Sin: Amurka Ta Buga Harajin Fito Kan Sassa Daban Daban Ba Tare Da Nuna Sanin Ya Kamata Ba
Published: 23rd, April 2025 GMT
Daga nan sai Geng Shuang ya bayyana matsayar kasar Sin don gane da hakan, yana mai cewa, kasar na matukar jajantawa al’ummun Haitian bisa halin da suka shiga. Yana mai kira ga daukacin al’ummun duniya da su ci gaba da taimakawa kasar wajen karfafa tsare-tsarenta na ikon gina kai, da rungumar tafarkin neman ‘yancin kai, da dogaro da kai, da gaggauta hawa turbar neman ci gaba na kashin kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki da ake aikatawa a Gaza.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada wajibcin tunkarar muggan manufofin yahudawan sahayoniyya na tilastawa al’ummar Gaza da yammacin kogin Jordan yin hijira daga muhallinsu, yana mai bayyana halin ko in kula da kasashen duniya suke nun awa kan wadannan laifuka a matsayin abin mamaki da damuwa.
Araghchi ya kuma yi wa takwaransa na Masar bayani kan ci gaban tattaunawar Iran da Amurka kan Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da ake takaddama a kai tsawon shekaru.