Leadership News Hausa:
2025-07-26@07:47:10 GMT

Tsohon Minista Ya Fice Daga Jam’iyyar APC A Nasarawa

Published: 2nd, June 2025 GMT

Tsohon Minista Ya Fice Daga Jam’iyyar APC A Nasarawa

Tsohon Ministan Muhalli, Barrister Mohammed Hassan Abdullahi, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki a Nasarawa.

Abdullahi ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin ƙaramin Minista na Kimiyya da Fasaha, kafin daga bisani ya zama cikakken Ministan Muhalli. Haka kuma, ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Nasarawa a lokacin Gwamna Tanko Al-Makura.

Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Nassarawa Duk Da Umarnin ‘Yansanda A Kano

Ya miƙa wasiƙar ficewarsa ga shugaban jam’iyyar APC na mazaɓarsa ta Uke, a ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, a ranar Lahadi. Wasikar ta nuna dalilinsa na barin jam’iyyar a matsayin na “ƙashin kai”.

Barrister Abdullahi ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yi wa ƙasa hidima da kuma goyon bayan da ya samu a lokacin aikinsa, inda ya ce: “Ina yi wa jam’iyya da shugabanninta fatan alheri.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nassarawa jam iyyar a

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare

Sanatoci da dama sun goyi bayan wannan buƙata.

Sun bayyana cewa hakan ya shafi dukkanin yankunan ƙasar nan kuma yana daidai da yadda sauran ƙasashe ke gudanar da ci gaban tattalin arziƙi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Obi Da El-Rufai Ba Su Shiga ADC A Hukumance Ba — Kakakin Jam’iyyar 
  • Xi Jinping Ya Karbi Takardun Nadi Daga Sabbin Jakadun Kasashen Waje
  • Jihohin Da Ke Shirin Rage Kudin Wutar Lantarki Su Shirya Biyan Tallafi – Ministan Wuta
  • Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu
  • Sojoji Sun Kwato Makamai Daga Hannun Ƴan Bindiga, Sun Ceto Yaro A Filato
  • Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
  • Jami’an Shige Da Fice Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
  • Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Sake Ciyo Bashin Dala Biliyan 21 Daga Ƙetare
  • Gwamna Sule Ya Ƙara Musanta Zargin Kare Ƴan Ta’adda A Nasarawa
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya