Yadda Kasar Sin Ta Nuna Wa Afirka Asalin Ma’Anar Hakkin Dan Adam Sabanin Irin Na Kasashen Yamma
Published: 29th, August 2025 GMT
Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, manyan tituna, tashoshin ruwa da wutar lantarki, gadojin kan hanyar ruwa da masana’antu, duk wadannan an tanade su ne don su zama hanyar rage talauci da tallafawa al’umma.
’Yancin Cin Gashin kai da Kiyaye Mutuncin Kasa
Wani muhimmin jigo na diflomasiyyar kare hakkin dan Adam ta kasar Sin, ita ce samar da ka’idar ikon mallakar kasa da rashin tsoma baki kan harkokin gudanar da mulkin kasashen abokan huldarsu. Ba kamar yadda kasashen yammacin Turai ke yi ba, kasar Sin ba ta jingina sharuddan siyasa kan lamuni ko tallafin da take bayarwa, kamar sauye-sauyen shugabanci ko tsoma baki kan harkokin siyasar kasashen. Wannan tsari na Sin ya yi matukar janyo ra’ayoyin gwamnatocin kasashen Afirka, wadanda galibi ke kallon taimakon da sai an gindaya musu sharudda a matsayin tauye musu hakkin ‘yancin cin gashin kansu. Don haka kasar Sin ta gabatar da kanta a matsayin abokiyar huldar da ke daukar kasashen Afirka a matsayin kasashe masu ‘yanci ba Bayi ba.
Kare Rayuwa da Lafiya
Kasar Sin ta tallafawa kasashen Afirka a fannin kiwon lafiya da taimakon jin kai. Tun daga shekarar 1963 kasar Sin ta fara turo tawagar likitocinta zuwa Afirka don aikin agaji. A lokacin da cutar annobar Ebola da annobar COVID-19 ta barke a kasashen Afirka, kasar Sin ta jaddada ‘yancin rayuwa da lafiya a matsayin babban hakkin dan Adam. Irin yadda ta samar da alluran rigakafi, asibitoci, da kayan aikin likitanci, hakan ya nuna yadda kasar ke kare mutuncin dan Adam ta hanyar kare bukatunsa na halittarsa na yau da kullum.
Musanyar Al’adu da Mutuncin Dan Adam
Baya ga samar da tattalin arziki da kiwon lafiya, kasar Sin na ingiza yin mu’amala tsakanin jama’arta da na Afrika don karfafa mutunci da daidaito. Ba da tallafin karatu ga daliban Afirka a jami’o’in kasar Sin, shirye-shiryen al’adu, da hadin gwiwar kafofin watsa labarai, duk hakan na nufin sauya tunanin yadda kasashen yamma suka dauki Afirka. Ta hanyar karfafa mutunta al’adu da hadin gwiwa, kasar Sin ta gabatar da kanta a matsayin mai daukaka darajar mutum da kasa baki daya.
Kalubale da Suka
Hausawa na cewa, “sara da sassaka, ba ya hana Gamji toho”, duk wanda ya kudiri aniyar tsamo wani daga cikin kangin talauci da koma baya da wani ya jefa shi, dole sai ya fuskanci “kalubale da suka” daga wannan mai zaluncin. An ce lamunin kasar Sin ga Afirka kuma babu “tsangwama”, na nufin mallake yankin ne. Wasu kuma sun ce, matsalolin muhallin Afirka na da nasaba da ayyukan da kamfanonin kasar Sin ke yi a yankin. Duk da wannan suka, shugabannin Afirka sun jaddada kuma kullum a shirye suke kan ci gaba da kare muradun Sin domin ta tsamo su daga babakeren kasashen yammacin Turai da suka mayar da su Bayi, suna masu jaddada cewa, ci gaban da kasar Sin ke samar wa yankin, shi ne asalin kare hakkin dan Adam.
Da wadannan muhimman abubuwan da kasar Sin ke yi a Afirka bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, za mu tabbatar da cewa, huldar Sin da Afirka wacce ta rataya a kan samar da ci gaba, kare ‘yancin cin gashin kai, kare mutunci, su ne hakikanin kare mutuncin dan Adam sabanin yadda kasashen yammacin Turai suka kakabawa Afirka, wai ‘yancin dan Adam, ‘yancin siyasa.
Ta hanyar ba da fifiko ga bunkasuwar tattalin arziki, da mutunta ‘yancin kai, kasar Sin ta sake fayyace ka’idojin hadin gwiwar ‘yancin dan Adam da kasashen Afirka. Ba tare da wani kalubale ba, wannan hangen nesa na kasar Sin ya yi tasiri ga yawancin ƙasashen Afirka da ke neman mutunci, daidaito, da cin gashin kai a dangantakarsu ta ƙasa da ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Sin ta
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.
Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.
Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.
NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuA kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan