Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa
Published: 17th, September 2025 GMT
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai tsawaita wa’adin shugabancin kasar daga shekaru biyar zuwa bakwai da kuma baiwa shugaban kasar damar ci gaba da mulki na tsawon wa’adi maras iyaka.
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar Litinin da kuri’u 171, yayin da aka kada kuri’a daya tilo da taki amincewa da hakan.
A ranar 13 ga watan Oktoba ne aka shirya kada kuri’ar karshe a majalisar dattawa, a cewar sanarwar da shugaban majalisar Ali Koloto Chaimi ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Sannan kuma shugaban kasar zai sanya hannu kan kundin tsarin mulkin sannan ya zama doka.
Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya karbi mulkin kasar ne bayan kisan mahaifinsa tsohon shugaba Idriss Deby, a lokacin da ya ziyarci sojojin da ke yaki da mayakan ‘yan tawaye a arewacin kasar a shekarar 2021.
Deby ya yi ikirarin samun nasara bayan zaben da aka gudanar bayan shekaru uku na mulkin soja a watan Mayun 2024, sannan kuma aka gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a watan Disamba, wanda ya bai wa jam’iyya mai mulki rinjayen kujeru.
An samu cece-kuce game da sakamakon zaben, bayan da madugun ‘yan adawa kuma firaministan kasar Succe Massara ya yi ikirarin samun nasara, ikirarin da hukumar zaben kasar ta yi watsi da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Ana ci gaba da bin hanyar diflomasiyya ko da a ƙarƙashin fada ce amma ba za a yi tattaunawa a ƙarƙashin umarni ba
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar a ranar Laraba cewa: Hanyar diflomasiyya za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga Iran, ko da a lokutan mawuyacin hali. Duk da haka, ya jaddada cewa Iran ba za ta yi tattauna da wani maƙiyi mai wuce gona da iri da mai daukar matakin ƙarfi ba, ta hanyar nuna tashin hankali da barazana ba.
Jawabin Araqchi ya zo ne a lokacin da ya halarci zaman taron kan tattaunawar kasa ta Azerbaijan, mai taken “Diflomasiyya ita ce Ingancin Hanyar da Iran ta Amince da ita,” wanda aka gudanar a birnin Tabriz. Ya lura cewa diflomasiyyar Iran na ci gaba da dogaro da gadon tarihi na muhimman ƙa’idodi da sassauci a cikin hanyoyi, kuma ya yi kira da a farfaɗo da rawar da diflomasiyyar gida ke takawa a yankunan biranen arewa da arewa maso yammacin Iran.
Araqchi ya jaddada cewa: Diflomasiyya na nan a fage har ma a lokutan yaƙi, yana mai nuni da cewa manufar Ma’aikatar Harkokin Waje ita ce kare haɗin kan ƙasar Iran, da albarkatun kasa da kuma ‘yancin ƙasar, ikon mallakar ƙasa da kuma muradun jama’arta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci