Faransa : Mutane 250,000 suka shiga zangar zangar ‘’a Toshe komai’’ inji CGT
Published: 11th, September 2025 GMT
Kungiyar kwadago ta CGT a faransa ta ce mutane 250,000 ne suka shiga zanga zangar da ake wa lakabi da ‘’A toshe komai’’ a fadin kasar, ko yake hukumomin kasar sun ce mutum 175,000 ne suka halarci zanga zangar ta jiya Laraba.
Rahotannin sun ce a babban birnin kasar an yi arangama a kusa da wasu muhimman wurare.
‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar yayin da aka kona kwandon shara da dama.
Babban Daraktan Kula da Sufurin Jiragen Saman ya kuma sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tashoshin jiragen sama na Marseille, Nice, Bastia, Ajaccio, Figari da Calvi, tare da haifar da jinkiri da sokewa a ranar.
Bayanai sun ce Kimanin mutane 295 aka kama a fadin kasar a zanga-zangar.
A halin da ake ciki kuma, kungiyoyin kwadago na Faransa sun kuma yi kira da a gudanar da taron gangami a fadin kasar a ranar 18 ga watan Satumba domin nuna adawa da kudirin kasafin kudi na tsigagen firaministan kasar Francois Bayrou.
Bayrou, wanda ya bayyana tsarin kasafin kudin shekarar 2026 a watan Yuli, yana neman goyon bayan shirin ceto kusan dalar Amurka biliyan 51 a wani bangare na kokarin rage yawan basukan da kasar Faransa ke bi, wanda yanzu haka ya kai kashi 113 na GDPn kasar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya nada Ministan Sojin kasar Sebastien Lecornu a matsayin sabon Firaministan kasar a ranar Talata. An dora masa nauyin yin shawarwari da jam’iyyun siyasa kafin kafa gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD ta yi maraba da yarjejeniyar Iran da IAEA dangane da komawa bincike September 11, 2025 Sauyin Yanayi : Shugabannin Afirka sun bukaci a yi adalci September 11, 2025 Sheikh Qasim: Hare-Haren HKI Kan Qatar Sashe Ne NA Shirinta Na “Isra’ila Babba” September 10, 2025 Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar September 10, 2025 Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta September 10, 2025 Iran Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Guda kan HKI bayan Harin Qatar September 10, 2025 Sojojin HKI Sun Ragargaza Hasumiyyar Tayyib II A Kokarin Korar Falasdinawa Daga Birnin Gaza September 10, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138 September 10, 2025 Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai. September 10, 2025 Babu Gaggawa Na Fara cire Haraji Kashi 5 Na Man Fetur A Nijeriya September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA