Aminiya:
2025-11-03@03:57:26 GMT

Trump ya buƙaci ƙasashen NATO su daina cinikin man fetur da Rasha

Published: 14th, September 2025 GMT

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya buƙaci ƙasashen da ke cikin ƙungiyar tsaro ta NATO da su dakatar da cinikin mai da Rasha tare da sanya takunkumi, kafin Amurka ita ma ta bi sahu da irin nata takunkuman.

Trump ya wallafa wannan bayani a shafinsa na Truth Social, wanda ya bayyana a matsayin wasiƙa ga dukkanin mambobin NATO da ma duniya baki ɗaya.

Mun kori Falasɗinawa sama da dubu 250 daga Gaza — Isra’ila ’Yan rakiyar amarya 19 sun mutu a hatsarin mota a Zamfara

Shugaban Amurkan ya ce ƙasarsa a shirye take ta sanya gagarumin takunkumi ga Rasha kan yaƙinta da Ukraine muddin ƙasashen NATO suka fara sanya irin nasu takunkumin da kuma dakatar da sayen mai na ƙasar.

“A shirye nake da in sanya manyan takunkumi kan Rasha, muddin dukkan ƙasashen NATO suka amince, kuma suka fara ɗaukar irin wannan mataki, da kuma lokacin da dukkan ƙasashen NATO suka daina sayen man fetur daga Rasha.”

Baya ga haka, Trump ya buƙaci mambobin ƙungiyar ƙasashen da ke yankin tekun Atlantika, su yi la’akari da ɗora harajin kashi 50 zuwa kashi 100 a kan China, a matsayin hanyar da za ta taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin Rasha a Ukraine.

Trump ya sha yi wa Rasha barazanar ƙarin takunkumi — ciki har da wanda ya sanar a ƙarshen makon da ya gabata bayan da Kremlin ta ƙaddamar da hare-hare ta sama mafi girma a kan Ukraine, amma har yanzu bai ɗauki wani mataki ba, lamarin da ke fusata Kyiv.

Shugaban wanda ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a watan da ya gabata a wani taro a Alaska, ya bayyana sayen man fetur na Rasha da ƙasashen NATO ke yi a matsayin abin mamaki, ya kuma ce hakan yana raunana ƙarfin gogayyar kasuwancinsu da Moscow.

Trump ya ce, muddin ƙawancen ƙasashen mai mambobi 32 suka ɗauki shawararsa, to lallai wannan yaƙi zai ƙare cikin ƙanƙanin lokaci, amma kuma idan ba haka ba, to suna ɓata lokaci ne kawai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rasha Ukraine

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka

Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.

“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.

Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.

“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.

Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.

“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazanar Sa Ga Nijeriya
  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida