-haren wuce...
“Yawancinmu ba mu je kasuwa ba yau saboda Sallah. Bidiyon da aka ɗora ne ya sa muka samu labarin wutar. Abin takaici, wasu shaguna da ke kusa da nawa sun ƙone,” in ji shi. Ƙoƙarin da wakilinmu ya na tuntuɓar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, bai yi nasara ba domin wayarsa ba ta shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani rahoton tsaro da hukumar Kididdiga (NBS) ta fitar a watan Disamban 2024, ta ce, yawan kudin fansa da jama’an Nijeriya suka biya ya zarce naira tiriliyan 2.23 ga masu garkuwa da mutane daga Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024. A cewar rahoton na CESPS, kusan kashi 65 cikin 100 na magidanta da suka fuskanci matsalar sace-sacen jama’a sun biya matsakaitan kudin fansa na naira miliyan 2.67, wanda ya kai naira tiriliyan 2.23. An fitar da rahoton ne kwana guda bayan rahoton hukumar kare kakkin Dan’adam na Nijeriya na shekarar 2024, ya nuna cewa akalla mutane 526 ne aka kashe a wasu munanan hare-hare tare da yin garkuwa da wasu 949 a wasu sassan kasar. Duk da masana sun sha nusar...
Domin shawo kan wannan matsalar, ministan ya zayyana kokarin da ake yi a karkashin dabarun bunkasa kiwon dabbobi na kasa, wanda ya mayar da hankali kan ginshikai guda 10 da suka hada da bunkasa kimar dabbobi, inganta kiwo, kiwon lafiyar dabbobi, samar da kudi, sauya salon kiwo da karfafawa matasa da mata gwiwa kan dogaro da kai. Maiha ya yi tunin cewa zuwa yanzu ma’aikatar ta samu cimma wasu nasarori da suka hada da yin rajistar nau’in kiwo guda takwas, “na farko a cikin shekaru 48” da kuma samar da wani shiri na kasa kan albarkatun halittun dabbobi tare da hadin gwiwar FAO. “Dabbobinmu na cikin gida suna samar da lita 1-2 na madara a kullun, idan aka kwatanta da...
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana ta Babbar Sallar. “Babbar Sallah tana bai wa Musulmi damar girmama sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi na ɗansa domin biyayya ga umarnin Allah. “Tana tunatar da mu muhimmancin imani, rashin son kai, da sadaukarwar da muke da ita ga al’umma da bil’adama, ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani a kan kimar sadaukarwa da biyayya ga Allah Maɗaukakin Sarki. “Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da duk wani nau’i na munanan ɗabi’u da kuma laifuka da suka shafi al’ummarmu. “Haƙƙinmu ne na gamayya mu yi aiki don tabbatar da tsaron al’ummarmu,...
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta labarin da ake ta yadawa cewa akwai yiwuwar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya canza mataimakinsa, Kashim Shettima gabanin zaben 2027. APC ta bakin mataimakin shugabanta na kasa na shiyya Kudu maso Gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu, ta musanta zargin inda ta ce wasu ne suka kirkire shi domin su kawar da hankalin mutane. Ijeoma ya ce, “Yanzu na fara jin labarin. Akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna tsakanin shugaba Tinubu da mataimakinsa Kashim. Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Lawal Uwais ya rasu Mun gurfanar da mutum 29 a kotu kan zargin kashe DPO a Kano – ’Yan sanda “Kashim babban jigo ne a wannan tafiya. Mutum ne mai kwakwalwa sosai, yana da alkibla kuma...
Gwamnatin kasar Saudiya ta yi amfani da fasahar kirkirarren tunani ko (AI) don sauwakawa kanta da kuma mahajjata a hajjin wannan shekara ta 2025, kama daga kula da cinkoson mutane, kiyaye lafiyar mahajjata da haka kuma ta kyautata ayyukan mahajjata a cikin nutsuwa da rashin damuwa. Jaridar ArabNews ta kasar Saudiya ta bayyana cewa tare da wannan fasahar ta kula da zafin dukkan wuraren da mahajjata zuwa zuwa da kuma hana cinkoson mutane a kewayen Kaaba da sauran wurare.. Jami’I mai kula da bangaren kirkirerren fasaha wato AI na aikin Ajjin bana ya shaidawa Jaridar ArabNews kan cewa sun kirkiro abubuwa da dama don sawwaka aikin hajji ga mahajjata da kuma khidimomin da kasar saudiyya take yiwa mahajjata, Ya ce...
“Idan za ku yi adalci a gare mu, a cikin makonni biyu da suka gabata, za ku ga cewa sojojin suna samun nasara wajen karya lagon ‘yan ta’adda, inda suka kashe su tare da tarwatsa sassaninsu,” in ji ministan. A karshen makon da ya gabata, wadanda ake zargi ‘yan ta’adda na Boko Haram sun dasa na’urorin fashewa a Unguwar Guzamala na Jihar Borno, inda suka kashe mutane tara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki wajen kai hare-hare a kan birnin Kiev da kuma wasu gundumomi 9 na kasar. Rundunar sojan saman kasar Ukiraniya ta ce; Kasar tasu ta fuskanci munanan hare-hare da makamai masu linzami a cikin gundumomin gabashi, yammaci da kuma babban birnin kasar Kiev. Rundunar soja da take tafiyar da sha’anin Mulki a birnin Kiev ta sanar da cewa; Daga cikin wuraren da aka kai wa hare-haren da akwai tashar jirgin kasa, hakan nan kuma muhimman cibiyoyi da gidajen fararen hula. Magajin birnin Vitali Klitschko ya sanar da cewa; Mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu mutane 20 su ka jikkata sanadiyyar harin na Rasha. Haka nan kuma...
Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar. An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi. Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi da kuma DRC. Shugaban kasar Zambia Hakayinde Hichilema ya bayyana cewa; Da akwai bukatar nahiyar Afirka ta fara samar da magunguna cikin gaggawa tare da dogaro da nahiyar wajen samar da kudaden da ake bukata domin yin hakan, saboda kaucewa dogaro da waje.” Haka nan kuma shugaban kasar ta Zambia ya ce: Saboda kwalara idan ta barke ba ta san iyakar kasashe ba, ya kamata...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yau mutane na kallon bukukuwan Sallah da ido daban—yayin da wasu ke ganin ta zama lokaci na shakatawa nishadi kawai, wasu kuwa na cewa an bar al’adun da ke nuna kimar wannan babban lokaci na Musuluncin. Wadanda suka manyanta na ganin akwai abubuwa da dama da a yanzu matasa sukayi watsi da su wadanda kuma na da muhimmanci yayin bukukuwan sallah a da can baya wanda kuma suke ganin ba a yin su a yanzu. Ko wadanne irin al’adu kenan na bukuwan sallah da dattawa ke ganin anyi watsi dasu. NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah...
Abdullahi ya ce, an dauko wanda ya fadan a sume amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa. Ya kara da cewa, an mika gawar marigayin ga Hakimin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i. Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki ta kai taimakon kuɗi domin tallafawa waɗanda suka tsira da masu taimaka musu. Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane da su taimakawa al’ummar garin Mokwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
A wani hari ta kasa da na sama, rundunar sojojin Operation Hadin Kai sun dakile wasu manyan hare-haren ta’addanci guda biyu a ranar Alhamis a Jihar Borno. Dakarun sun kashe da dama daga cikin maharan tare da kwato tarin makamai da alburusai. Wani mutum ya mutu a cikin rijiya a Kano Mahajjata kusan miliyan biyu na hawan Arfa a Saudiyya Rahoton da hukumar tsaron sojan Najeriya suka fitar na nuna cewar, dakarun sojan rundunar ta OPHK an kaddamar da hare-haren ne a wasu wurare daban-daban na sojoji a Buratai da ke karamar hukumar Biu da kuma Mallam Fatori da ke karamar hukumar Abadam. An bayyana cikakkun bayanan hare-haren a cikin wata sanarwa da Mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na...
Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai. Kana a bayan manufar ta kasar Sin akwai wani tunani mai muhimmanci da kasar ta rike, wato na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. A ganin kasar Sin, dukkan al’ummun kasashe daban daban suna zama a duniya daya, don haka suna da makomar bai daya. Saboda haka ya kamata a lura da bukatun sauran kasashe, da tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai daya, yayin da...
Wani matashi dan shekara 33 mai suna Muhammad Sagir ya rasa ransa bayan ya fada rijiya a unguwar Kawon Alhaji Sani da ke karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano. A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, mataimakin jami’in kashe gobara (ACFO) Saminu Yusif Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:42 na rana a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025. Tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Jibril Aminu, ya rasu Ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga wani mai suna Sabi’u Muhammed, inda ya sanar da su lamarin. “Nan da nan aka tattara tawagar ceto daga hedkwatar hukumar zuwa wurin.” “Da isowar jami’an, ma’aikatan sun gano wani mutum guda...
Mai bawa jagoran Juyin juya halin musulunci shawara kan al-amuran siyasa Ali Shamkhani ya sake tabbatar da cewa kasar Iran ba zata dakatar da aikin tace makamacin Uranium kamar yadda gwamnatin Amurka take so ba. Sannan ya kara da cewa kasar tana kokarin sake gabatar da wata shawara daban ga kasar Amurka. Ali shamkhani ya fadawa tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon a wata hira da ta hadasu a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu suna rubutun wata shawagara ga gwamnatin Amurka dangane da hakan. Shamkhani ya kara da cewa wasikar da Amurka aikawa Tehran bata ambaci batun daukewa kasar takunkuman tattalin arziki ko kadan ba. Ya kuma soki kasar ta Amurka a wasikar da...
Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya. Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an yi masa sallar Jana’iza a babban masallacin kasa a Abuja a yau Alhamis. Sannan za’a maida shi garinsa Song na jihar Adamawa inda za’a rufe shi. A rayuwarsa dai Farfesa AAmin likitan zuciya ne, sannan malami da shugaba Jami’ar Maiduri na Jahar bornin a wani lokaci, ya kuma karantar. Har’ila yau Farfesa Amin ya rike kujerar Ministan ilmi da manfetur, sannan jakadan Najeriya A Amurka...
Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun da wuri, musamman ganin yadda aka ce ta bazu zuwa ƙasusuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mahajjata aikin hajjin bana suna ci gaba da tururuwa zuwa tsayiwar Arafat a yau Alhamis Mahajjata na ci gaba da tururuwa zuwa Arafat domin gudanar da muhimmin rukunnan aikin Hajji. Mahajjata suna gudanar da ranarsu tun daga ketowar alfijir har zuwa bayan sallar isha’i a filin Arafat, bayan sun gudanar da ibadar ranar Tarwiyah, wadda mahajjaci ya yi a Mina, yana taqaita salloli ba tare da hada su ba. A safiyar rana ta goma, mahajjata za su sake komawa Mina don jifan Jamarat al-Aqaba, kafin su yi aski ko saisaye, su yanka dabbar layya, Sannan su nufi dakin Ka’aba domin yin Tawafin Hajji.
Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki Sojojin Yemen sun sanar da kai wani farmakin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma nuna tsananin Rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a zirin Gaza. Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, inda ta ce farmakin da rundunar sojin saman Yemen ta kai da jiragen saman yaki marasa matuka ciki kirar Yaffa guda biyu, ya samu nasarar cimma burin da ake bukata. Rundunar...
Abubakar ya tabbatar da cewa rundunar na da cikakken niyyar kare sararin samaniyar Nijeriya da rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan. Ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda irin goyon bayan da yake bai wa sojoji, musamman ta fannin kayan aiki da walwalar ma’aikata. A makon da ya gabata, rundunar ta kashe aƙalla ‘yan ta’adda 20 a wani samame da aka kai Garin Mani, da ke ƙaramar hukumar Maru a Jihar Zamfara. Wannan farmaki ya biyo bayan luguden wuta da aka riƙa yi wa ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka. Shugaban sojin ya ce motsa jiki abu ne da ya zama dole ga dukkanin ma’aikata, kuma babu wanda zai samu ƙarin girma ba tare da...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ce har yanzu jam’iyyar adawa mafi ƙarfi a Najeriya. Ya ce PDP tana da ƙarfi kuma za ta iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027. Barazanar Yajin Aiki: Abuja da wasu jihohi 3 za su faɗa cikin duhu A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Saraki, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu na PDP, ya faɗi haka ne a wani taro da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Ilorin. Ya amince cewa wasu sun bar jam’iyyar, amma mutane da dama suna ci gaba da shigowa jam’iyyar. “PDP ce kawai jam’iyyar adawa ta haƙiƙa,” in ji shi. “Eh, muna fuskantar ƙalubale, amma muna...
Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), sun yi barazanar shiga yajin aiki, wanda hakan zai iya jefa Abuja, Kogi, Nasarawa da Jihar Neja cikin duhu. Ma’aikatan, ƙarƙashin ƙungiyoyin NUEE da SSAEAC, sun ce kamfanin ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka bayan sun dakatar da wani yajin aiki a watan Nuwamban 2024. A shekara 25, na kashe tiriliyan 161 wajen inganta lafiya a Afirka – Bill Gates Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ƙorafe-ƙorafen nasu sun haɗa da rashin biyan kuɗin fansho na tsawon watanni 16, rashin ƙarin girma, rashin kula da lafiyar ma’aikata. Sun kuma ce an ƙi biyansu ladan aiki na shekarar 2024 duk da cewa sun taimaka wajen samar da kuɗin...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya haramtawa kasashen duniya 12 shiga Amurka a wani mataki da ya ce na kare kasar ne daga “yan ta’adda na kasashen waje. Wata takarda da fadar White House ta fitar a ranar Laraba ta ce haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni, ya shafi kasashen Afghanistan, Burma, Chadi, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Somalia, Sudan, da kuma Yemen. Baya ga hakan akwai wasu kasashe bakwai su ma da aka gindawa wasu sharudda da suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Saliyo, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela. A cewar Amurka matakin bai shafi mutanen da balaguron su zuwa kasar ke da amfani ga muradun kasar ba.” Haka ma...
Attajirin nan na duniya dan asalin kasar Amurka, Bill Gates, ya ce a shekara 25 da gidauniyarsa ta yi da kafuwa, ya kashe Dalar Amurka biliyan 100, kwatankwacin Naira tiriliyan 161 wajen inganta kiwon lafiya a nahiyar Afirka. Attajirin ya bayyana hakan ne a Legas yayin wani taro da gidauniyarsa ta Gates Foundation ta shirya mai taken Goalkeepers, ranar Laraba. Ya ce gidauniyar ta fara aiki ne a shekara ta 2000, kuma babban makasudinta shi ne ganin an rage samun mace-macen kananan yara a fadin duniya, musamman a Afirka. Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Mayar Da Unguwa Mayanka Ke Shafar Lafiyar Al’umma Bill Gates ya ce, “Ganin...
Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Belarus Aleksandr Lukashenko a nan birnin Beijing. Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya sake taya takwaran nasa na Belarus Aleksandr Lukashenko murnar nasarar yin tazarce. Xi ya ce, Sin na daukar huldar sassan biyu da muhimmanci, kuma tana raya ta bisa hangen nesa kan manyan tsare-tsare, tare da fatan kara hadin gwiwa da Belarus, don gaggauta bunkasa huldarsu, da ma cimma moriya tare cikin hadin gwiwa. Ya kara da cewa, dole ne kasashen biyu su kara hadin kai, da marawa juna baya karkashin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da MDD da SCO da sauransu, don taka rawarsu tare wajen dakile babakere, da kiyaye...

Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Amurka wacce ta bude cibiyoyin rarraba kayakin Agaji a Gaza, ta ce zata rufe cibiyoyin zuwa ranar Alhamis mai zuwa don sake tsara ayyukan Rabomn. Majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda sojojin yahudawan suna kashe falasdinawa wadanda suke fama da yunwa a lokacinda suka iso cibiyoyin raba abincin ko kuma suka hau kan hanyar zuwa karban abincin. Labarin ya kara da cewa a jiya Talata kadai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa mayunwata 27 a kokarinsu na karban abinci. Sannan a yau Laraba ya zuwa lokacin bada wannan labarin sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 32 a hare-haren da suka kai kan yankuna daban-daban a Gaza. Majiyar ta kara da cewa Palasdinawa 95 ne...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hizbullah dangane ce wacce ta shafi yankin kudancin Asiya gaba daya. A nashi bangaren shugaban kungiyar Hizbullah sheikh Naem Kassem ya godewa JMI ta irin tallafin da take bayarwa ga kungiyoyi da kasashen kawancen masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka hada da Falasdinawa da Lebanon da sauransu. Aragchi ya kara da cewa Iran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon a...
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta jaddada haramcin gudanar da hawan Durbar na shagulgulan Babbar Sallah. Wannan sanarwar na cikin wata takarda da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Sanarwar ta bayyana cewa an sanya wannan doka ne bisa rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu na shirin amfani da hawan Durbar domin tayar da hankali da barazana ga tsaro da doka a jihar. Rundunar ta taba sanya irin wannan haramci a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama da suka gabata, kuma an yanke shawarar ci gaba da dokar har zuwa Sallah Babba. Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ɗauki...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke Unguwar Mu’azu, inda manyan masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi, musamman shugabannin addini da na al’umma, suka halarta. Da yake jawabi a wajen taron, Ko’odinetan ROOSC a Jihar Kaduna, Mr. Ezra Angai, ya bayyana cewa wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da abokan ci gaba da kuma kungiyoyin aiwatar da shirin, domin inganta samun ilimi mai nagarta ga yaran da ba...

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Amurka Da Isra’ila Suna Da Mugun Nufi Kan Iran Da Kasashen Musulmi
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suna da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi. A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar Imam Khumaini {r.a}, Pezeshkian ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya aikata wani aiki hauka da wauta ba, idan kasashen musulmi suka hada kansu. Pezeshkian ya kara da cewa: Wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama suna kare “haramtacciyar kasar Isra’ila” mai laifi, kuma suna ci gaba da adawa da shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Ya ci gaba da cewa: “Babu mutum...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2. Hari ya gudana daidai inda aka tsara shi, kuma ya haifar da firgici da ya kai ga miliyoyin yahudawan sahayoniyya gudu tare da shigewa maboyar karkashin kasa kamar burage. Har ila yau, harin ya dakatar da dukkan ayyukan filin jirgin, tare da hana wani jirgin dakon kaya na sojan Amurka sauka a filin jirgin sama na Ben Gurium a rana ta biyu a jere. A cikin wannan yanayi ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake...
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”. Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...

Karuwar Darajar Sana’ar Samar Da Kayan Laturoni Da Dangoginsu a Sin Cikin Watanni 4 Na Farkon Bana Ya Karu Da 11.3%
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata kotun kasar Mali ta kori karar da aka shigar a gabata, don neman soke matakin da majalisar soj0jin kasar ta dauka na rusa jam’iyyun siyasa gaba daya. A ranar 13 ga watan Mayu ne da ya gabata ne majalsiar koli ta sojojin kasar Mali ta fitar da dokar haramta dukkan jam’iyyun siyasa a kasar wadanda yawansu ya kai 300, tare da manusar sake fasalinsu. Wasu lauyoyi da kuma ‘yan siyasar kasar ne dai su ka shigar da karar a gaban kotu, daga cikinsu har da ‘Montagal Tal’ wanda ya kasance jagoran daya daga cikin jam’iyyun da aka majalisar sojojin ta soke. Masu shigar da karar, sun bayyana matakin da majalisar sojan kasar ta dauka da cewa keta hurumin ‘yancin...

Guardian: Isra’ila Tana Kai Wa Makarantun Dake Dauke Da ‘Yan Gudun Hijira a gaza Hari, Tana Sane Da Hakan
Jaridar Guardian ta ta kasar Birtaniya ta bada labarin cewa, Hare-haren da sojojin HKI su ka kai kan wata makaranta, inda yan gudun hijira Falasdinawa suke samun mafaka da gangan suka yi shi, suna sane, kuma a halin yanzu suna Shirin kai wa wasu makarantun guda 4 hare-hare nan gaba. Jaridar ta kara da cewa: Isra’ila ta ayyana wasu Karin makarantu wadanda Falasdinawa suke samun mafaka a cikinsu domin kai musu hare-hare a nan gaba. A lokacinda HKI ta kasa ganin mayakan Hamas a fili sojojinta sun koma kan kissan Falasdinawa fararen hula, wadanda suke samun mafaka a makarantu. A cikin watanni da suka gabata sojojin mamayar sun kai hare-hare akan wasu gine-ginen 6 wadanda suka kasance makarantu ne, wadanda...
A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN. Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan. Sanarwar ta jaddada cewa, da zarar an fitar da kudaden, dole ne a aiwatar da duk wasu bukatu da kungiyar ta JUSUN ta gabatar ba tare da bata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Yau Talata, kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman watanni 4 na farko na bana, wadanda suka nuna cewa, a watan Afrilu, sha’anin jigilar kayayyaki ya bayyana inganci da boyayyen karfi, kuma duk da kalubaloli da matsin lamba daga ketare da aka fuskanta, ya tafi yadda ya kamata tare da samun bunkasuwa. Kana daga watan Janairu zuwa na Afrilu, darajar hajojin da aka yi jigilarsu a kasar ta kai dalar Amurka triliyan 16, wadda ta karu da kashi 5.6 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci a bara. Kazalika, yawan hajojin da aka yi jigila yana cikin wani yanayi mai dorewa, bisa la’akari da yadda jigilar kayayyaki ta amfani da layin dogo da...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, yace nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu cikin shekaru biyu kadai shaida ce ta shugabanci mai hangen nesa da jaruntaka. Ya bayyana haka ne a yayin taron farko na National Dialogue on Citizen Engagement and National Security da aka gudanar a Abuja, mai taken “One Voice, One Vision: Uniting Perspectives for a Stronger Nigeria.” A cewar Ministan, wannan taro ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke kokari yi amfani da damamaki da ke gabanta. Ya jaddada cewa wannan dandali da Voice of Nigeria (VON) ta shirya ba kawai taron tattaunawa kan manufofi bane, sai dai wata kafa ce da aka tanada domin hada ra’ayoyi da...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na...