Sarkin Zazzau ya jagoranci jama’a domin murnar Maulidin bana
Published: 5th, September 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya jagoranci jerin gwanon zuwa gidan Sarkin Ladanai na Zazzau a matsayin al’adar tarihi na bikin Mauludin na bana.
Bikin Mauludin na bana shi ne karo na 185 da aka shirya a hukumance da aka gudanar a Zariya.
An kama mace ɗauke da bindiga da N2m a otal Mauludi: ’Yan sanda sun haramta hawa babur da daddare a GombeSarkin da ya hau kan doki ya samu rakiyar ’yan uwa na masarautar domin yin mubaya’a ga fitaccen gidan malamin addinin Musulunci, wato gidan Sarkin Ladanai.
An gudanar da bukukuwan murnar ne don zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).
Manyan Malaman Addinin Musulunci sun gudanar da addu’o’i a harabar domin samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Masarautar Zazzau da ke Jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya.
Abu Ladan, Sarkin Ladanai na farko da ya koyar da ilimin addinin Musulunci a makarantar da mahaifinsa Kanuri ya kafa a lokacin da ya tafi aikin hajji da ƙafa ya dawo da wasu littattafai.
Ana karanta waɗannan littafai na Musulunci a gidan duk ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a matsayin wani ɓangare na tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
Waɗannan sun haɗa da yin salati ga annabi da addu’o’in zaman lafiya da wadata da ci gaban al’ummar Zazzau.
Tun daga wannan lokacin har zuwa yau, ana ci gaba da karatu da yin addu’o’in Maulidin Annabi a gidan Sarkin Ladanai.
Sarkin Zazzau, tun daga wancan zamani zuwa yanzu, ya ci gaba da halartar taron na shekara-shekara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mai Martaba Sarkin Zazzau Sarkin Ladanai
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.
A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.
Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.
Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.
Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.
Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”
“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”
Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.
Daniel Karlmax