Ghana Ta Fada Cikin Takaddama Bayan Tisge Babbar Mai Shari’a Ta Kasar Da Shugaban Kasa Ya Yi
Published: 23rd, April 2025 GMT
Gwamnatin Shugaban kasa John Mahama ta tsige Gertrude Torkornoo daga mukaminta na babbar mai shari’ar kasar, bisa wasu zarge-zarge da ake yi mata, domin bayar da damar gudanar da bincike.
Matakin da gwamnatin ta dauka na tsige babbar mai shari’ar ya jawo cece-kuce a tsakanin mutanen kasar.
Tsohon mai shigar da kara na kasar Godfrred Yeboah Dame ya yi tir da matakin na gwamnati da ya siffata da farmaki mafi girma akan ma’aikatar shari’a a tarihin kasar.
Ita kuwa jam’iyyar hamayya ta zargi shugaban kasa da tsoma baki a harkokin shari’ar kasar, domin nada alkalan da za su zama masu biyayya ga jam’iyyar da take Mulki ta ( NDC).
Torkornoo da ta hau mukamin nata a 2023, kuma ta kasance mace ta uku da ta rike wannan mukamin a tsawon tarihin ma’aikatar shari’ar kasar. Har ya zuwa yanzu dai ba ta ce komai ba akan tuhume-tuhumen da ake yi ma ta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
Gwamnatin kasar Faransa ta yi kakkausar suka tare da tofin Allah tsine kan harin ta’addancin da aka kai birnin Zahidan na kasar Iran
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin birnin Zahidan na kasar Iran, tare da jaddada adawar kasarta kan duk wani harin ta’addanci da aka kai kan fararen hula.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da wata sanarwa inda ta ce, birnin Paris na matukar yin Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a birnin Zahidan na kasar Iran a ranar 26 ga watan Yuli, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama ciki har da uwa da kuma ‘yarta.
Sanarwar ta kara da cewa, “A yayin da take mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka mutu, suna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a wannan harin ta’addanci.”
Wani abin lura a nan shi ne cewa, a safiyar ranar Asabar 26 ga watan Yuli ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari kan ginin hukumar shari’a ta cibiyar birnin Zahidan, fadar mulkin lardin Sistan da Baluchestan a kudu maso gabashin kasar Iran, inda suka kashe da kuma jikkata wasu Iraniyawa.