2025-06-03@03:16:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4392
«da gwamnati»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk jarirai 1000, yayin da na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu zuwa yara 5.6 cikin duk yara 1,000, adadin da ya yi kasa sosai cikin jerin kasashen duniya, dake rukunin masu al’ummun dake sama-sama a matsakaicin samun kudin shiga. Shen Haiping ta kara da cewa, idan aka nazarci wadannan alkaluma, za a ga cewa cikin sama da shekaru goma da suka gabata,...
Rahotanni daga kasar ta DRC sun ambaci cewa an ga tsohon shugaban kasar Joseph Kabila a jiya Alhamis a garin Goma wanda yake a karkashin ikon ‘yan tawayen kungiyar M23. Majiyar malaman addinin kirista a yankin ce ta sanar da cewa, ta gayyace shi ne domin ya shiga Tsakani a kawo karshen yakin da ake yi a yankin. Bishop Joel Amurani ne ya sanar da cewa, su ne su ka gayyaci tsohon shugaban kasar wanda ya kasance akan karagar Mulki daga 2001 zuwa 2019. A yayin ziyarar tashi a garin na Goma, Kabila ya gana da bangarori mabanbanta da su ka hada da malaman addinin yankin. A can birnin Kinshasha, gwamnatin Felix Tshisekedi tana zargin Kabila da cewa yana goyon...
Mamakon ruwan sama da ya sauka a jihar Rivers ta Najeriya ya yi gyara, tare da daukar rayukan mutane 25,kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta kasar ta sanar. Ruwan da ya sauka a garin Okrika ya haddasa zaizayar kasa,wacce ta binne gidaje da dama, da kuma yin awon gaba da mutane. Masu ayyukan ceto sun ce har yanzu ana ci gaba da gano gawawwakin mutane a karkashin baraguzai. Haka nan kuma mutane da dama sun rasa matsugunansu. Duk da cewa ana ci gaba da ayyukan ceto said ai har yanzu da akwai yankuna da ba za a iya shiga cikinsu ba saboda sun yi lungu.
MDD ta yi gargadi akan yunuwar da mutanen Gaza suke fama da ita, sannan ta kara da cewa: Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji, kuma rabin cibiyoyin kiwon lafiya na yankin sun daina aiki saboda rashin isar da kayan agaji daga waje.” Ofishin MDD wanda yake kula da ayyukan agaji ne ya yi wannan gargadin, sannan ya kara da cewa: Yankin Gaza shi ne wurin da aka fi fama da yunwa a duniya baki daya.” Mai Magana da yawun ofishin na MDD ya ce: da akwai manyan motoci 600 da suke dauke da kayan agaji da su ka isa kan iyakar Gaza, amma asalinsu 900 ne da bisa wasu dalilai an hana su isa bakin iyaka.” Haka nan kuma...
Da yake jawabi ga ɗimbin mutanen da suka halarci wannan tattaki, Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kawar da duk wani nau’in miyagun laifuka a jihar, tare da mai da hankali sosai kan ‘yan bindiga. Ya ce, “A yau mun fito dubunnan mu domin mu yi tattakin samun zaman lafiya, domin mu sanar da duniya cewa Zamfara ta samu ci gaba sosai ta fuskar tsaro. “Gwamnatina ta ba da himma da kayan aiki masu yawa don ƙarfafa sojoji, tattara bayanan sirri, da haɗa kai don dawo da zaman lafiya a jihar. “Mun sami gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga, yawancin wuraren da ake fama da rikici a baya, a halin yanzu sun kasance cikin kwanciyar...
Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar, sun nuna daga watan Janairu zuwa watan Afirilun bana, masana’antun samar da manhajoji da ayyukan ba da hidimomin fasahohin sadarwa na Sin sun bunkasa lami lafiya. Alkaluman sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa watan Afrilun bana, jimillar kudin shiga da masana’antar ta samu, ta haura yuan tiriliyan 4.25, adadin da ya karu da kaso 10.8 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara. Kazalika, jimillar ribar masana’antar manhajojin ta kai yuan biliyan 507.5, yayin da saurin karuwar jimillar ribar masana’antun ta yawaita zuwa kashi 14.2 bisa dari. Har ila yau, jimillar kudin shigar masana’antun fitar da kayayyakin manhajojin ta kai dalar Amurka biliyan 17.26, adadin...
Kwararran likita tiyata, Farfesa Sani Ali Aji ya bayyana cewa kwarrun likitocin tiyata guda 6 ne kacal suka rage a Jihar Kano, wanda ake has ashen tana da al’umma fiye da miliyan 20. Farfesa Sani ya kara da cewa wannan karanci na likitoci ya faru ne sakamakon karancin albashi, karanci kayan aiki na zamani da sauransu, wanda hakan ya sa kwararrun likitoci suka koma kasashen Turai da na Larabawa domin samun alfashi mai tsoka. ‘Yansanda Sun Kama Mutane 41 Da Ake Zargi Da Kisan DPO A Kano Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kano Ya bayyana cewa maganin wadannan matsaloli shi ne, samar da kayan aiki wadatace da albashi ga ma’aikata mai tsoka da sauransu. Farfesa Sani...
A bikin cikarsa shekaru 6 cur yana mulkin Jihar Yobe, Gwamnan jihar Mai Mala Buni da aka gudanar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu akan harkokin ilimi da noma, inda ya ce akasarin waɗanda suka amfana a waɗannan fannoni guda biyu matasa ne. Da yake jawabi a yayin wannan taro na bikin cikarsa shekaru 6 akan mulki da aka gudanar a babban ɗakin taro na Banquet da ke gidan gwamnatin Jihar a garin Damaturu tare da ma su ruwa da tsaki na Jihar. An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA Gwamnan ya bayyana ƙudirinsa na ci...
A bikin cikarsa shekaru 6 cur yana mulkin Jihar Yobe, Gwamnan jihar Mai Mala Buni da aka gudanar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ya bayyana irin gagarumin ci gaban da aka samu akan harkokin ilimi da noma, inda ya ce akasarin waɗanda suka amfana a waɗannan fannoni guda biyu matasa ne. Da yake jawabi a yayin wannan taro na bikin cikarsa shekaru 6 akan mulki da aka gudanar a babban ɗakin taro na Banquet da ke gidan gwamnatin Jihar a garin Damaturu tare da ma su ruwa da tsaki na Jihar. An gano gawar direba a cikin mota a Bayelsa Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA Gwamnan ya bayyana ƙudirinsa na ci...
An gano gawar wani direban da yake tuƙi ƙarƙashin kamfanin sufuri da har yanzu ba a tantance shi ba a yankin Samphino na Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa. Daily Trust ta ruwaito cewa, an gano gawar direban matashin mai matsakaicin shekaru da sanyin safiyar Juma’a a cikin motarsa a mahaɗar Samphino da ke unguwar Kpansia a unguwar Yenagoa. Mutanen da suka mutu a ambaliyar Neja sun ƙaru zuwa 88 —NSEMA Faransa ta haramta shan sigari a cikin jama’a Wasu shaidun gani da ido da mazauna wurin da suka gano mutumin a wurin, an bayyana cewa, sun sanarwa da jami’an tsaro lamarin inda suka yi gaggawar ɗaukar mataki a wajen tare da killace wurin. Mazauna yankin sun ce mai yiwuwa wasu...
Yawan mutanen da suka rasu a sakamakon mummunar ambaliyar ruwan sama a yankin Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ya ƙaru zuwa 88. Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Husseini Isah, ne ya sanar da haka a ranar Juma’a. Ya ce, “adadin mamatan na ci gaba da ƙaruwa, amma a halin yanzu mun ƙirga mutum 88.” Hussain Ya ƙara da cewa ana ci gaba aikin ceto. Aminiya ta ruwaito cewa wasu mutum 12 ’yan gida ɗaya suna cikin mutanen da ambaliyar ta yi ajalinsu. NAJERIYA A YAU: Yaya Girman Matsalar Rashin Tsaro A Shekaru Biyun Tinubu? Faransa ta haramta shan sigari a cikin jama’a Ambaliyar ta yi rusa da gidaje sama da 50...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin akidar Jamhuriyar Musulunci ta Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da haƙƙin da doka ta tanada ba ta fannin inganta sinadarin uranium, domin inganta harkar kiwon lafiya, aikin gona da masana’antu, yana mai jaddada cewa: makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin koyarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin ziyarar da ya kai masarautar Oman, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata hira da gidan talabijin na kasar, ya yi bayani kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da kuma muradun yankin da na kasa da kasa na Iran da Oman, da kuma muhimman batutuwan...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Hanyar Warware Takaddamar Shirin Makamashin Nukiliyar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan hasashe game da kusancin cimma yarjejeniyar nukiliyar da ke gudanarwa tsakanin Amurka da Iran Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hanyar diflomasiyya tana bukatar a dage dukkan takunkumai da aka kakabawa Iran da kuma mutunta hakkin mallakar makamashin nukiliyar Iran, yana mai cewa: Hanyar cimma yarjejeniya ta ta’allaka ne ta kan teburin tattaunawa, ba ta hanyar kafafen yada labarai ba. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya fada a jiya Alhamis cewa: Kafafen yada labarai na yada jita-jita game da yarjejeniyar da ake shirin kullawa tsakanin Iran da Amurka. Araqchi ya ci gaba da yin tsokaci a shafinsa na Twitter a dandalin Twitter, inda ya ce: “Muna shakkar...
Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi. Ya jaddada cewa, “tattaunawa hanya ce ta ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba kayan aiki na tilastawa ko mika wuya ba.” Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan. Ya...
A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa. Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin...
PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da yankin Gaa-Odota da ke Ilorin da kuma yankin Ganmo da Amoyo na jihar. “Kamen da aka yi a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya alakanta wadanda ake zargin da ayyukan damfara ta Intanet a jihar. Sanarwar ta kara da cewa, “Kayan da aka kwato daga hannunsu da aka kama sun hada da manyan motocin alfarma...
Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan (in ji Ja’afarus Sadik) sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa. Amma saboda kankancinsa duk lokacin da ya jefa shi a kafada sai ya fado alhali kuma ga babban mayafinsa a rataye a kantarsa. Sai ya yi mana sallah. Bayan gamawa na tambaye shi ya ba ni labarin Hajjin da Annabi (SAW) ya yi na karshe. Sai (Jabir) ya yi ishara da hannunsa tare da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin tsaro na cikin matsalolin da suke ci gaba da ci wa ’yan Najeriya da dama tuwo a kwarya, har a wannan lokaci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yake cika shekara biyu a kan mulki. Wasu rahotanni da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka fitar dai sun koka da yadda suke ganin matsalar ta kara kamari a wadannan shekarun. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan matsala ta rashin tsaro. Domin sauke shirin, latsa...
Wani masanin tattalin arziki, Ademola Adigun, ya ce, duk da janye tallafin mai, sashin mai a Nijeriya ba ya tafiya kan ka’ida. Ya yi bayanin cewa kawai an rage biyan tallafin ne amma ba wai an daina biya gaba daya ba, kuma babu gasa tsakanin ‘yan kasuwa wanda shi ma na haifar da nakasu. Adigun ya soki tsarin sayar da danyen mai a kan kudin naira domin zabar da masu saye, ta yadda za a samar da lamari kamar na ‘ya’yan mowa da bora, da ke iya korar ‘yan kasuwa masu zaman kansu, lamarin da ya tilasta wa kusan gidajen mai 5,000 rufewa. Adigun, duk da ya nuna farin ciki kan yadda masu zuba hannun jari suke nuna sha’awar zuba...
A wannan zango na shekaru biyun Tinubu, ma’aikatar yada labarai ta kasa; ita ce ginshikin aiwatar da wadannan dabaru da tsare-tsare, musamman ta fuskar sake fasalin hukumomi, aikewa da sakwannin jan kunne da ladabtarwa da kuma jin ra’ayoyin daidaikun mutane, wanda hakan ya bai wa gwamnatin damar sanin matsalolin ‘yan kasa da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su. Tunda farko, ma’aikatar karkashin jagorancin ministanta, Alhaji Mohammed Idris, ta yi kokarin aiwatar da aikin da ta sanya gaba; ta hanyar nuna babu sani babu sabo ga ma’aikatun gwamnatin da suka keta doka da oda baki-daya, domin kuwa haka ma’aikatar ta kasa zaune, ta kasa tsaye wajen bibiyar ‘yan Nijeriya a wureran ayyuka da sauran wuraren zamansu, don jin...
Sulhu da ‘Yan Bindiga Ya Fi Zubar Da Jinin Ɗan Adam A Kaduna – Uba Sani Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Kazalika, wasu kwararrun, sun ayyna larurar, a matsayin cieon da ke yiawa mutane, kisan mummuke, musamman duba da cewa, bata nuna wasu alamu, idan an kamu da ita, sai dai kawai, ta ci gaba da zama barzana ga lafiyar ‘yan Adam, kamar kamuwa da masu larorin da suka hada da; mutuwar barin Jiki, lalata Koda da kuma rashin iya gani. An kiyasta cewa, a daukacin fadin duniya, sama da mutane, biliyan 1.3 ke fama da ciwon, wanda kuma rabin adadin wannan alkaluman ne kacal, aka yi masu gwaji aka...
Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ta afka wa yankin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja a ranar Laraba. Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na Laraba, ta kuma lalata dukiyoyi da dama, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace. Garin Mokwa dai ya shahara da zama wani zango na direbobin manyan motoci, wanda hakan ya sa garin ya zama daya daga cikin mafiya hada-hadar mutane a jihar ta Neja. NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ambaliyar ruwa ta kashe sama da...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da mutum biyu da Gwamna Uba Sani ya aike da sunayen su a tantance su a matsayin Kwamishinoni. A cikin wata wasika da Gwamna Uba Sani ya aikawa Majalisar Dokokin, ya bukaci a amince da Farfesa Abubakar Sani Sambo a matsayin Kwamishinan Ilimin sai kuma Barrister Gloria Ibrahim a matsayin Kwamishinar Matasa da cigaban jihar. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, RT. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya bukaci sabbin kwamishinonin da aka amince da su, su yi amfani da kwarewar su domin farfado da bangaren Ilimi da bunkasa ci gaban matasa. Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan tantancewa da amincewa da shi a matsayin Kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo ya...
“Ina isar da wannan sakon ba wai a matsayina na tsohon shugaban kasa ba, har ma a matsayina na dan jihar Ogun cike da alfahari, na kasance tare da ku a lokacin bikin bude gasar, na kalli wasannin a cikin dakina, kuma hakika wasannin sun nuna cewa ba wai kawai wasanni ba ne, alama ce ta hadin kai, baje kolin hazaka, da kuma kishin kasa. “Daga karshe Obasanjo ya jinjinawa jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya, da kuma kananan kungiyoyin da aka gayyata bisa jajircewarsu, inda ya kara da cewa, kwamitocin da suka shirya gasar, abokan hadin gwiwa, da masu aikin sa kai na hukumar wasanni ta kasa sun cancanci a yaba musu saboda mayar da wannan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce, ta kama mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan DPO ɗin Rano, CSP Baba Ali. Rundunar ta bayyana lamarin, wanda ya janyo kace-nace, a matsayin harin kai tsaye kan sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi, waɗanda suke sadaukar rayuwarsu domin kare al’umma. NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 NDLEA ta kama maniyyata aikin hajji ɗauke da hodar iblis A wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Alhamis, ya ce rundunar ’yan sanda na aiki tuƙuru domin ganin an gurfanar da duk waɗanda ke da hannu wajen kisan, da kuma masu alaƙa da ƙone-ƙone. Sanarwar ta ƙara da cewa, “Rundunar ta...
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Da yake jawabi ga manema labarai a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja kafin jirgin maniyyatan ya tashi zuwa Saudiyya, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce aikin Hajjin bana ya samu nasarori da dama da suka nuna ci gaba da inganta aikin hajjin Nijeriya. NDLEA ta kama maniyyata aikin hajji ɗauke da hodar iblis ’Yan bindiga sun kashe makiyaya 2, sun sace shanu 320 a Kaduna Ya ce, an yi jigilar maniyyata 41,568 ta jiragen sama 105. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ya nuna matuƙar godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed...
Kasar Brazil ta jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya A yayin ganawarsa da sakataren kwamitin kolin tsaron kasar Iran, mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil ya sanar da cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da makamashin nukiliya na zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin inganta sinadarin Uranium don bunkasa harkokin ilimi cikin gida ta hanyar fasahar makamashin nukiliya. A yayin ganawar tasu, Ali Akbar Ahmadian, sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran, da mataimaki na musamman ga shugaban kasar Brazil Celso Amorim, sun jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da tuntubar juna tsakanin kasashen biyu masu cin gashin...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Suna gudanar da kyakkyawar tattaunawa da Iran Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa: Amurka na tattaunawa da Iran sosai kan Shirin makamashin nukiliyarta. Donald Trump ya fada a ranar Laraba cewa: “Ya damu da abin da ke faruwa a Ukraine, kuma bai sani ba ko Putin na son kawo karshen yakin,” a cewar gidan talabijin na Al Jazeera. Dangane da tattaunawar da aka yi da Iran, Trump ya ce: “Suna tattaunawa mai kyau da Iran.” Trump ya ce: Dole ne bangarorin Gaza su amince da takardar da Steve Witkoff wakilin Amurka na musamman a yankin Gabas ta Tsakiya ya gabatar.

Falasdinawa 23 Suka Yi Shahada A Farmakin Da Sojojin Mamayar Isra’ila Suka Kai Kan Sansanin Al-Bureij
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin Zirin Gaza Falasdinawa fararen hula 23 ne suka shahada tare da jikkata wani adadi masu yawa a wani sabon kisan kiyashi da sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila suka yi a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke kudancin zirin Gaza. Rahotonni sun bayyana cewa: sojojin mamayar sun kai hare-hare ne ta hanyar jiragen saman kan gidajen jama’a, ciki har da gidan iyalan Al-Qarnawi da ke gabashin sansanin. Haka hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar wani Bafalasdine a yankin Qizan al-Najjar da ke kudancin Khan Yunus. Sannan jami’an ceto sun gano gawar wani Bafalasdine a wani gidan da aka...
Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC. Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a...
Fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da jiragen yaki mara matuki suka kai kan birnin Kordofan na kasar Sudan Kafofin yada labarai na cikin gidan kasar Sudan sun rawaito cewa: Akalla fararen hula 10 ne suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan jihohin Yamma da Kudancin Kordofan. Shafin yanar gizo na Sudan Tribune ya watsa rahoto cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun zafafa kai hare-hare ta sama a garuruwa da biranen yankin Kordofan tun farkon wannan wata. Yankin dai ya sha fama da tashe tashen hankula tsakanin bangarorin da ke gaba da juna, inda kungiyar Rapid Support Forces ke...
Ambaliyar dai, ta afku ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama yana sauka a daren Laraba. Wani mazaunin garin, Mohammed Usman ya ce tuni aka fara tsamo gawarwaki da dama a cikin ruwan, amma wasu da dama ba a iya ganin su ba musamman a wuraren da gidaje suka nutse. Daraktan yada labarai da ayyuka na musamman a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Dakta Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban Hukumar da ke yaƙi da shan miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Janar Buba Marwa (mai ritaya), a ranar Laraba, ya bayyana kamen wasu mutum biyu da suka yi yunƙurin safarar hodar Iblis a lokacin da ake jigilar maniyyata aikin hajji a kan hanyarsu ta zuwa ƙasar Saudiyya don gudanar da Hajjin bana. Da yake jawabi a wajen buɗe taron kwamitin kula da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Abuja, Marwa ya bayyana cewa, waɗanda ake zargin sun haɗiyi miyagun ƙwayoyin ne, inda suka nuna cewa su Musulmi ne masu kishin addini da suke shirin gudanar da aikin hajji. ’Yan bindiga sun kashe makiyaya 2, sun sace shanu 320 a Kaduna Ɗalibai sun maƙale lokacin da gini ya rufta suna...

Sin Da Kasashen Yankin Pasifik Sun Yi Nasarar Gudanar Da Taron Ministocin Harkokin Wajen Karo Na Uku
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da shugaban kasar Kiribati, kuma ministan harkokin wajen kasar Taneti Maamau, sun jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashen yankin Pasifik karo na uku a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin. A yayin taron, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda shida kan kafa kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin Pasifik. Na farko shi ne dagewa kan mutunta juna. Ya ce kasar Sin tana goyon bayan kasashen yankin wajen kiyaye cikakken ’yancinsu, tsaro da muradunsu na ci gaban. Kuma Sin ta yi imanin cewa, kasashen yankin za su ci gaba da bin manufar kasancewar kasar...
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake dasuwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmaci a makon da ya gabata, wanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamnatakewa tsaro da sauransu. Inda muka yi masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin. ///…Masu sauraro shirimmu na yau zai yi magana dangane da zaben majalisun dukoki na kasa da kuma larduna a kudancin kasar Lebanon inda kungiyar Hizbullah da kuma Amal ta mabiyan mazhabar iyalan gidan manzon All..suka fi rinjaye. Inda zamu ga yadda Hizbullah ta lashe dukkan bazabun da yakamata ta lashe haka ma...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce tun da ya hau kujerar mulki shekaru biyu da suka wuce ko kwabo bai ciyo ba a matsayin bashi. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wasu ’yan jaridu a Kaduna ranar Alhamis, albarkacin cikarsa shekaru biyu a mulki. A cewar Gwamnan, bankuna da dama sun tunkare shi suna neman ya ci bashi amma ya ki saboda ba ya so ya ci gaba da dilmiyar da jihar a kangin bashi. Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su Gwamnan ya ce a maimakon haka, ya ma rage kudaden alawus-alawus na Sakataren Gwamnatin jihar da...
Daga baya, hukumar WAEC ta fitar da sanarwa tana mai bada hakuri, inda ta ce wasu ƙalubale ne suka hana isar da kayayyakin jarrabawa akan lokaci. Wannan lamari ba sabon abu ba ne, domin a watan Afrilu, LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu masu rubuta jarrabawar UTME sun bar gida da asuba domin isa cibiyoyin jarrabawa kafin ƙarfe 6:30 na safe, ba tare da wadataccen tsaro ko sufuri ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutanen da ya zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba sun rasa rayukansu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afka wa garin Mokwa na jihar Neja. Mazauna yankin sun kuma ce babbar hanyar da ta hada arewaci da kudancin Najeriya da ta bi ta yankin ita ma ambaliyar ta yanke ta. Kodayake dai har yanzu babu cikakkun bayanai a kan ambaliyar, amma mazauna yankin sun kiyasta cewa mutanen da suka rasa ransu za su kai 50. NEJERIYA A YAU: Sai Yaushe ’Yan Najeriya Za Su Ci Gajiyar Manufofin Shugaba Tinubu? ’Yar Najeriya ta tsinci miliyan 8.2 a Saudiyya ta mayar wa da mai su Gidaje da sauran kadarori na miliyoyin nairori ne dai suka salwanta, yayin da wasu...
Shima a nasa jawabin Janar Martin Luther Agwai cewa ya yi, “Aikin wanzar da zaman lafiya na daya daga cikin muhimman aikin Majalisar Dinkin Duniya da ake iya gani, inda sama da sojoji 87,000 ke sanye da rigar wanzar da zaman lafiya da farar hula suka taka rawa a cikin wasu ayyuka 12, daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo zuwa Lebanon, daga Sudan zuwa Mali. Nijeriya kuma na wakiltar ayyuka guda 8.” Wadannan jajirtattun maza da mata suna taimakawa wajen daidaita yankuna, ba wa fararen hula kariya, tallafawa tsagaita wuta, da sake gina da amana inda ta lalace. Mahimmanci lamari shi ne, tun lokacin da aka kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta farko a shekara ta 1948,...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ya gana da ministan harkokin cikin gida da kuma gwamnonin Larduna, inda ya basu shawarar amfanin da kekyawar yanayin da kasar take ciki don ciyar da kasar Gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana cewa, a halin yanzu kasar Iran bata fuskantan watai annoba kamar CoviD19, ko matsalar tsaro a cikin gida da sauran wanda zai hanasu aiki. Ko kuma yake bukatar kudade masu yawa don warwaresu. Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa kasar Iran a halin yanzu bata fuskantar wata matsala, don haka ya bukaci Gwamnonin lardun su yi amfani da wannan damar don amfani da matasan kasar wadanda suka yi karatu don bukasa...
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kuma kawayenta a wajen kungiyar sun gudanar da taro a birnin Riyad na kasar Saudia inda suka tattauna kan yawan man fetur da zasu haka daga shekara da ta 2027. Shafin yada labarai na tanar gizo na kasar Saudia Arab News ya bayyana cewa wannan yana daga cikin abinda kasashe suka amince a bayan kuma a halin yanzu kungiyar ta rika ta tsara yawan man da ko wace kasa zata haka daga shekara ta 2022 har zuwa shekara ta 2026. Labarin ya kara da cewa kungiyar tana da tsare tsaren haka man fetur har guda uku biyu suna tafiya kamar yadda suka tsara a yayinda daya kuma sun warewa kasashe 8 daga cikinsu...
Kasashen kungiyar ‘ the Association of Southeast Asian Nations’ ko ASEAN ta yi allawadai da kisan kiyashiun da ke faruwa a zirin gaza, sannan ta bukaci kasashen duniya su dauki matakan da suka dace don dawo da doka da oda na kasar Falasdinu da aka mamaye, a kuma kawo karshen kisan kiyashin da ke faruwa a can. Har;ila yau kungiyar ta bukaci a bude kofofin shiga gaza don isarda abinci da magunguna zuwa zirin gaba sannan a daina kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. A wata sanarwan da da kungiyar ta bayar tace a dakatar da kashe fararen hula a dukkan bangarorin sannan ta bukaci a maida aikin hukumar UNURWA na MDD don isar da agaji a cikin...
Jihar Gombe ta rattaba hannu kan kwangilar sama da biliyan 48 don aikin kula da Makarantar ‘yan mata ta Mega dake Doma da kuma zaizayar kasa Baya ga sanya hannu kan kwangilar, an kuma bayar da cak don biyan diyya ga mazauna yankin mai nisan mita 10 da ke kan hanyar aikin. Da yake jawabi a wurin rattaba hannu kan kwangilar a hukumance a Hayin Missau Bogo, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana matakin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da muhallin Gombe da kuma kare makomar jama’a. A cewarsa aikin ba wai kawai zai shawo kan zaizayar kasa ba ne zai dawo da fata ga al’ummomin da abin ya shafa. Alh. Inuwa Yahaya wanda ya...
A ranar 23 ga Mayu, 2025, jam’iyyar APC ta bayyana Tinubu a hukumance a matsayin dan takararta guda daya tilo don zaben 2027, duk da fuskantar sauyin ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban. Buhari ya jinjina wa kokarin Tinubu wajen rage talauci da hauhawar farashin kayayyaki, yana mai kira ga fannoni masu zaman kansu da daukacin ‘yan ƙasa da su ba da gudunmawarsu. Ya kammala da cewa: “Ina taya Shugaba Tinubu murnar cikar shekaru biyu a ofishi. Allah ya ci gaba da ba ka hikima da tausayi wajen jagoranci. Mu kuma mu rage tsammaninmu daga gwamnati.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
A wani lamari mai ban al’ajabi, a daren jiya dalibai a jihar Taraba sun zana jarrabawar kammala karatunsu na Ingilishi na WAEC da karfe 8:25 na dare, sama da sa’o’i 12 da fara sa’o’i 8:00 na safe. Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa jinkirin ya haifar da rudani da damuwa a tsakanin iyaye da masu kula da su, wadanda ke nuna shakku kan dalilan dage jarabawar da ba a taba ganin irinsa ba. Lamarin dai ya yi matukar tayar da hankali idan aka yi la’akari da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a yankin. Ba tare da wani bayani a hukumance daga WAEC ba, dalibai da iyaye suna mamakin abin da ya jawo tsaikon da kuma...
Majalisar dokokin jihar Nasarawa, ta umurci gwamnatin jihar da ta cire sabbin malamai 1000 wadanda ke karbar albashinsu daga aikin tantance malaman da ake yi a jihar. Mataimakin kakakin majalisar Muhammad Adamu Oyanki, ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake karanta kudurin majalisar bayan Daniel Ogazi ya kawo lamarin cikin gaggawa ga al’umma yayin zaman majalisar a lafiya. Mohammed Adamu Oyanki ya ce malamai 1000 da ke karbar albashin na aiki ne bisa ka’idojin aikin gwamnati don haka ya kamata a cire su daga aikin tantancewar da ake yi a jihar domin samar da zaman lafiya, hadin kai da adalci. Ya kuma umurci mashawarcin da ke gudanar da aikin tantancewar da ya mayar da wasikun...
A wani babban ci gaba na kawo sauyi a tsarin kiwon lafiyar Najeriya, gwamnatin tarayya ta yi ta kaddamar da ayyuka 16 a asibitin masu tabin hankali na gwamnatin tarayya dake Kware a jihar Sokoto. Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar, Ministan Kasa a ma’aikatar Lafiya da walwalar jama’a, Dokta Iziak Salako, ya jaddada cewa ayyukan na daga cikin ajandar sabuwar fata ta gwamnati shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na kasa. Ya ce FG ta himmatu wajen samar wa asibitoci kayayyakin more rayuwa, kayan aiki da kudade, da tallafi don inganta ayyukan hidima a fadin kasar. Dakta Salako ya ci gaba da bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta samar da muhimman ayyuka...
A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki ya kai wani harin a unguwar “Shuja’iyya” wnada ya yi sanadin shahadar mutum daya, sai kuma wasu shahidan 4 a unguwar “Shari’u 5”, da kuma wasu shahidan 4 a garin “Bani-Suhaila”. Wasu rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a garin ‘Abasan al-kabira’ da ya yi sanadin shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu masu yawa. A yankin Qizan kuwa, ‘yan sahayoniyar sun...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Harin da “Isra’ila” ta kai wa filin saukar jiragen saman Sanaa, manufarsa ita ce yin matsin lamba akan matsayarmu ta taimakawa al’ummar Falasdinu da ake zalunta.” Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kara da cewa; Komai girman hare-haren da Isra’ilan za ta kai ba zai yi tasiri akan matsayarmu ta taimakawa Gaza ba,sannan kuma ya kara da cewa; Abinda Isra’ila makiya ke son yi, shi ne a kyale ta yi yadda take so da Falasdinawa ba tare da an mayar mata da martani ba daga kowace kasa ta musulmi.” Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma ce; Matsayar da kasar Yemen take dauka na taimakawa Falasdinawa, matsaya ce ta addini.” Haka...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya sanar a marecen jiya Laraba cewa, Iran za ta iya dakatar da tace sanadarin Uranium a karkashin yarjejniyar da za a iya kullawa da Amurka. Kakakin ma’ikatar harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Dr. Baka’i ya yi watsi da labarin da kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya watsa na yiyuwar dakatar da tace sanadarin “Uranium’ yana mai kara da cewa; zai ci gaba babu kakkautawa, kuma ba abinda za ma za a yi tayi ba.” Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato Baka’i yana cewa; labarin na Reuters, ba komai ba ne sai farfaganda ake maimaitawa, da kuma an sha kore gaskiyarta. Kamfanin dillancin labarun na “Reuters’ kamar yadda...
Jaridar Vadiot Ahranot ta HKI ta buga labarin dake cewa; Shugaban kasar Chile Gabriel Boric ya bayar da umarni a janye jami’an diplomasiyyarsa kasarsa masu kula da alakar soja daga ofishin jakadancin kasar tasa a Tel Aviv. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Chile ta wallafa wani sako a shafinta na “Internet” cewa; Ofishin jakadancin nata ya sanar da mahukunta wannan haramtacciyar cewa sun janye jami’an diplomasiyyar biyu. Kasar ta Chile ta bayyana dalilinta na yin haka da cewa, shi ne yanayin da mutane Gaza suke ciki ta fuskar jin kai ta tabarbarewar harkokin rayuwa saboda yakin da Isra’ila take yi. Haka nan kuma kin amincewar “Isra’ila” da a shigar da kayan agaji cikin yankin na zirin Gaza. Ita dai kasar...
Daya daga cikin maniyyata Aikin Hajjin bana daga jihar Filato mai suna Hajiya Zainab ta mayar wa da wani dan kasar Rasha kudinsa da ta tsinta a birnin Makka na kasar Saudiyya, har kimanin Naira miliyan takwas da dubu 200. Rahotanni sun nuna matar ta tsinci guzirin maniyyacin ne a Masallacin Harami na Makka a ranar Talata . Ta tsinci kudin ne da yawansu ya kai Dala dubu biyar, kimanin miliyan takwas da dubu 200 a Naira, idan aka canza a kan farashin N1,648 a kan kowacce Dala daya. Babu wanda ya tayar da bam a Abuja —Wike Kotu ta yanke wa Murja Kunya hukuncin dauri a gidan yari Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da kuma Shugaban...
Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya ce rahotannin da ya samu na nuna babu gaskiya a labarin da ake yaɗawa cewa mai ƙunar baƙin wake ne ya tada abu mai fashewa a barikin soji na Mogadishu da ke Abuja. Wike ya bayyana hakan ne ga manema labarai, lokacin da ya kai ziyarar duba aikin titunan da za a ƙaddamar domin bikin cikar shugaba Tinubu biyu a kan karagar mulki. Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162 Ministan ya kuma ja hankalin ’yan jarida kan yaɗa labaran da ka iya jefa firgici a zuƙatan al’umma. Aminiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a shingen bincike na barikin sojin Mogadishu, kuma...
Babbbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke wa fitacciyar ’yar Tiktok, Murja Ibrahim wacce aka fi sani da Murja Kunya hukunicn daurin watanni shida a kurkuku. Alƙalin kotun Mai Shari’a Simon Amobida ya kuma ba wa Murja zabin biyan tarar Naira dubu 50. Ya ce saboda yawan mabiyanta a shafinta na Tiktok, an nada ta jakadiyar EFCC da Babban Bankin Najeriya (CBN) wajen wayar da kan mutane kan illar wulakanta Naira a dokar Najeriya. Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Born Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162 EFCC ce dai ta maka Murja a kotun, bisa zarginta da wulakanta Naira, bayan bullar wani bidiyo da ta ɗauka tana rawa tana yi wa kanta liƙi...
A cikin wani mataki na ci gaba da sauya fasalin bangarorin noma da kiwo, Gwamnatin Jihar Jigawa na shirin kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanonin kiwon kaji na kasar Indiya, wato Srinivasa Farms. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Jigawa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar. Ya ce a wani bangare na ziyarar zuba jari a fannin noma da gwamnatin jihar ke gudanarwa zuwa kasar Indiya, tawagar jihar karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi ta kai ziyara ofishin babban kamfanin Srinivasa Farms dake birnin Hyderabad domin tattauna damar hadin gwiwa da nufin farfado da harkar kiwon kaji a Jigawa. Hamisu Mohammed Gumel ya kara da cewa...
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin ta ce kamfanoni mallakin gwamnatin kasar, sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata cikin watanni hudu na farkon shekarar nan ta 2025, inda jimillar kudaden shigarsu ta ci gaba da karuwa bisa daidaito a shekara guda. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, sun nuna tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu, jimillar kudaden gudanarwa na wadannan kamfanoni ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 26.276, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.65, adadin da ya nuna daidaito matuka idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2024. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Kunngiyar Tarayyar Turai, ta ce ba ta gamsu da sabon tsaron raba kayan agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke shirin aiwatarwa a Gaza. Babbar jami’ar diflomasiyyar kungiyar, Kaja Kallas, ta bayyana cewa Tarayyar Turai ba ta goyon bayan sabon tsarin raba agajin jin kai da Amurka da Isra’ila ke kokarin aiwatarwa wanda ke kaucewa hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji. Kallas, ta kuma bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza sun wuce abun da suke bukata wajen yakar Hamas, a yayin da adadin wadanda suka rasa rayukansu ke ci gaba da karuwa. Tun bayan da Isra’ila ta dawo da yaki a watan Maris bayan ruguza yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma...
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da dage takunkumin da ta kakaba wa wasu manyan jami’an gwamnatin Zimbabwe. Birtaniya ta ce ta yi hakan ne domin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyar ta bayyana cewa za ta dage takunkumin da ke kan mutum hudu da kuma kamfanin kera makamai mallakar gwamnati a Zimbabwe. Wannan matakin ya zo watanni bayan Tarayyar Turai ita ma ta sassauta nata takunkumin kan Zimbabwe. Birtaniya ta saka takunkumin ne a lokacin saboda damuwa da abinda ta kira take hakkin dan Adam da aka rika samu a kasar ta Zimbabwe.
Gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump ta umarci ofisoshin jakadancinta da ke faɗin duniya su dakatar da bai wa dalibai da sauran mutane da ke neman bizar ziyara zuwa kasar. Gwamnatin ta ba da umarnin ne yayin da take fadada shirin binciken bada bisa ta hanyar tantance abubuwan da mutum ke wallafawa a shafukan sada zumunta, musamma dalibai. Wasu daliban kuma da tuni suke Amurka an kwace bizarsu saboda shiga gangamin nuna goyon-bayan Falasdinawa. Wannan na daga cikin matakan da Trump ke dauka na hana manyan makarantun Amurka da suka yi fice wajen dogaro da kudaden makaranta da suke samu daga daliban ketare. Kafin wannan lokaci fadar gwamnatin Amurka White House ta ce gwamnatin Trump ta bukaci dukkanin ma’aikatun Amurka su...
Ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ba za ta amince da duk wata tattaunawa kan dakatar da shirinta na inganta makamashin Uranium gaba daya ba. Ya bayyana hakan ne a gefen ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Oman, inda ya jaddada cewa, bai kamata tattaunawa da Amurka za ta hada da batun ba wanda Tehran ba za a amince da shi ba. Araghchi ya ce, ana ci gaba da tattaunawa da Amurka, amma batun tace uranium shi ne ya kasance babban abin da ake samun sabani. Ya kuma kara da cewa, an yi shawarwari da ministan harkokin wajen Oman game da shirya wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da Amurka. Ministan ya...
A nasu jawabin, kwamishinonin kudi da kasafin kudi Misis Augustina Wandamiya da Mista Emanuel Pridimso sun bayyana cewa, an yi bitar kasafin ne da nufin gano wuraren da aka samu rarar kudi da kuma tabbatar da cewa, an kashe kudin kasafin shekarar 2024 a inda ya dace. Sun kara da cewa, jihar ta kula da tsari wajen aiwatar da kasafin kudi, tare da tabbatar da gaskiya, wanda hakan, ya taimaka wajen samar da kyakkyawan aiki a ayyukan raya jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
A jiya Talata ne aka fitar da sanarwar hadin gwiwa ta taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Sanarwar ta ce bangarorin uku sun amince hulda, da mu’amalar al’adu, da kuma hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da Sin, da kuma kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC na da dogon tarihi, don aka ana fatan kara inganta dangantakar sassan uku karkashin jagorancin ka’idoji, da ra’ayoyi, da manufofi, da alkawuran da aka cimma matsaya daya kan su, ciki har da tsarin dokokin MDD. A cikin sanarwar, an kuma yabawa kasar Sin, bisa muhimmiyar gudummawa da take bayarwa wajen inganta zaman lafiya,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Uba Sani ya amsa da cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 100 cikin watanni shida don magance matsalar ƙarancin ruwa a faɗin jihar, tare da alƙawarin cewa za a maye gurbin dukkan kayan aikin da suka lalace. Ya ƙara da cewa an riga an kashe sama da Naira miliyan 400 wajen gyara da maye gurbin bututun ruwa da aka lalata, kuma kafin ƙarshen shekara Kaduna za ta fara samun ruwa ba tare da katsewa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun sojojin Najeriya sun dakile wani harin hadin gwiwa da ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Marte da ke jihar Borno, inda suka kashe wasu da dama daga cikin maharan. Majiyar leken asirin hedikwatar sojan Najeriya ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin karfe 1:35 na wayewar safiyar talata 27 ga watan Mayu. Majiyar ta ce wasu ’yan ta’adda da ba a tabbatar da adadin su ba sun kai hari a bataliya ta 50 da ke Marte. Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900 Tinubu ya ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya ta Kabo Zuwa Jami’ar Fasaha ta Tarayya Dakarun da ke samun goyon bayan wata tawaga ta runduna ta 24 da bataliya ta...
Majiyoyin labarai a kasar Yemen sun bayyana cewa HKI ta kai hare-hare a kan tashar Jiragen sama a birnin San’aa inda a wannan karon suka lalata hanyar tashin jiragen sama a tashar. Tashar talabijan ta Al-manar ta kasar Lebanon ta kanalto majiyar HKI tana tabbatar da wannan labarin. Tashar radio ta HKI ta nakalto ministan yakin HKI Yasra’il Katz yana tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hare-haren ta sama sun wargaza wani bangare na tashar jiragen sama na birnin, sannan ya lalata jirgin sama tilo wanda ya rage a tasahr jiragen. Hakama tasha ta 12 ta HKI ta nakalto Katz yana cewa jiragen yaki fiye da 10 ne suka yi aikin hare-hare a kan tashar jirage na...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi ya tir da kalaman jakadan Burtaniya a Washington, Peter Mandelson, wanda yayi kira ga Amurka kada ta taba barin Iran ta tashe makamashin Uranium a cikin kasar. Ministan ya kara da cewa Mandelson yana son ya karkatar da tattaunawan da Iran take da Amurka. Ya kuma kara da cewa Iran ce take sanar da kasashen turai yadda tattaunawa tsakanin Amurka da ita ke tafiya, tun Amurka ta waresu daga tattaunawar. Yace, idan har haka ne tunanin kasar Burtaniya wacce take cikin kasashen da suka sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu, yana ganin mai yuwa Iran ta dakatar da sanar da su abubuwan da ke tafiya a tattaunawar. Ya zuwa zagaye har 5 wadanda Amurka da...
Majiyar kungiyoyin bada taimakon gaggawa a Gaza sun bayyana cewa ya zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Laraba, sojojin yahudawan Sahyoniyya sun kashe akalla mutane 16. Shafin labarai na Arab News ta kasar Saudia ya nakalto Mahmud Bassal kakakin wata kungiyar bada agaji na Gaza yana cewa da misalign karfe biyun dare jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan gidan Osama Al-arbeed dan jarida mai daukar hotuna a gidansa da ke arewacin Gaza, inda harin ya raunata Osman Arbeed sannan ya kashe wasu daga cikin yan gidansa. Har’ila yau wasu mutane 6 sun kai ga shahada a yayinda wasu 15 suka ji rauni daga ciki har da yara kanana, a garin Khan Yunus a safiyar yau Laraba. A lokacin...
A wani wasa da masana ke ganin zai matuƙar ƙayatarwa a gasar kofin Unity, yau Laraba za a buga wasa tsakanin manyan ƙasashen Afrika biyu Nijeriya da Ghana, ba kawai wasan ƙwallon ƙafa bane yau, kare mutunci, da ɗaukaka martabar ƙasa da kuma ramuwar gayya duk suka haɗe a wasan da za a buga a filin wasa na Gtech dake birnin Landan. Babu kanwar lasa a cikin ƙasashen biyu in dai batu ake na taka leda a nahiyar Afrika duba da cewa dukkansu sun lashe manyan kofuna na cikin gida kuma sun nuna abinda zasu iya a fagen ƙwallon ƙafa a Duniya, Ghana ta lashe gasar AFCON ta ƙasashen Afrika sau huɗu a tarihi yayin da Nijeriya ta lashe sau...
Falasdinawa da dama ne suka ji rauni a jiya Talata a lokacinda yahudawan Sahyoniyya suka bude rumbunajiyar kayakin abinda ga Falasdinawa a garin Rafah na kudancin gaza. Shafin yanar gizo na Afirka News ya bayyana cewa dubban Falasdinawa wadanda suka yi kwanaki 90 basu sami abinci ba saboda rufe kofar shiar da abinci zuwa gaza. Wannan dai yana daga cikin walakanci mafi girma wanda sojojin HKI suka yiwa Falasdinawa a Gaza, tun bayan fara yakin. An kiyasta cewa falasdinawa kimani dubu 180 ne suka fito don karban agajin HKI da Amurka. Sannan jiragen yakin HKI sun yi barin wuta a sama don tsorata falasdinawa masu neman agaji. A yayinda sojojin yahudawa suna harbi a sama don tsoratar da su. Duk...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Idan har Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta neman sake ciyo sabon bashi, jimillar bashin da ake bin Najeriya a yanzu zai koma Naira tiriliyan 162. A ranar Talata ce shugaban ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman ta sahale masa ya ciyo bashin, wacce shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya karanta a zauren majalisar. Abbas ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi. Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje Kotu ta ci su...
Kungiyar kare hakkin bil’aama ta “Amnesty International” ta bayyana cewa; mai yiyuwa ne kungiyar ‘yan tawaye ta m23 da kuma sojojin gwamnatin DRC sun aikata laifukan yaki. A wani rahoto da aka buga a jiya Talata, kungiyar kare hakkin bil’adam ta ce; Kungiyar M23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta kashe mutane da dama, da kuma azabtar da su bayan da ta tsare su. Kungiyar ta M23 ta kwace iko da yankin gabashin kasar mai cike da albarkatun karkashin kasa da su ka hada Bukavu da Goma. Tare da cewa an kulla yarjejeniya a tsakanin M23 da gwamnatin DRC sai dai kuma har yanzu suna ci gaba da fada.
Gwamnatin kasar Ireland ta yi doka a jiya Talata wacce ta hana a shigar da duk wasu kaya da aka kera a matsugunan ‘yan share wuri zauna da a karkashin dokokin kasa da kasa ake daukarsu a matsayin haramtattu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Ireland ya fada wa kamfanin dillancin labaurn Faransa cewa; Gwamnati ta amince da a ci gaba da yin wasu dokokin da hana mu’amalar kasuwanci da matsugunan ‘yan share wuri zauna da ba su bisa doka, domin an yi su ne akan kasar Falasdinawa.” Daga cikin kayayyakin da Majalisar dokokin ta Ireland ta haramta, da akwai ‘ya’yan marmari da itatuwa. Ministan harkokin wajen Ireland Simon Harris ya fada wa ‘yan jarida cewa, yana fatan ganin...
Sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na yankin zirin Gaza da su ka hada da sansanonin ‘yan hijira da kuma rusa gidajen da su ka saura a tsaye. Tashar talabijin din ‘almayadin” ta bayyana cewa; An sami shahidai 7 da safiyar yau Laraba, bayan harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai akan wani gida da yake a Deir-Balah,dake tsakiyar zirin Gaza. A can sansanin ‘yan hijira dake kusa da filin wasa na ‘al-Anan’ kuwa mutane 4 ne su ka jikkata. A yankin Safdawi dake cikin birnin Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan wani gida wanda ya haddasa gobara, da kuma shahadar mutane 8. A unguwar “Shuja’iyya” sojojin na mamaya sun rushe gidaje da...

Arakci: Idan Birtaniya Ta Ci Gaba Da Batun Dakatar Da Tace Uranium A Iran, Za A Dakatar Da Tattaunawa Da Ita
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Akaci ya bayyana cewa; Idan har kasar Birtaniya tana ci gaba a kiran Iran ta dakatar da tace sanadarin uranium a cikin kasarta, to kuwa Iran din za ta yanke tattaunawar da take yi da ita. Ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran ya rubuta a shaifnsa na hanyar sadarwa ta jama’a cewa: Iran ta tuntubi Birtaniya ne da kyakkyawar manufa,haka nan sauran kasashen turai da aka yi yarjejeniyar Nukiliya da su, duk da cewa, Amurka ba ta son su shiga cikin tattaunawar.” Arakci ya kuma ce; Idan har matsayar Birtaniya shi ne ta ga an daina tace sanadarin uranium baki daya a cikin Iran, wanda hakan keta yarjejeniyar da ita kanta tana...
Rhotanni daga jihar ta Beneu sun ce a wani hari da makiyaya su ka kai a yankin Gwe ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42. Mahukunta a yankin sun sanar da cewa; an gano gawawwakin mutane 32 da aka kashe sanadiyyar harin da aka kai kauyukan Ahume da Aodona, yayin da aka gano wasu gawawwakin mutane 10 a kauyukan Tyolaha, Tse-Ubiam, kamar yadda shugaban karamar hukuma Gwer ta yamma Victor Omnin ya bayyana. Shugaban karamar hukumar ya bayyana wa ‘yan jarida abinda ya faru da cewa; na takaici ne, domin a wannan lokacin da muke Magana ana ci gaba da gano gawawwaki.” Jahar Benue tana tsakiyar kasar Nigeria ne a yankin da ake kira : Middle-Belt”. An kuma dauki shekaru masu...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo. Wannan cibiyar ilimi, wacce aka kafa a shekarar 2022, yanzu ta zama jami’a ta uku ta gwamnatin tarayya a jihar, bayan Jami’ar Bayero Kano da kuma Jami’ar Ilimi ta Tarayya da aka assasa a kwanan nan, wacce aka sanya wa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule. Matashi ya shiga hannun ’yan sanda kan kisan matar aure a Kano Tinubu zai ciyo bashin Naira tiriliyan 39 daga kasashen waje Kano na kuma da jami’o’o’i biyu mallakin gwamnatin jiha. Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da damuwa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin al’ada, saboda rashin kayan tsafta, ruwa da kuma tsaftatattun ban daki. Irin wannan matsala na addaban mata marasa galihu da wadanda ke zama a karkara. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA...

Sin Za Ta Kara Zurfafa Dunkule Rawar Yankunan Raya Tattalin Arziki Da Fasahohi A Fannin Janyo Jarin Waje
Mataimakin ministan ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin Ling Ji, ya ce gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa dunkule rawar da yankunan raya tattalin arziki da fasahohi mallakin gwamnati ke takawa, a fannin janyo jarin waje, a gabar da kasar ke kara fadada matakanta na bude kofa ga kasashen waje. Ling Ji, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin wani taron manema labarai da ya gudana, ya ce a halin yanzu yanayin hada-hadar tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa na cikin wani halin ha’ula’i, kuma sakamakon haka, matsayar yankunan raya tattalin arziki da fasahohi na muhimmin jigon daidaita hada-hadar cinikayyar waje, da zuba jari na kara bayyana a fili. Ya zuwa shekarar 2024, adadin irin wadannan...
Da yake magana da tashar talabijin ta ON Sports, Salah ya ce “Zan daina wasa ne kawai idan na fara jin gajiya a jikina”, “Idan ka tambaye ni ra’ayi na, ina tsammanin zan iya taka leda har zuwa shekaru 39 zuwa 40 amma idan na ji ina so in daina, zan daina, na samu abubuwa da yawa a harkar kwallon kafa”, inji Salah wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Firimiya Lig ta bana. Salah ya ci wa Liverpool da Chelsea kwallaye 186 a gasar firimiya kuma ya na matsayi na biyar a jerin wadanda suka fi kowa zura kwallo a raga inda kwallo daya kacal ta rage ya cimma tsohon dan wasan Newcastle da Manchester United Andrew Cole,...
Shuganan Kasa Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Wakilai takardar neman amincewarta domin ya ciyo bashin jimillar kudi Naira tiriliyan 39 daga kasasahen waje domin aiwatar da wasu ayyuka. A wasiku ukun da ya aike wa majalisar, wadanda shugabanta, Abbas Tajudeen, ya karanta a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan majalisa domin ciyo bashin daga kasashen waje a shekarar 2025–2026. Ya ce rancen na 2025–2026, ya kunshi Dala biliyan 21.5 (kimanin Naira tiriliyan 34) da Yuro biliyan 2.2 (kimanin Naira tiriliyan 3.96) da Yen na Japan biliyan 15 (kimanin Naira biliyan 164.7) da kuma Yuro miliyan 65 (kimanin Naira biliyan 116.79) a matsayin tallafi. Yana kuma neman cin bashin cikin gida ta hanyar bayar da takardun lamuni na...

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Nuna Misali Na Bude Kofa Da Raya Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da ASEAN Da GCC
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga aiwatar da matakai da za su zamo misali na bude kofa, da raya hadin gwiwa, da dunkule mabanbantan wayewar kai tsakanin Sin da ASEAN da GCC. Li Qiang, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, cikin jawabinsa ga bikin kaddamar da dandalin Sin da ASEAN da GCC, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Li, ya kuma yi kira ga sassan uku da su samar da wani salo na yin komai a bude tsakanin shiyyoyi, duba da cewa adadin al’ummunsu, da darajar tattalin arzikin da suke da shi ya kai rubu’in na duniya baki daya. Don haka dinkewar kasuwannin sassan 3, zai samar da babban fage na...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Ce: Dole Ne A Dauki Kwararan Matakan Don Dakatar Da Laifukan Gaza
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a dauki kwararan matakai don dakatar da laifukan da ake yi a Gaza A yayin ganawarsa da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif da tawagarsa a yammacin yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada wajabcin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da inganci tsakanin kasashen Iran da Pakistan domin dakile laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a Gaza. A farkon taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana matsayin Pakistan na musamman a duniyar Musulunci, inda ya bayyana jin dadinsa da kawo karshen yakin da ake yi tsakanin Pakistan da Indiya, tare da bayyana fatansa na warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu ta hanyar lumana. Haka...
Kafin tashinsa zuwa kasar Oman shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna neman kyakkyawar dangantaka da maƙwabtansu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar kafin ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Tehran zuwa birnin Muscat a yammacin yau Talata cewa: Makasudin ziyarar tasa zuwa kasar Oman ita ce kulla kyakkyawar alaka da kasashe makwabta, kuma alaka tsakaninsu tana bunkasa kowace rana. Shugaba Pezeshkian da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Mehrabad ya bayyana cewa: A halin yanzu yawan ciniki tsakanin Iran da Oman ya kai dalar Amurka biliyan 2.3, yana mai jaddada bukatar ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shugaba Pezeshkian ya ce: Zai gudanar...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Cewa: Ba Zata Taba Amincewa Da Batun Dakatar Da Sarrafa Uranium Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba za ta daina sarrafa sinadarin Uranium a kowane hali ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar a wata hira da tashar CNN ta Amurka cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da hakkinta na tace sinadarin Uranium a kowane hali ba. A yayin da yake mayar da martani game da kyakkyawan fata na shugaban Amurka Donald Trump game da shawarwarin nukiliyar da aka yi tsakanin gwamnatinsa da Iran da kuma yadda yake kallon ci gaban da aka cimma, Baqa’i ya ce: Idan manufar Amurka ita ce tabbatar da cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ba zata yi amfani da shi wajen karfin soji ba, to yana ganin...
Mijinta mai suna Ibrahim Mohammed ne ya gano ta, inda aka garzaya da ita asibiti, daga bisani aka tabbatar da mutuwarta. “Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya amince da haurawa cikin gidan matar, inda ya shake ta, sannan ya daba mata wuka a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarta. Sanarwar ta kara da cewa “Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gujewar da Trump ta yi daga yakin Yemen ya harzuka mahukuntan gwamnatin Isra’ila da kasashen Larabawa da suka dogara da shi Shafin Jaridar Hill ta Amurka ta buga wani sabon labarin da ke bayyana irin kayen da Amurka ta sha a Yemen da kuma irin dimbin hasarar da Amurkan ta yi domin kare yahudawan sahayoniyya kafin ficewa daga kangin matakin martanin kasar Yemen. Labarin da Imran Khaled ya rubuta mai taken “(Al’ummar Yemen) sun yi tsayin daka da kuma ja da baya da Trump ya yi… Shin Amurka za ta fice daga Yemen?”, yarjejeniyar “dakatar da kai hare-haren wuce gona da irin Amurka kan Yemen” ta bayyana yadda Amurka ta yin watsi da kawayenta cikin sauki, wanda ke nufin gwamnatin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron kasa karo na tara na kungiyar yara jagorori na kasar Sin (CYP), wanda aka bude a yau Talata a birnin Beijing. Xi ya jaddada muhimmancin ganin kungiyar ta bi sawun jam’iyyr kwaminis ta kasar Sin a da kuma yaye hazikai masu gina kasa da za su raya hanyar gurguzu mai sigogin kasar Sin. A game da bikin ranar yara ta duniya da za a yi a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, ya taya musu shiryawa murna a madadin kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ya mika sakon gaisuwa ga dimbin yara jagororin, da masu dora su a kan hanya, da bangarensu na...
An kammala gasar fada tsakanin mutum-mutumin inji cikin jerin gasannin mutum-mutumin inji ta kasa da kasa a ran 25 ga watan nan da muke ciki a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Gasar ta fada tsakanin mutum-mutumin inji da aka yi a wannan karo, ita ce irinta ta farko a duniya, inda kuma ta zama wani dandali dake yi wa masu kallo a daukacin duniya karin haske game da kimiya da fasaha a wannan bangare. An watsa gasar ga masu kallo na cikin gidan kasar Sin da ketare kai tsaye, matakin da ya ba su damar sanin gajiyar da ake ci daga kimiya da fasaha. CMG ta gabatarwa al’ummun duniya wata dama mai kyau ta fahimtar kimiyyar mutum-mutumin inji...
Hukumomin Kasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Zulhajji a ranar Talata, wanda ke nuna cewa ranar Laraba 28 ga Mayu, 2025, ita ce 1 ga watan Zulhajji, 1446 Bayan Hijira. Hakan yana nufin Alhzai za su yi Tsayuwar Arfa ranar Alhamis, a yi Babbar Sallah ranar Juma’a na mako mai zuwaa yi
’Yan sanda sun kama babban wanda ake zargi da kisan wata matar aure masi shekaru 22 a gidanta da ke unguwar Tsamiyar Duhuwa da ke yankin Farawa a Jihar Kano. A ranar 6 ga watan Afrilu ne aka tsinci gawar matar mai suna Rumaisa Haruna, ne a gidanta bayan an yi mata kisan gilla. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar kama wanda ake zargin mai shekaru 35 mazaunin unguwar Madatai ne a ranar 23 ga watan Mayu ta hanyar binciken sirri. Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin a hannun ’yan sanda, inda ya bayyana cewa ya shiga gidan wadda aka kashe ne ya shake ta, sa’annan ya soka mata wuka a wuya, lamarin...
Tinubu ya bayyana cewa, rancen da ake shirin amsowa na da matukar muhimmanci, domin dakile mummuman tasirin da cire tallafin man fetur ya yi akan tattalin arzikin kasar. Tinubu ya kara da cewa, za a yi amfani da wadannan kudade ne zuwa muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa, da shirye-shiryen ci gaban kasa baki daya a fadin jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tabbas a halin yanzu, wasu kasashe ba su ba da’a muhimmanci ba, kana suna ta daukar matakan kashin kai yadda suka ga dama, lamarin da ya sa al’amuran kasa da kasa suka shiga rudani. Dangane da wannan batu, dole ne Sin da kasashen Afirka masu da’a su karfafa hadin kai, su yi adawa da siyasar nuna fin karfi, da daukaka ra’ayin cudanyar mabambantan bangarori masu fada-a-ji a duniya, da kare tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Ta la’akari da yadda adadin yawan al’ummar Sin da Afirka ya kai kashi daya bisa uku na yawan al’ummar duniya, kokarin hadin gwiwarmu tabbas zai karkata duniya zuwa ga turba mai dacewa. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan dari da hamsin da ɗaya da dubu dari takwas da sittin da uku (N151,863,895.97) domin sake gina wani masallaci da wani matashi ya cinna wa wuta a yayin da jama’a ke tsaka da sallar Asuba a cikin jam’i a Tiga Gadan da ke Karamar Hukumar Gezawa, a watan Mayun bara. Aikin sabunta masallacin ya kunshi gina makarantar Islamiyya tare da ofis da bandaki da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da tankin ruwa na sama. Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya sanar amincewar sake gina masallacin ya biyo bayan alkawarin da Gwamna Abba Kabir ya yi a lokacin da ya...