Gwamnan Neja ya rushe kwamishinoninsa
Published: 1st, September 2025 GMT
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa.
Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan.
Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a jihar tare da yi musu fatan alheri.
Sai dai kuma gwamnan ya sake nada sakataren gwamnatin da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da mataimakinsa a da wasu jami’ai a kan muƙamansu
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwamishinoni majalisar kwamishinoni Sallami kwamishinoninsa
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27, wanda ya shafi kashe-kashen kudade na yau da kullum da kuma manyan ayyuka.
Ya ce, wannan ƙarin kasafin kuɗin zai inganta ayyuka da tsare-tsare da ake gudanarwa a muhimman fannoni irin su ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, noma da sauran muhimman ayyukan ci gaba.
Sagir ya ƙara da cewa, za a mika ƙarin kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar domin tattaunawa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da ka’idojin kasafi suka tanada.
Kwamishinan ya ƙara jaddada cewa, wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da adalci, da kula da kuɗaɗen jama’a yadda ya dace, da kuma tabbatar da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar baki ɗaya.
Usman Muhammad Zaria