Iran: Kasar China Ta Zuba Jari A Aikin Samar Da Wutan Lantarki Daga Rana A Bushar
Published: 29th, August 2025 GMT
Shugaban kamfanin rarraba wutan lantarki na kasar Iran ya bada sanarwan cewa kasar China ta zuba jari na kimanin dalar Amurka miliyon 70 a aikin samar da wutan lantarki mai karfin MW 200 wanda kamafanin SATBA yake ginawa a lardin Bushar na kudancin kasar Iran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Gholam Reza Hashmati ya bayyana cewa wannan shi ne zuba jari mai tsoka wanda kamfanin waje yayi a shirin samar da makamashi mai tsabta na kasar Iran.
Yace MW 200 zai taimaka wajen samar da wuta mai tsabta ya kuma rage dogaro da man fetur da kuma gas wadanda suka gurbata yanayi.
Hashmati ya kammala da cewa yankin Bushar yana gaba a cikin yankunan kasar Iran wajen samar da makamashi mai tsabta wanda baya gurbata yanayi, saboda a halin yanzu yankin yana da MW 750 na iran wannan makamashin, sannan aikin da ake fatan wani kamafani kasar China zai zuba jari a cikinsa mai karfin MW 2000.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD Ta Yi Tir Da Dirar Mikiyan Da Jamus Takewa Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 29, 2025 Majalisar dokokin Iran ta gabatar da kudirin ficewa daga NPT August 29, 2025 Guterres: Dole ne a kawo karshen halin da ake ciki a Gaza August 29, 2025 Pezeshkian: Alakar Iran, China Na Da Amfani Mai Yawa Ga Kasashen Biyu August 29, 2025 Araqchi: Matakin Gungun Kasashen Turai Kan Iran Lamari Ne Da Zai Dagula Al’amura August 29, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Mayar Da Martani Kan Kudurin Tawagar Turai August 29, 2025 Yemen Da Jaddada Yiwuwar Daukan Dogon Lokaci Dakarunta Suna Arangama Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya August 29, 2025 Guterres: Shirin Gwamantin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Wani Babban Hatsari Ne August 29, 2025 Aragchi: Iran Zata Maida Martani Ga Kasashen Turai Dangane Da “SnapBack” August 28, 2025 Farashin Mai Ya Tashi Saboda Kammala Gyaran Bututun Druzhba August 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher
Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan
Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.”
Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da Qatar ke yi na tsayawa tare da ‘yan uwantaka na Sudan da kuma rage musu wahalhalun da rikicin yaki da makamai ya haifar. Haka nan ya kunshi rawar da Qatar ke takawa wajen karfafa martanin jin kai da kuma gina gadoji na hadin kai da al’ummar da abin ya shafa a fadin duniya.
Tallafin ya kunshi kimanin buhuhunan abinci 3,000, tantuna 1,650, da sauran kayayyakin bukatu, wanda Asusun Ci Gaban Qatar da kuma Hukumar Ba da Agaji ta Qatar suka bayar, don tallafawa wadanda suka rasa matsuguninsu daga El Fasher da yankunan da ke kewaye. Ana sa ran sama da mutane 50,000 za su amfana daga wannan tallafin, wanda ya haɗa da kafa sansanin agaji na musamman na Qatar mai suna Qatar Charity.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci