Shettima zai tafi Gabon bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar
Published: 3rd, May 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai bar Abuja yau zuwa Libreville, babban birnin ƙasa Gabon, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Brice Clotaire Oligui Nguema.
A halin yanzu Shugaba Tinubu yana ziyara ta kwanaki biyu a Jihar Katsina.
A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa, Najeriya na goyon bayan sauyin mulki na dimokuraɗiyya cikin lumana a ƙasar Gabon kuma ta sake tabbatar da ƙudirinta na inganta dimokuraɗiyya a Afirka.
Oligui Nguema, wanda ya kasance shugaban riƙon ƙwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu, inda ya samu kashi 94.85% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Rashin tsaro: ‘Ba za mu miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba’ Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a Zamfara’Yan takara bakwai ne suka fafata, inda tsohon Firayim Minista Alain Claude Bilie-By-Nze ya zo na biyu da kashi 3%.
Ana sa ran Shettima zai dawo Najeriya bayan bikin rantsarwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a KolmaniA cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.
Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu muhimman ayyuka da yake yi.
Waɗannan ayyukan sun haɗa da gyara da inganta harkokin Kwastam, kammala wani shiri da zai sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya, da kuma taimaka wa ƙasar wajen cika alƙawuran da ta ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA).
Shugaba Tinubu, ya yaba da ƙwazon Mista Adeniyi da yadda yake gudanar da ayyukansa.
Ya ce ƙarin wannan wa’adin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga a hukumar, da kuma tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.