HausaTv:
2025-11-03@02:01:50 GMT

Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD

Published: 30th, August 2025 GMT

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Juma’a cewa, sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya yanke shawarar  soke takardar izinin shiga kasar ga wasu mambobin kungiyar ‘yantar da ‘yancin Falasdinu (PLO) da hukumar Falasdinu (PA), ciki har da shugaban PA Mahmoud Abbas, gabanin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York na watan Satumba mai zuwa.

Wadannan matakai na nufin cewa da alama Abbas ba zai iya zuwa New York  don gabatar da jawabinsa na shekara kamar yadda ya saba yi ba.

Wannan mataki dai na cikin jerin takunkuman da Amurka ta kakabawa jami’an Falasdinawa a watan Yulin da ya gabata, a daidai lokacin da wasu kasashen yammacin duniya ke neman amincewa da kasar Falasdinu a hukumance.

A cewar sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, wadannan takunkumin ba su hada da aikin hukumar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya ba, kuma ma’aikatar ba ta bayar da wani karin bayan ikan hakan ba.

Sai dai fadar shugaban kasar Falasdinu ta bayyana matukar  mamakinta game da matakin na Amurka, inda ta jaddada cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar MDD, musamman ganin cewa Falasdinu mamaba ce mai sa ido a MDD.

Ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta sake nazari tare da janye shawarar da ta yanke, tare da tabbatar da kudurinta na bin dokokin kasa da kasa.

Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta bayyana hakan a matsayin yin fatali da kudurorin MDD da aka rattaba a hannu a kansu a cikin  yarjejeniyar 1947.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka August 30, 2025 Jami’in Sojin Isra’ila: Masu Tunanin Hizbullah Ta Yi Rauni Suna Mafarki Ne August 30, 2025 Mali: Kungiyar Al-Qaeda ta kwace iko da garin Farabougou da ke tsakiyar kasar August 30, 2025 Mutum Guda Ya Yi Shahada Sanadiyar Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon August 29, 2025 Malasiya Ta Bukaci A Kori Isara’ila (HKI) Daga MDD August 29, 2025 Iran: China Ta Zuba Jari A Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana A Bushar August 29, 2025 MDD Ta Yi Tir Da Dirar Mikiyan Da Jamus Takewa Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 29, 2025 Majalisar dokokin Iran ta gabatar da kudirin ficewa daga NPT August 29, 2025 Guterres: Dole ne a kawo karshen halin da ake ciki a Gaza August 29, 2025 Pezeshkian: Alakar Iran, China Na Da Amfani Mai Yawa Ga Kasashen Biyu August 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: harkokin wajen

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar.

A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne.

Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar.

Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar babbar barazana a Najeriya,”, inda ya kara da cewa ana kashe dubban Kiristoci, kuma masu tsaurin kishin Islama ne ke aikata wannan kisan gillar.

“Saboda haka ya ayyana Najeriya kasar da ake da damuwa a kanta.”

Bugu da ƙari, Trump ya ce ya bai wa ‘yan majalisar wakilai Riley Moore da Tom Cole umarnin fara bincike kan hakan kuma su kai masa rahoton sakamakonsa.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka da kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya
  • Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar
  • Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific
  • M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya