Aminiya:
2025-08-01@09:21:12 GMT

An kama matashi kan ‘satar’ ’yar maƙwabcinsa

Published: 2nd, May 2025 GMT

An kama wani matashi ɗan shekaru 33 bisa zargin yin garkuwa da ’yar maƙwabcinsa mai shekaru 21 a ƙauyen Paikon Bassa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji a yankin Babban Birnin Tarayya.

Wani ɗan banga a yankin, Dangana Bala, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun ƙorafi daga iyayen matashiyar da ta ɓace na wasu makonni.

Ya ce iyayenta sun yi zargin mutumin, wanda suka ce ya daɗe yana soyayya da ita a ɓoye.

Ya ƙara da cewa da samu wannan bayanin, ’yan sintirin suka sanar da abokan aikinsu a ƙauyen Dafa da ke makwabta da su, kuma an gano matashiyar a ƙauyen Tukurwa da ke Ƙaramar Hukumar Kwali a ranar Lahadin da ta gabata.

Wulaƙancin da ake mana a Kudu ya yi yawa —Hausawan Legas NAJERIYA A YAU: Yadda naira biliyan ɗaya ta salwanta a gobarar Kasuwar Jos

Ya ce ’yan sintirin sun gano cewa a ranar da ake shirye-shiryen Easter, mutumin ya fita da yarinyar a kan babur ya kai ta gidan abokinsa a ƙauyen.

“A gaskiya, iyayen yarinyar sun daɗe suna korafin cewa mutumin ya jima yana soyayya da ita a ɓoye. Har ma sun gargade ta da ta nisanci mutumin. A ranar Lahadi, ’yan sintirinmu da ke Dafa sun ga yarinyar da mutumin a kan babur, kuma nan take suka sanar da mu, muka je ƙauyen Tukurwa don kama shi a gidan abokinsa.”

Sun kuma ce tun farko mutumin ya musanta ɗauke yarinyar lokacin da iyayenta suka je wurinsa suna neman inda take.

Ya ce, “Daga baya mun samu labarin cewa ya fi shekara yana soyayya da ita da niyyar aure, amma iyayenta sun ƙi duk da cewa ya kashe kuɗi a kanta.”

Bala ya ce an miƙa mutumin da abokinsa da aka samu yarinyar a gidansa, ga jami’an tsaro a Kwali.

’Yan sanda a yankin sun tabbatar da faruwar lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Garkuwa makwabtaka soyayya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa

Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa.

Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025.

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri  Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno

An sanar da wannan naɗin ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa da Hukumar CDCFIB, ta fitar, wacce sakatarenta, Abdulmalik Jibrin, ya rattaba wa hannu.

Wannan naɗin na zuwa ne bayan da shugaban hukumar na yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, ke shirin ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60 a duniya.

Olumode Samuel Adeyemi yana da ƙwarewa da gogewa a aikin kashe gobara.

Ya fara aikinsa a Hukumar Kashe Gobara ta Abuja, kafin daga bisani ya koma Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa, inda ya bi matakai har ya kai matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar a sashen kula da ma’aikata.

A tsawon lokacin da ya shafe yana aiki, ya samu horo da ƙwarewar da ake buƙata a cikin gida da kuma waje.

Haka kuma ya riƙe muƙamai daban-daban a hukumar, kuma memba ne a ƙungiyoyi irin su ANAN, Cibiyar Gudanar da Harkokin Kamfanoni ta Ƙasa, Cibiyar Gudanar da Harkokin Jama’a ta Ƙasa, da kuma Cibiyar Kula da Kuɗaɗe ta Ƙasa.

Hukumar ta yaba wa shugaban da zai ritaya, bisa gudunmawar da ya bayar da kuma irin shirye-shiryen da ya jagoranta a lokacin da yake shugabancin hukumar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shekara 2 Ta Gwamnatin Tinubu: Gwamnonin Arewa Sun ƙaryata Zargin ACF Na Watsi ɗa Yankin
  • Dalilan Da Suka Sa Canada Ta Goyi Bayan Kafa Kasar Falasɗinu
  • Kwara Ta Kwashe Mabarata Daga Titunan Jihar Su 94
  • Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar kashe gobara ta ƙasa
  • Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Yadda ’yan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka sama da 10 a Katsina
  • Shugaban Ivory Coast Ouattara zai sake takara wa’adi na huɗu
  • Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu
  • ‘Yan Sanda A Kano Sun Kama Kasurgumin Dan Fashin Nan Barga Da Wasu Mutum 14